Sashe 329
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk yadda yaso na sake jiki dashi da safe naji kunyar hakan kwana shi biyu ya juya ya koma daga sunan zuwa ghana aiki ya kwasheshi kuma zuwa Australia daga can sai a waya mukai magana dashi. Haka naci gaba da rayuwa ni da fatima sai yan abokan arzikin da a yanzu muka samu a garin dake dan zagayo ana mu,amula arziki dasu. Ba fita mukeyi ba don haka bamu da labarin komai dake faruwa sai wani shigowa da sister tayi a wurinta muke jin labarin ashe hjy falmata bata da lafiya kusa wata biyu ke nan duk labari har ya baza gari muna cikin gida bamu sani ba. Ba tare da jin komai ba nayi mata faran samun lafiya na canza topic din hiran mu saboda ban dauki zancen a komai ba har a zuciyana. Mun wayi gari da mumunan labarin da anty Amarya ta bugo muna tunda safe cewa an kama ya mustapha a kasan waje tare da wasu abokan harkallahshi su shiddah. Wanan labarin sai baimun dadi ba sam danaji amma sai naga ita Anty kamar ma murna rakeyi da hakan don tana fadi tana kwasan dariya a lokacin. Haka na wuni ranan a cikin damuwa don wanan labarin daya riskemu maradadi ga ya mustapha din a ranan ina jin yadda Fatima take waya da aibanta shi . Nakira umma munyi maganan amma nace ta kyale idan ba gwagwo hari ta kirata da kanta ta fada mata ba don kada su dauka muna bibiyan bayan sune saboda mutum wuyan sha,ani gareshi. Dole muka daiyi Dan zance kan abinda ya shafi zancen kafin my kashe wayan cikin tausayawa a halin da abin ya shafa ballema da take dan son ga iyayyen shi kasancewanshi shi kadai a garesu. Ba anty ba kawai had Faiza data kirani iron abinda take fada min me nan cewa wai asirin shi ya tuno dama yana wandaka da kudi son ranshi, ashe kallar sana,an da yakeyi ke nan. Gashi yanzu asiri ya tonu gwaggo hari tana cikin tashin hankali tana bin manyan kasan su taimaka afito mata dashi suna fama kashin kudi. Don babu Wanda zai iya fito dashi akace son laifin nasa babbane sosai na katseta da fadin har in baida laifi ba zasu sakeshi ba ? Yana da laifi kan don ashe dama sana,arshi kenan sayar da kwaya ga anty Nabila dake faman jiranshi taki kula kowa akanshi yanzu. Kuma shi yace baya sonta dan dama dama Fatima gwaggo hari kuma ta hana halakan shi da Fatima din wai bata hada zuri,a da anty Amarya don ba mutanen kirki bane. Tay tayin maganganu da dama nidai said umm nake amsa mata had zuwa lokacin da muka gama wayan da ita hankalina ya tafi ga zancen ta sosai. Yanzu na yarda da cewa kowa kanshi yasani a fannin ubanne na don na fahince su tsab kowa basu bari ba me nan don' ai ba anty amarya kawai ta haifi Fatima a gaskiya camfinsu yayi yawa sosai wallahi. Wasa wasa wanan maganan har ya kai gwaggo hari ta kirani da kanta kan case din tana kuka take fada min na taimaka mata nayiwa uncle magana ya tsoma baki ko Allah zaisa a sako ya mustapha din don shi yana hurda da manya sosai. Nayi mata alkawarin zan mass magana na kuma jajanta mata kan matsalan tana godiya muka gama wayan na kashe ina fadin olesi, olopopo. Yanzunne tasan ina da rana run ranan da suka tafi bata kirani taji lafiyata garama in na kirata a lokacin ina masu yaya hanya har sau biyu. Na kira umma na sheda mata yadda mukayi da gwaggo hari din tace idan ba matsala nayiwa uncle din waya na sanar dashi halinda ake ciki koda akwai taimakon da zai iya mata a kan case din. Banki ba nayi sa,a ranan ya kira waya saboda haka nake kwance jiki ba lakka said ga kiranshi bayan sallah la,asar na dauka muka gaisa dashi jin muryana da yayi wani iri yasa yake tambayana meke faruwa ? Dan jim nayi kafin na amsa da babu komai yace your voice sound like kamar baki da lafiya na danyi murmushi kafin nace dashi kawai dai iam not in good mood ne yau din. Ya tambaya da sauri akan me fa nace kawai labarin wani cousin brother din mune ya samu matsala sai naji yace wanan da aka kama a abroad ? Cikin mamaki na tambaya kasan da zancen ne yace kwarai kuwa nasan komai saidai laifin ai babbane sosai don hakane kowa baya son saka kanshi ciki. Amma aiba laifin shi bane asalima kayan da ake tunanen nasane ba kayan shi bane sheri akai mashi kuma sunki bari yayi bayani. Yaya kikasan da hakan ke ya tambayeni Dan murmushi na sake tare da fadin na sanine mana haka zancen yake yanzu haka wa yanda sukai mashi sherin suna kokarin barin kasan ta ruwa . Nan na kara mai bayanin komai tare da rokonshi a kan ya taimaka muna please son case din ya zo da sauki da sauri yace ta yaya zan jefa kaina a wanan case din mai karfi haka ? Akan mutanen da har gobe nasan ba sonki sukiyi ba fatima tareshi nayi da fadin koda basu sona sune dai yan uwan nawa dana sani kuma nake bearing din sunan iyayyena a yanzu. Dan ajiyan zuciya ya sauke yana fadin yanzu ya kike son ayi ke nan don dole risk zan dauka na jefa kaina a cikin wanan case din don ba karamin case bace tunda ba a Nigeria aka kamashi ba. Bayani nayi mai yadda zai gane yayi shiru yana saurarena har saida na gama kafin yace anya kuwa Sahiba ba kina ganin har hanji ba ? Wanan irin bayani haka kamar a gabanki akai komai yanzu na gamsu indai hakane abin ba zaizo da wani matsala ba sosai insha Allahu. Shirun da yajine ba amsana yasashi kallon wayan shi muryan fatima yaji tana kwallamin kira kamar a cikin tashin hankali bai kashe wayan tasaba yanajin duk abindake faruwa alokacin wurin. Innalillahi ya ambata hankali tashe kafin yayi dabaran kiran layin fatima din yayi mata bayanin abinda zatayi min a lokacin. Wanan karon ban wani sha wahala sosai ba na mike don yanzu abin nawa akwai sauki sosai ba kamar dacan da mm nake wahala sosai ba idan ya tashi min. Barcin nan dai da nakan yi shinayi alaman sun sauka min a kai kenan lokacin kodana falka magariba tayi a lokacin. Duk yadda yadda yan uwa sukai tsamanin zancen ya wuce hakana yanzu a garesu don labari yazo masu cewa ai har an kashesu ko don an kamasu da babban laifi maigirma a kasan don haka aka halbesu. Ranan wayan gwaggo hari ya tayar damu barci karfe hudu da rabi na safe da kukanta take fadamuna cewa sun samu labarin cewa an halbe su boy don Allah na bincika masu gaskiyan zancen suji. Nima salati na saka a rude kafin na jawowa kaina natsuwa ina bata hakkuri tare da fadin gwaggo ki natsu wanan maganan ba gaskiya bane don ko jiyan nan munyi waya da uncle ya fada min ya samu ganin shi. A cikin wani irin karagi tace ya ganshi fa nace kwarai kuwa gwaggo don insha Allahu da alaman nasara sosai a case din. Sai naji ta sake wani irin shesheka kuka lokaci guda wanda nima yasani sake hawayen da suka taru min a fuskana lokacin. Wanan labarin ya dan karfafa mata gwiwa har yan uwa sun fara cika mata gida da sunan makoki da tayata jimame kan matsalan sai gashi ta fito tana fadin insha Allahu boy yana nan dawowa don ko jiya mijin sahiba ya ganshi har sunyi magana dashi. Nan take aka dauka zancen ya tabi zuciyar tane harta fara sakin magana haka taci gaba da fadin insha Allahu sahiba tace zai dawo gida da yardan ubangiji. Nan yan gulma suka samu nayi don basu yarda da abinda take fadi ba sun dauka zancen ya fara taba mata kwakwalwanta ne haka. Sai sam basu yarda da abinda take fadin ba wasu nacewa ina wani mijin sahiba can zai iya fitar dashi a wanan hatsarin daya fada ? Ya Abubakar duk da yadda suke da mustapha din yaji zafin kamashin da akace anyi munyi waya dashi yake fada muna sai dai ta Allah amma yana da wuya a fito dashi sai ban gaya mai zancen kokarin da uncle keyi ba a can din. An dai sha wuya hankali ya tashi sosai Allah da ikon shi watan su hudu a can sai gashi anyi nasaran fito dashi din ta hanyar kamo masu laifin aka wankeshi. Uncle da kanshi ya dawo dasu Nigeria bai fadawa kowa zuwan su ba sai ganin su gwaggo tayi tare baikai awa biyu ba ya juya zuwa Maiduguri. Ganin mustapha din ya fito ta hanyar uncle mukhatar ya kara daga darajan shi dani a idanun su tunda sunga yayi abinda basu taba tunanen zai yuyuba ga mustapha din. A sai zuwa barka da arziki akewa gwaggo hari kowa yana fadin albarkacin bakinshi a lokacin irin yadda a yanzu nayi masu rana a cikin su bayan sun wofintar damu a baya. Don ba,a dade ba da nayo masu aiken abubuwan azumi dana aikowa dangin mu ga baki daya har wa yanda ke yola dana nan garin kaduna daga ciki kuwa har da na Family din Alh Nuhu da Alh gyade da suke tsare har lokacin a gidan wakafi amma haka na aiko masu da kayan shiga azumi. Suma lokacin da baffah hamza ya kai masu kayan abincin dana tea din saida suka so su nuna bore wai ba zasu karba ba inji yaranshi. Amma iyayyensu mata da wahala ya gama kamasu zuwa lokacin sukace ai ba a haka tunda har na nuna kulawa a garesu kada suga laifina su dubi laifin iyayyensu maza kawai. Shima baffah hamza ya dora masu da nasiha kan tunda har ban nuna komai ba duk da irin laifin da akai muna amma ina nuna su yan uwanane na jini ya kamata suma su sauke makaman su hakana a kan mu. Su kwatanta idan sune mahaifinmu ya raba mahaifinsu da duniya yaya zasuji a ransu a kan mu sai jikin su yayi sanyi inda akai masu mm asiha sosai har wasun