Sashe 81
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abinda ya faru tana fadin ikon Allah yanzun me ya kawo hakan kuma tunda kunce Sahiban batayi mata komai ba. Kafin wani ya bada amsa kira ya shigo a wayan mommy din ta duba take fadin ga yaya Nuhu ya kirani jin sunan data ambata yasa na dago kai ina kallon mommy din da sauri. Naga yadda take girmama wanda ya kira din suna waya tana bashi girma kamar yana a gabanta lokacin. Suma sauran duk shiru sukayi suna sauraron mahaifiyar nasu dake fadin wallahi wallahi yaya ban tura su don wani abu ba son kawai kwana biyun na bata jin dadi shi kuma baya garin yasa nace suje su duba min lafiyan ta. Shiru tayi tana saurare kafin tace ai bai isa yayi hakan ba yaya tunda bashi ya haifi kanshi don me zaice ta kwashe kayan ta a nan zai saka nasa a falon. Wasa wasa dai sai ga kira kala kala na shigowa wayan mommy din kowa da abinda yake fadi idan ya kirata din duk hankalin mommy yabi ya tashi sosai a lokacin. Zamana yayi min amfani don na fahinci wasu abubuwa a lokacin saidai abinda na kasa fahinta shine yadda mommy din ta ke fadin zance na kasa raba daya biyun inda mommy din ta dosa a yanzu. Shin mommy tana bayana ne ko kuma tana bayan yan uwanta ne don ga bayanin ta sam bata yarda sun zageni ba haka kuma bata yaba ni ba don na fahincin hausan da sukeyi sosai a lokacin duk da hankalina na nuna bani tare dasu waya nake kallo kuma ban san me suke fada ba na nuna hakan. Karshe dai yakai har mommy din ta shirya ta fita zuwa gidan tun abin safe har sai dare don ko daddy dake wani kasan saida takai ya saka nakin shi a zancen a yadda naji bakin Fa,iza. Don ance yaya wai yayi odan wasu kaya masu kyau yakai gidan dole saida ta kwashe kayan ta a falon ya saka sabbi nasa bai saurari zancen kowa a cikin su ba a lokacin. Nan fa aka sakashi a bakin dangi wasu na fasin yayi daidai wasu kuma suna fadin bai kyauta ba don ance har Alh Nuhu yace Nazifa ta bar gidan ga baki daya sai da akai ta bashi hakkurine ya barta ta zauna. Waishi ba wani daga cikin dangi da zai fada ya musa mai bai dauki mataki a kanshi ba, da wanan na fahinci ya saka masu tsoron shi a zuciya yana ganin cewa zai iya taka kowa a cikin su yadda yaga dama. Abu dai har yakai daddy dawowa gida lokacin don yadda mommy hankalin su ya tashi kada ya halaka mata da a banza kan abinda bai kai ya kawo ba a lokacin. Dole daddy ya taso yazo har ya kaisu ga sa,insa kowa na fadi a gaban dan uwa sai yaga bayan dan uwan shi. Shi Alh Nuhu ya fara furta cewa Alh Aliyu dcp kasan nafika nafi karfin ka kada kaga don mun kulla wani zumuncin dakai kamar ban iya maka komai a yanzu. Daddy yayi murmushi yana fadin kafin ka iya min komai ni zan ma idan kace hakane zaka bullo min don komai naka a tafin hannu na yake kasani kasanni na san ka don ni komai nawa ga Allah na dogara dashi baga na wani ko abin wani. Aure daine ruwan mu muka saka ga gareshi Allah yayi cewa tun farko yar ka matar modibbo ce don haka kai koni bamu isa mu hana wanan auren ba a yanzu. Daya daga cikin wa yanda suke iyayye a garesu ne yayi magana tare da fadin kaicon ku kuma ji kunya ace iyayyen mu zariyan su guda kan auren yayan ku da girman ku ku zauna kuna wanan abin. Ina kai dake da diya mace aure kakaita tayi biyayya ta zauna lafiya da mijin yau maizai sa ka koya mata cewa itace ta auro shi bashi ke auren ta ba anya Nuhu idan mun kawu wanan hali naka ba raba kan zuri,an nan zakayi ba nan gaba. Kai kuma Aliyu kabawa yayan hakkuri ku yafewa juna wanan ai sai yaran su ji dadin yin fitinan dayafi wanan din gaba. Duk da kowa na kulle da dan uwan shi hakan bai hana a gaban iyayyen nasu suba juna hakkuri ba kafin a watse sai dai na ciki na ciki a lokacin ga kowan su. Don shi Alh Nuhu yana ganin Alh Ali dcp yana kokarin nuna shi din wani a gaban shi alhalin banza yake kallon duk da yasan yana da nasa rufin asirin don bai nema ga wani duk da yayi ritaya baisa ya koma baya ba. Daddy bai tsaya ba ya shigo motar shi ya bar gidan kanin mahaifin su din yana cike da bakin ciki tare da tunanen yadda Nuhu ya dauki kanshi da girma har yana ganun yana iya taka kowa a yanzu. Dan guntun murmushi ya sake a fuskan shi don yin wani tunanen da yayi a zuciyar shi tare da dan dukan sitiyarin motan da yake tuki. Tun jiya muke da labarin dawowan daddy din a bakin fa,iza saida bamu samun ganin shi ba sai da yamma suna zaune tare da ya Abubakar mun dawo daga islamiya muka ganshi. Wurun su na nufa nakai har kasa ina gaida shi kafin na juya ina gaida ya Abubakar din dake zaune a cikin bacin rai yayi dukun dukun da ranshi. Daddy ne yake tambaya muna karatu sosai ko nace muna dai tabawa don na kusa fita harufa zan iya hada kalma yanzu yace yayi kyau mu mayar da hankali nagode nace na mike zuwa cikin gidan. Yabini da kallin tausayi kafin ya juya yana cewa dan nasa komai ya kusa zuwa karshe don ba zan bar yaran nan haka ba ana kokarin aibantasu a cikin yan uwa. Gashima a cikin gida har karima tana zargina a kansu da uwarsu akwai abinda yakai wanan muni a rayuwan bawa a sheganta ka don wani dalili can na daban. Yaba zaune yadda yake ya kurawa mahaifin nasa ido don baison tuna wanan zancen ko kadan kafin yace . Daddy tun farko ban so ka boyewa kowa wanan zance ba tunda ba tsoron su akeji ba don baka san ko waye wanan yarinyar ba kake dauka ba zata iya kwato wa kansu yanci akan komai ba . Tayi kankanta ga yadda kake nufi amma yanzu ai dole in fasa kowa ya sani don nasan ko waye Nuhu idan ya fadi magana da wasa kada ka dauka wasan ne yake maka kaima don zai iya aikata abinda ya fada. Saidai kaima modibbo ya zama dole ka kara jajircewa a ko wani lokaci ka zamo kuma mai hankuri da matar ka don kasan irin da uwarka ta zaba ma. Kamar yadda muka saba dakin mommy mukan fara shiga mu gaida ita kafin na hjy karima karshe wanda yaga dama a cikin su yakan leka umman mu a part din mu ya gaida ita. Muna shiga a yadda muka samu mommy din yasa ban tsaya ba na fito zuwa dakin hjy karima na tsaya daga kofa ina gadai ita ta amsa min ba yabo ba fallasa lokaci daya muka shigo da diyanta. Don har babban tana gida an samu hutun makaranta a lokacin bayan fitanane suke fada mata ai nice na goya Amira da zamu tafi kuma na dawo da ita a goye don ta taka wani abu da zamu fita tana kuka. Da sauri take fadin taga kafan yarinyar sai babban take fadin wanan sahiba din cire mata shi kuma tayi mata addu,a a wurin. Mai karatu idan baku manta ba nayi tallan magani a lagos kuma matar da mijinta sun yarda danu sun ban nasha sin kuma fada min wasu ina kuma gwadawa yana amfani sosai a tare dani a yanzu. Bayan na shiga ban tsaya ba don na samu umma har part din ta gyara ko ina tayi abincin da zamuci. Wanka na shuga na fito na saka wani dongon rigan silk a jikina sallah nayi don magariba ya gabato sai bayan mun idar din muna zaune a falo ne da littafi a hannu don haka kawai naji bana son cin abunci a ranan. Sallaman hjy karima ne a kofan mu take shigowa dakin muka karba kallo daya nayi mata nikan na dukar da kaina naci gaba da karatun da nakeyi. Sai bayan sun gaisa da umma ne naji ta abanci sunana tana fadin sahiba yau meya samu kafan kanwaki ne haka. Na dago da sauri na dan kalli gurin da take tsaye din ina fadin ina ganin dutse ta taka ko wani abu kafan ya dan mata ciwo. Amma na lalasheta tayi shiru mantawa nayi i fada a gasa mata da ruwan zafi da muka dawo kada wurin yayi mata ciwo da dare. Amma ai da takalma a kafanta na gani ta sake fada nace kaddara idan zai sameka sai ya samu sanadi don ban san yadda akayi ba ta cire takalman ta tako da kafa shine har hakan ya sameta. Shiru tayi ta juya ta fita bayan tace dani ta gode ta barni zaune ina binta da kallo ta fita umma ta juyo tana fadin. Bana fada maki ki rabu da yaran matar nan ba son bata da mutunci a dan maraice nace umma suke biyoni ni kuma ban iya daina kulasu don daddy. Sallaman da akayine yasa umma fasa fadin abinda zata fada a lokacin tabi kofan da kallo kaina na kasa ban dago naga mai shigowa part din ba a lokacin.