Sashe 105
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Watan mu daya yanzu a logos ke nan ba wanda ya kara waiwayan mu daga fanin yan uwan mu don haka bamu san halin da suke ciki ba damu. Muma bamu san halin da suke ciki ba a can ga karatun mu ya tsaya a lokacin shine babban abinda yafi damuna a lokacin . Kudin hannun umma na karba naje company nayi odar drinks din dai danayi niyar mu sayar da nake ganin shine zai kawo muna samu a yanzu. Zuwa yamma ko sun iso muna dashi an loda a cikin shagon dake kallon wajen gidan nike zama a shagon ina sayar da kayan don mun samu har fridge mun saya mun saka a ciki. Haka kuma na budewa Amar dan qures karami na saida katin waya shima a nan yake zama a shagon shi din don yau da gobe bai bar komai ba tunda yaron ya fara girma a lokacin. Haka nake wahalace wurin ganin rayuwa ta inganta muna ni da kaina na sama muna addimition muka koma makaranta. Idan mun tafi umma muke bari a gida da yanzu mun saba da makwabta duk da ba ruwan wani da wani a can lagos din kowa tashi ta fidda shine a garin kowa ka gani yawanci kazo nazo ne ake zaune. Nasha wuya wurin samun nawa addimition din don har saida na danganta da sarkin hausawan agege ya kama min na samu gurbin karatun a inda nake so. Kamar yadda suma basu waiwaye mu ba hakane muma din muka gaji muka fitar dasu a cikin ran mu a yanzu. Lokaci baida wuya ga Allah , har karatun mu yayi nisa a yanzu ga Allah ya tarfawa garin mu nono sana,an mu tana ja sosai. Don haka bamu cikin damuwa ko fargaban abinda zamuci dama shine damuwa na a lokacin. Sahiba kan ta canza a yanzu natsuwa da wayewa yazo min don girma ya fara kamawa nakai sha tara ga shekaru a yanzu. Weekend ne don haka yau nake da burin shiga kasuwa in sayo abinci don bana wasa har in bar abinci ya fada a gidan. Na shirya tsab dani na fito a shago na samu su umma nake fadin umma na fito zan shiga kasuwa zan duba abinda bamu dashi a gidan. Umma tace dani kada in dade akwai alaman hadari yau nayi masu sallama na fita ba mota don haka na fara takawa zuwa inda nake tsamanin samun mota da sauki. Lagos market nacewa dan Nape din yance inter nashiga muka dauki hanya akwai mutum daya dana samu a cikin motar dana shiga din ban damu da maishi ba nima na shiga motan na zauna a ciki. Muyin nisa ga tafiya ina dan kallin gefen dama naji maishi yana kokarin yaba min wani bakin kyale a kaina. Iya abinda na tuna ke nan a lokacin sai bude ido nayi na gan ni a tsakiyan mutane a kaina sun rike ni wurin kamar a gefen titi muke dasu. A hankali nake dan tsuntar abinda mutanen wajan ke fadi suna cewa A, weee see d people when try to kill d girl with d ritular . Ita kuma ashe akwai tsari a jikinta ta mayar dasu haka suna zaune tufafun jikin su duk ya yage fuskan su da gani sun sha duka na fitan arziki sosai. Abin ne ya daure min kai bayan na daga kai na kalli gefen da mutanen suke zaune sai ga wani a cikin yarbanci ya miko min ruwa a gora yana fadin. Karbi ruwa kisha Allah ya kareki yau da sun halakaki sai Allah ya baki sa,a sune suka halaka daga mai Nape din har shi wanda kuke baya zaune kunzo nan kun tsaya dasu kuna ta dabe duk kin yaga masu riguna kince sai sun rufa da wanan bakin kyalen da suke son yafa maki a jikin ki suka ki yarda su yafa shine aka samesu wurin nan akai masu dukan tsiya. Hannu nakai saman dan kwagirin dana daura daga ciki na naji yana jikina na karbi ruwan na dauraye fuskana kawai dashi na mike tsaye. Kasuwan da ban yarda na karasa ba ke nan koda suka tambayeni unguwar mu nace a agege nake suka kwashe zuwa can . Naki yarda in fada masu inda nake don nasan lagos nasan mutanen cikin ta sosai da sherin su don haka nayi masu karyan unguwa suka kaini wani waje kusa da gidan sarkin zabarmawa nace nan ne unguwan mu din. Wani lungu na samu na labe a ciki saida suka wuce na fito na bulla wani titi na samu mai adaidaita ya kaini gida. Ban fadawa umma komai ba saidai a yanayin data ganni kawai tasan babu lafiya lokacin don haka ta biyo ni zuwa ciki tana tambayana ko lafiya ? Lafiya kawai nace na shige na samu gadon dakinta na kwanta naja bargo na rufe jikina daku sai lokacin tsoro ya kamani kuma. Ga lissafin ya Abubakar yau shekaran daya da watan shi shidda rabon shi damu gashi hankalin shi yana wurin mu amma kuma ya kasa yarda ya turo wani inda muke yana ganin yin hakan zaisa wani yaji a unguwar da muke zaune. Ashe tun bayan sati biyu da kawo mu wanan gidan da yayi tafiya ya kamashi zuwa can ma,aikatan su don haka baya kasan ga baki daya shi . Lokacin kan mu gaba dayan su muna dauka sun fita zancen mune yasa bamuji duriyan ko mutum dayan su ba kuma. Gashi yasan a wanan lokacin abincin daya aje muna ya kare ga karatu yasan mun bar zancen shi ke nan yake tunane. Yayi mamakin da mahaifin shi tun bayan tafiyan mu bai sake jin ya tuntubeshi da wani zancen mu ba kuma idan sunyi waya dashi. Hakama mommy mahaifiyar su ba wanda ke tambayan shi ko yana da labarin mu tun da muka tafi sai hakan yake bashi mamaki sosai. Allah ya gani yana jin tausayin wanan a halin sosai a zuciyan shi don yana ganin an danne muna hakkin mu sosai saboda son zuciya da tsoron wani yasa an kasa aiwatar da komai a kan hakan. Ciwo nayi sosai da faruwan hakan sai daga baya nake fadawa umma abinda ya faru dani hankalin umma din ya tashi sosai don haka ta kwashe sai wurin wani malamin yarbawa da ta dade da sani a tsohon uguwar mu din . Saidai mun samu tsohon yanzu ya dan tsufa sosai don haka ba lalai bane ya iya sheda ta sosai amma duk da hakan mun samu ya taimaka. A cikin bayanin shi naji yana kiran mamiwota wai ni din aljannun ruwa nake tare dasu don haka yana da wuya aci galaba a kaina ai. Sai gashi yana fadawa umma cewa mutanen da dukiyan mu yake wajen su har sukai sanadiyan zuwan mu nan yanzu wasun su susan muna raye hankalin su ya dan daga da hakan. Jin ya fara irin wanan zancen na tashi na fice daga wurin zuwa dan waje kadan na zauna nan na dinga ganin irin manyan motocin da ake parkerwa a wajen masu kudi suna zuwa neman isimi na kuma gane ba shi kadai ke aiki a wajen ba. Duk na gaji da zama ina jiran umma can kamar ance in dago idona wurin wata mota dake tsaye a wajen tun zuwan mu sai idona ya hango min wanda ban zata ba a lokacin. Yana waya ya bada baya bai kallon gefen da nake zaune din haka yasa na mike da sauri a daidai lokacin da umma da Amir suka fito daga dan wurin da nake zaton mutumin babalawo ne shi ba Alfa bane kamar yadda umma tace dashi da zamu zo. Dan karamin hijjab din dake kaina naja na gyara rufe fuskana da kyau dashi ta yadda ba za a gane ko wacece ba a lokacin gashi dole sai munbi inda yake zamu wuce. Allah Allah nakeyi inga mun bar wajen don yanzu gaba daya ban son in kara ganin wani wanda na sani a wanan bangaren na mahaifan mu ga baki daya naji kawai na tsanesu ma a lokacin. Bin mu yayi da kallon mamaki har wanda suke tare ya fito suka shiga mota hanyar da mukabi suka biyo ya hangomu mun tare mota zamu shiga. Cema driver yayi ya bi bayan mu a hankali yaga inda zamu har suka biyo mu har gidan sai da sukaga umma tasa ke ta bude kofan ta kuma rike min hannu mun shiga suka bar unguwan namu. Amma abinda mamaki yace a fili ga wanda suke tare din a kaduna ya barmu yanzun kuma ya ganmu a nan lagos har da gida me hakan ke nufi ke nan. Zancen su da mahaifiyar shine ya dawo mashi a rai da tace mudin yayan abokin kawun shi ne dake lagos yayi tafiya mai dadewa yasa ya kwaso mu zuwa gidan daddy din kamar yadda daddy ya fada mata a lokacin. Ke nan mahaifin namu ya dawo ne a yanzu ko kuwa kodai wani plan ne hakan dama aka shirya ne sai yaji hankalin shi sam bai kwanta ba ga zancen mu din haka kawai yaji yana son yasan wani abu game damu lokacin. Bayan kwana biyu shi kadai yazo ya hango umma zaune a shagon ta tana sayar da kayan sanyi da rechage card ya dan dade tsaye kafin yaja motar shi ya tafi. A wata yamma kuma weekend ne haka kawai yaji ai ya biyo titin namu ni ya fara hangowa tsaye da yaro a hannu na na fito daga shagon mu din yaji gaban shi ya fadi. Yaron wata nerboug din muce na dauka don ina da son yara zata fita zuwa kasuwa ta bar yaron a wurin mu shine yake kuka na daukeshi a lokacin ya ganmu tare da yaron. Tambayan kanshi yayi akan me ya damu da mutanen nan ne hakane kamar wasu yan uwan shi na jini ko yan uwan nasa ma yaushe rabon shi dasu yanzu. Nikan zaman gida yayi yawa jiki bai saba hakan ba don dole kuma in dinga fita mu samu abinda zai kara tallafa muna ga karatun da mukeyi mai tsada don su can ba free education sai ka biya kudin komai. Haka yasa na samu aikin dare yamma in taso goma na dare a wani babban shago dake unguwar mu din