Sashe 72
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Da malamai sukace ba a haka ai sai suke cewa ai duk rabin dukiyan mahaifi su ya kare ne a wurin shi don haka ba za, a raba dashi ba abin har yakai alkali ya tashi daure shi don tijaran da yayi a kotu din. Don shi wanan yaya Nuhu din haka yake da tijara dan duk a tasha yayi rayuwan shi gun shigowan su kaduna da zama. Shiya kowa a cikkn yannuwan su yake kafa kafa dashi don sun taba wani rikici da maigidan nan soka mai yuka har aka kulleshi akace suna yara a lokacin. Umma me i hate d man ma self before i see am wallahi na fada cikin kunan rai da takaicin jin wanan labarin nasa da nake ji yanzu. Umma tace kada in soma in nuna hakan koda wasa a gaban kowa idan nayi hakkuri wata rana zan kamashi a hannu ne don Allah zai daukan muna fansa a gareshi. Kwance makai ina hadiyan zuciya kowa yasan yadda bafulace yake wurin zuciya ina faman saka yadda shima zan halakashi da hannuna. Umma ta fahinci me nake tunane sai naji tace min ranan da duk naji kin nuna masa wani hali a yanzu ranan zan bar maki garin nan in barku a cikin su ga baki daya daga ke har kaninki. Jin hakan yasa nayi wani irin ajiyan zuciya mai karfi wasu hawayen suka kara zubo min ina tunanen ni yaya zanyi in ramawa mahaifina zaluntar shi da akayi. A sannu yan gidab suke dan jan mu a jiki muna sabawa dasu duk da ba hausa a bakin mu sai dan turancin lagos da mukeyi da yarbanci. Har kwana uku wanda ya kawo mu bai shigo gidan ba ko ya shigo ne dai bamu ganshi bane oho ? Gashi wani lokaci sai naji na tsani wanan matar da akace ai mahaifin su daya da mahaifina idan na tuna da abinda sukai mashi a jikin shi. Itama umma na kula ta dan sake jikinta a duk da ko yaushe tana daki bata dogon motsi a gidan baka ma gane cewa muna gidan da zama din daga can ciki muke zaune idan ba mun fito bane har wani ya ganmu. Zancen karatun mu ya taso muka koma makaranta duk da yanayin karatun ba daya ba saidai munyi sa, a don karatun can yafi na nan da muka sama don haka mun samu an sakamu ajin da daddy yace a saka mu din. Mun ake kaiwa da safe makaranta don muna riga manyan yaran gidan fita zuwa school don haka tare dasu Amira diyan hjy karima muke tafiya school din. Da farko ba wani abinda ke hadamu da yaran sai yaran suka fara kawo muna rainin wayau suna kiran mu da wani suna da bamu fahinta ba. Ranan na dawo na tambayi umma meye ma,anam kalman tace a ina naji nace da ita a bakin diyan hjy karima suke kiran mu da yan cin arziki. Salati naga umma ta fara tace dole mu bar gidan nan don zaman mu a wanan gidan ba zai yuyu ba kan wanan matar da yayanta. Nace umma ta barmu dasu don ko mun bar gidan nan cikin wahala zamu kara komawa kuma bamu san inda zamu dosa ba ai idan mun bar nan din. Bayan kwana biyu da yin tambaya gun umma din sai ga yaran sun kara kiran mu da wanan sunan nace na your mama be dat . Na kaiwa yar yarinyar duka tare rankwashe har muka dawo gida sai darzan kuka takeyi mota na tsayawa ta fita da gudu zuwa gidan ta rafka ihu uwar dake kwance tana barci ta fito a gigice ta na tambayan abinda ya sameta tace nice na doke ta ai kuwa nan fa tayo kaina ina shigowa ta tsare hanya a cikin sababi tana nunani da yatsa a cikin sababi. Na kyaleta ina kokarin shigewa ciki ta hankadone baya nayi tangal tangal kamar zan fadi na ja na tsaya take na fulanin suka kawo min nace a hasale dont beat me again if not i will show u my true clour now , , , , ,