← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 337

Sashe 172

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

gargadi kada ya fadawa kowa ga inda muka tafi. Shiru nayi ina tunane a raina yadda abubuwa ke son tikice muna kuma gana aikin da mukazo yi na gane zamu kwasa dasu sosai inba gyaran Allah ba. Shi kuma yanzu yaya ya fito da wani zance wai akan matsalan mahaifin da kawai ya share zancem kamar yadda kowa ma ya share har sai an je gaban ubangiji. Olawede ya kira waya yana min bayani kan sai an buga waya a kawo mai kaya nace ya bari idan kin dawo zan fada maki. Sai lokacin na nisa ina fadin yaushe ya kira umma wallahi banso ya kai ga kira ba naso na tura kudine a tura masa kaya tun bai nema ba. Sai kuma zancen aikin nan ya dauke min hankali umma kinga mutanen nan basu tsoron Allah sam wallahi wai yanzu kokari sukeyi su koremu da asiri ko su shafa muna mantuwa mu bar garin nan a rikice. Yaushe tsoron Allah zai shiga zuciyar mutanene sun Allah ba karya bane wai mutuwan nan fa kullun yita akeyi ana nunawa mutane ishara akan shagala da duniya. Amma maimakon tsoron Allah ya shiga zuciyoyin yan Adam sai kuma kara dulmiya da son duniya akeyi musanman musulman mu na wanan nahiyar na yanzu. Waya na dauka na turawa wa kamfani kudi tare da kiran su nayi masu bayanin abubuwan da zasu kawo muna. Mikewa nayi na kwaso takarduna ina dubawa kafin nayi wani zabura da sauri don ganin sunan wanda ban zata ba a cikin jerin sunan da nike lissafowa a lokaci. Kafa ma sunan ido nayi na dan lokaci kafin na saci kallon umma inda take zaune na kara mayar da kallona kan sunan ina kallo. Jikina ne yayi sanyi sosai na kasa aikin da nakeyi din na zurfafa a cikin tunane mai nisa lokaci guda. Barci na shige da wuri ranan umma tana daukan duk hakan gajiyane a nasu fahintar basu san abinda na gani bane a takardan yasani a cikin damuwa don sunan wanda ban taba zato ko tsamani ba da nagani a cikin wanan jerin sunayen. Saidai kuma zuciya na taki yarda da hakan cewa shi din ne saidai idan mai kama da sunan shi ne na gani din acikin masu ruwa da tsakin maida kamfanin baya a yanzu. Sam zuciyar shi bai yarda da abinda yake gani a wayan shi ba don haka washe gari ya dauki wayan ya saita shi ta yadda zai kaishi har inda yake bashi location din wayan umma din. Ganin inda ya kaishi a GRA din na kaduna ya tsaya yana mamaki hakan kuma signal din yaci gaba da nuna mai green kundunbala yayi ya shiga compound din wurin yana bin ko ina da kallo. Har inda computer din nasa ya tsaya wuri daya yana dan halbawa ya dago kai ya kalli kofan gidan da kyau mamakine ya kamashi lokaci daya amma cikin karfin hali irin nasa yasa ya fito don tabbatarwa kanshi ganin dalilin kasancewar hakan. Gyara tsayi yayi tare da dan gyaran kwalan rigan shi nocking din kofan gidan yayi tayi lokaci guda kusan sau uku ba wanda ya bude gidan. Kallin gidan ya kara yi na dan wani lokaci kafin ya juya ya na kokarin shiga motan shi jin an bude kofon yasashi juyowa ya dan waigo don ganin ko waye ya fito. Nice tsaye dagani sai dan rigan barci mara hannu har kasa duk dantsen hannuna sun bai yano a waje. Sai gashin kaina dana daure daga baya yay dan tuntu babu hula a saman kan nawa din. Sunan shi na dan kira ina fadun sannu da zuwa kayi hakkuri barci mukeyi bamuji nocking din kofan naka ba tun dazun. Tsaye yayi ya dan kuramin ido na dan lokaci kafin yace wai Sahiba kece din dama kina garin nan bamu da labarin hakan ? Ehto tafiyan ne dai yazo muna a hakan bawai munzo nan din bane da shiri bare mu fadawa wani zamu zo din . Bissimillah mana shigo umma na ciki barin tayar maka da ita na fads ina shigewa ciki shikan imanine ya kasheshi a wurin lokaci guda. Umma na sama a daki na fada mata zuwan shi mamakine kwarai ya kama umma ban tsaya mata wani bayani ba don sallaman shi da mukaji ya shigo falon lokacin . Haka yasa ta fito daga dakin a cikin hijab din ta mai ruwan siminti har kasa tana mashi sannu da zuwa ya amsa ta nuna mai kujera ya zauna. Sun gaisa duk umma tana a kunya da ganin shi tunda bata samu fada mai cewa muna kaduna ba ita da bakin ta saida ya gano hakan da kanshi. Dan shirune ya biyo bayan gaisuwa kafin can ya kawar da shirun da fadin gaskiya mama banji dadin hakan ba ace kuna cikin garin nan banda masaniya saida na,urana ya nuna min hakan ta hanyarshi har nazo nan inda kuke yanzu ? Bayan munyi waya dake mama koda ka sani ai sanin baida amfani yaya don ba lalai bane bayan kai wani dan uwa ya neme mu a garin nan tunda ba ruwan kowa damu . Juyowa yayi ya kallo inda nake fitowa ina maganan wanan karon na dora jacket din rigan a sama na daure a tsakiyan kwakwasona . Ba tsoro ko wani darr dinshi a fuskana lokacin ga wani gogewa da wayewa irin na matan goggagu da ya baiyana a fuskana alaman dai jiya ba yau bane a wurina. Amma ta yaya yarinyar nan idon ta yai sauri budewa hakane ya tambayi kanshi lokaci daya kuma ya ba kanshi amsa da fadi ba abin mamaki bane kuma ga yarinyar data tashi lagos kuma tayi karatu a cikkn sa ga aiki kuma duk a lokaci daya haka. Sahiba ni kike fadawa wanan maganan haka na dan kai zaune ina murmushi na kara fadin sorry to say tun jiyan da kuke waya na hana umma ta fada ma hakan. Don aikin daya kawomune kawai zamuyi mu koma inda mukafi karfi da wayau don haka ba lalai bane sai ka sani. Dan murmushi bakin ciki ya sake kafin ya dago kai ya dan kalleni yana fadin, , , , , ,
Chapter 172 · 0% Book details