Sashe 157
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi. Uwarta kwashi salati tana taba hannayen ta wuri daya tace mjin nakine dan iska Nazifa yaushe kika zama haka wai ban sani ba . Duk tantirancina da iya shege duk kuma irin cin fuskan da Alh zaimun kin taba jin na bude baki na zage shi ? Lalai dole kijawa kanki duka ki zagi uwarshin ki zageshi har kannen shi dan banzane da bazai dukeki ba ? To wai ma fada min meye yaron nan modibbo ya rageki dashi a duniyan ko kuwa cikin yan uwan ki kaf dake aure waya kaiki samun dakin aure haka ki fada min. Mama kin sani fa uwarnan nashi ba zata taha barin mu zauna lafiya dashi ba cikin tsawa uwar tace da ita rufa min baki wace tayi gadon rashin hankali a wurin ubanta. Ke da kina da hankali hjy Addah ba kanwar uban ki bane da zaki buga mata waya nacin mutunci irin haka. Wallahi mama kar, , , rufa min baki na kira hjy Addah din ta fada min komai kuma ta rantse min bata san komai ba akan wanan zancen don baya ko zuwa gidan nasu. Ke gaki sarkin marasa hankali da wayau kin kirata kin zageta ko kin manta ita ta haifi dan kuma ta aura maki shi da yardan ta . Idan ba yana bin umurnin mahaifiyar shi ba ko kusa dashi ke nazifa kina zaton zaki iya zuwa kon nunawa duniya tayi masa zaben tumun dare ke nan a kan ki. Gobe sai ki nemi wace zata gyara tsakanin ku dashi idan kun bata son ko tayi niyar taimakon ki diyan ta ba zasu bari ba. Idan kina dauka maganata wallahi kiyi gagawan gyara tsakanin ki da mijin ki idan kuma kinki har suka gaji dake karshe ba zaki sha da dadi ba. Dolene ki sauke girman kanki da wani fadin rai in kina son ku zauna lafiya da mijin ki dolene kuma ki masa biyayayya kamar yadda Allah yace ai masu. Abincin shi shimfidan sa dama yan uwan shi su kasance kin kiyayye hakan sai ki kamo su daga kasa an fada maki haka ake kama gida a cikin karfi da yaji kome ? Duk gatan ki da wani girma da kikaga yan uwan ki na baki a yanzu yau in akace auren ki ya mutu da yaron nan angama baki shi don mahaifin ki ba zai baki abinda mijin ki ke baki ba har ya hasakaki haka a cikin yan uwa ba. Fada sosai mahaifiyar tayi mata tare da nuna damuwan ta kan kada auren yar nata ya mutu asirin su ya tono don samun da sukeyi a wurin shi. Sam bata bata daman furta komai ba a gaban ta har ta gama tayi mata sallama ta fito zuwa gida ta bar yar nata na hadiyan rai. Sai fadi take kaji mun mama da wani zance ai hakan kukayi har baba yake ganin yafi karfin ku yake maku abinda yaga dama irin nacin fuskan da yake masu. Nikan babu da namijin da zan zauna yana min haka na kyaleshi don bai isa yace ya juyani yadda yaga dama ba har yan uwan shi su samu kafan rainani ina sam hakan bazai yuyu ba. Gabantane ya fadi ras don tunawa da kalamin mahaifiyar ta na karshe me mamake nufi da hakan tana nufin saki ke nan ko me ? Komawa tayi ta lankwashe a cikin kujeran da take zaune tana maida numfashinta a hankali tare da lumshe idanun ta. Ba komai take tunane ba sai tunanen rabuwan ta dashi don tasan idan fitinan su yakai fitina mahaifinta kai tsaye zai bashi rashin gaskiya shi kuma din ya saketa. Ta dade zaune ta nemawa kanta mafita saidai mafitan ne da kamar wuya a wurin ta don haka na nufin sai ta kwanta an hauta za a zauna daidai ke nan haka ke nufi. Tun bayan sallah asuba dana iya tashi nayi na koma na kwanta wani irin zazzabi da ciwon kai suka rufeni lokaci guda maganin dana sha na shaka yasa har barci ya dan daukeni lokacin. Yar uwa idan nace maki wanan abin baya damuna bata lokacine son in akwai abinda ke damuna a rayuwana lokacin danayi wayau din nan nasan duniya shine wanan laluran fadi ba a tambayeka ba din da yanzu yake son zama min babban lalura don har wasau nason amfani dani wurin cin ma bukatan su wanda hakan ya dan so kawo min matsala a rayuwana daga baya. Don ba kowa zai yarda da hakan lalura bace da akan jarabi bawa dashi kai tsaye musaman nida nayi zama a cikin kabilu da za a iya ganin kamar harkan wani cultisim na shiga acan nake haka. Shine dalilin daya sa na bakishi a cikin labarina don ki fahinci kan labarin cewa ina da wani lalura ko baiwa zan kirashi yadda bature ke kiran shi a turance da talents yan baiwa ke nan. Gani ba kawa ta kut da kut ummace dai komai nawa don da ita na bude ido da ita na tashi kuma nake rayuwa da ita sai dan kanina Amar dake tare damu shi din namijine kuma tunda ya kai secondry ya fara barin mu gida haka kuma ya samo asaline don yaran Abdulhamid da suke fita tare wurin buga ball. Ban san dadin kawa ko aminiya ba sai zuwan mu kaduna shakuwa na da Faizan daddy yasa nasan muhimancin mu,amula da sa,an ka. Abubuwa da dama nakan so in damu wata muyi shawara saidai wacece zan sama tunda ban shaku da kowa ba a rayuwana dan dama wani lokaci mukan zauna idan weekend ne ban fita ba tare da muniya matar Abdulhamid muyi hira . Saidai tsiyan abin ban yarda hiran yai tsawo don rashin sabo da mutane da bamuyi ba sai tsakanin mu kawai muke mu,amula mu kadai duk wanan kuma yana cikin tarbiyan da muka samune a wurin umman mu don kokarin nisanta mu da mutane da tayi. Ranan da ya Abubakar yazo umma ta sheda mashi na tafi wurin aiki yake tambayan aikin me nakeyine ta fada mai a wani company nake aiki kuma a na samu sosai ga aikin . Don yanzu dana kare karatuna akwai samu sosai a wurin Alhamdullahi gaskiya mama dama Sahiba tayi karatune ya tambaya a cikin mamaki. Ikon Allah umma ta fada ta mike ta shiga daki ta dauko mashi takardun karatuna ta bashi ya duba ya dade yana nanata karantasu. Ya dago kai yana fadin ikon Allah dama ashe ta tsaya har tayi karatu haka toshi yana ina har haka ya faru wai ? Gaskiya dolene yaran nan su ja baya da kowa a yanzu duba ga yadda aka watsar dasu haka a cikin duniya bayan kuma asan suna raye a doron duniyan kowa ya fita batun su har daddy din. Wai dai zancen Nazira ko yana da kamshin gaskiyane daddy na da hannu cikin wanan kisan da akayi yasa baya son a tayar da zancen yake ta fadin lokacin tayar da zance baiyi ba. Wani lokaci yake jira ayi wanan case din sai lokacin da wani daga ciki ya mutu ko sai lokacin da ba musu case din za ayishi. Ya gama tunanen shi ya dago kai yana cewa umma kai gaskiya mama wanan abin alfaharine ga kowan mu wallahi saidai bai kamata ace ta tsaya aiki a company ba don basu da tabbas ga hakan. A, a a kada kace hakan don wanan aikin mu mun samu rufin asiri sosai a cikin sa ta yadda ba zamu raina hakan ba a garemu. Na sani mama amma ina nufin tunda tana da takardu haka masu kyau me zai hana a sama mata aiki a karkashin gwaunati tayi zai fi wanan din da takeyi yanzu idan an samu. Koda kuma za,a samu din ya kasance dai a arewa za a samo mata don yanzu in son samune nafi son ku koma gida kusa da yan uwa ku zauna. Take annurin fuskan umma ya canza lokaci guda take fadin a, a ka barmu nan inda muke don zaman mu nan yafi min kwanciyar hankali da komawa can inda fitina da tsegumi zai hanamu zaman lafiya. Sai dai idan har kun yarda mu dinga kai ziyara muna ganin wanan baida matsala amma a yanzu hankalin mu ya fi kwanci da zaman mu a nan. Shiru yayi yana dan tunane kafin yace mama masan abinda kike tunane don matsalan ku dasu uncle nuhu ne hakan kuma a sannu an kusa kaiwa karshen zancen insha Allahu. Don ina bincike yanzu sosai akan matsalan ba tare da sanin kowa ba don bana son kowa yasan da ina wanan binciken gaba daya har daddy ban yarda da su san da zancen ba don na kula indan na yunkura kamar ana tosheni ga hakan. Idan har haka zai ja matsala a rayuwan ka modibbo gara a rufe wanan zancen mu hadu a lahira dasu Allah yai muna hissabi a gaban shi umma ta fada da sauri ta kara da fadin. A yanzu bamu da abinda zamuce sai godiya ga Allah da kuma gareku kai da dan wurin hjy harin nan dake zuwa wani lokaci haka kuma inda sahiba ke aiki a yanzu gaskiya banda abinda zan fada sai hamdallah. Jin an ambaci sunan mustapha ya bata fuska don baison jin hakan ba sam bai dau son mu,amulan mu da wanan guy din yasa yace na dai fada maku kuyi hankali dashi mustapha din. Ya kwana biyu ma baizo nan ba ai tun lokacin da yazo kan matsalan maganan da kai masa mutanen kan Sahiba suka taka tafada mai abubuwa da dama a game dashi tun ranan ban sake ganin shiba gidan nan. How comes mama har kuka yarda yasan da wanan matsalan nata har yaji komai a bakin ta ya fada a dan tsorace cikin mamaki yana buga hannun kujeran da yake zaune a kai.