Sashe 181
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
farga da hakan ba sai wajen kofan masu gadin get dakeda dan tazara da inda gidajen namu suke. Kofan na bude saidai basu cikin daki ga takalman su nan a kofan da alama sun gudu ko an daukesune muka fara zargi . Tambayan sunan su na fara yi aka ce Lukas da Barau suke ba wani tsoro a zuciyana ko fuskana sabanin sauran jama,an wurin da suke a firgice lokacin. Hasken wayan dayan mutumin na karba na fara bin inda abin ke kuka na fara karanta addua a bakina ina tafiya zuwa wurin da kukan abin ke fitowa. Innalillahi wa, inna alaihim raji,un wani mugun halittane a wajen kamar an masa tarko shi bai shigo compound din wurin ba kuma bai tafi tankar kafeshi akayi. Dabba zan kira abin da suna ko dodo gaskiya idan na tsaya fada zan bata lokaci haka yake kamar kosassan karya amma yafi karya girma da abu najen kasa kamar nono a jere har kasa. Bindin shi kawai yakai kaurin wani katon kare fuskan shi kamar hallitan alade amma a sabule zakace tsokane kawai baida fata ya wani irin walkiya na tashin hankali. Mutum biyun da sukai karfin halin biyoni a baya sukai saurin juyawa da sauri acikin tashin hankali sukuma sauran na ganin su suka arta cikin compound din a guje har wasu na ihu. Kowa yace a zamanin nan ba dodo ya tubawa Allah don har gobe akwai sauran halittan boye da Aljannu masu rikida su koma irin don tsafi. Daga inda nake na fara fadin kayi ko kiyi gagawan komawa gun wanda ya turo ka daga yau kada ka kara dawowa aike a cikin garin nan har abada. Kamar mai jiran a bashi umurni ya fara tafiya yana wani irin kugi da numfashi ya nausa yayi yamma ya bace a cikin duhun dare. Saida suka kai basu ganni bane wasun su suka juyo dan dubani din a hanya muka gamu dasu ashe sauran makwabtan unguwar tamu duk suna tsatsaye cikin tashin hankali. Washe gari kan ace kwabo labari ya karade ko ina a cikin gari ga wanda Allah ya nufa ya ji wanan labarin . Kowa da fassaran abinda yake fada wasu suce ai dodo aka gani wasu kuma suce masu maita ko tsafine da suke rikida suka zama hakan suka fito yawon dare. Rana ta baci masa ua kafe a wurin nikan tunda ba a fita office weekend ne barci nayi sosai ranan abina. Sai daya na mike nayi wanka tare da alwala nayi sallah umma ne ta lekoni ina addua take fadin in fito naci abinci saidana shafa na saka kaya na fito daga dakin. Na zauna na zuba abinci na fara ci ke nan mukaji anyi nocking din kofan gidan Amar ne ya amsa yake fadin waye yana bude kofan. Ganin mai nocking din yasashi dan sake murmushi yana fadin wellcome broda tare da dan rusunawa kadan ya shigo da sallama rike da hannun Amar din ciki yana gaida umma. Ta amsa mai da dan fara, a tare da tambayan shi iyalinshi ya amsa cikin jin dadin hakan kafin na dago ina gaidashi ya amsa min. Ya su mommy da yara shima din ya amsa da lafiya kalau yana juyawa wurin Amar tare da tambayan shi ya yake yana zuwa makaranta ko ? Ya amsa da eh mun fara zuwa a nan har an fara muna test kuma naci dukka, gaban shine ya fadi don kama da Amar a yanzu yayi da mahaifin mu sosai don duk zuwan da yakeyi wurin mu bai taba ganin wanan kamar namu da mahaifin mu ba irin yau. Don gaskiya duk wanda yasan Abbah mu yasan duk muna kama da Abbah mu sosai saidai shida yake namijine yafi kama da Abbah din sosai. Umma yanzu nake karantawa cewa wai jiya an samu dan matsala a wanan unguwar wani abin firgita ya ziyarci shiyan nan da fatan wanan matsalan bai shafeku ba dai. Bai shafemu ba kuma bana zaton akwai wanda ya shafa a cikin wurin nan Allah ya kare kowa dake cikin nan wurin dama wasu makwabtan unguwar nan. Saidai hakan ba karamin daga muna hankali yayi ba don gaba daya jinyan ba wanda yai barci da dadi saboda tashin hankali. Idan wurin nan babu security daya dace gaskiya ya kamata a canza maku wuri kada sani abu yazo ya sameku a nan din. Daga inda nake zaunen na sake kallo shi naji yaci gaba da fadin ina tsaron kada wani abu ya sameku ne umma don garin nan baida kyau yanzu kaduna ba kamar da can bane. Ba abinda zai faru da yardan Allah don akwai hadin kai sosai a cikin wurin nan kada ka damu da hakan. Kafin tace dashi wai da gaske ne zancen auren yar uwarka ko shirmen Faizace kawai irin da sukeyi ? Kwarai mama zasu aurar da ita ga dan gidan uncle gyade yayan mommy, yaya gyade dai gyade dana sani zasu ba yarinya karama kamar wanan din. Allah ya kyauta amma shi Alh ina nufin yaya mahaifin ku yasan wa yan nan mutanen kuma ya yarda ayi wanan hadin ?. Eh yace min uwar ce ta nuna ita dai tunda yarta naso abashi ita har hakan yaso saka rikici a tsakanin su da farko. Fuskana da hannayena ne kawai a wayan da nake tabawa din lokacin amma hankalina yana wurin zancen da sukeyi Waye wanda zata aura ke nan don ba gama sanin yan uwan namu dama nayi ba tunda a boye muke a cikin su lokacin kamar mujiya. Sahiba aikin ku na tafiya kamar yadda ya dace dai ba matsala ko sai lokacin na dago daga inda nake saman kujera a gaban dinning din na dan kallo shi ina murmushi nace. Ba matsala saidai halin mutane ne sai an fito masu a inda basu zata ba don basu da niyar bamu hadin kai muyi aikin daya kawo mu. Kenan sai kun hadasu da hukuma ko wani abu makamancin hakan zasu dauki abin serious sosai haka nake tunanen yi a karshe . Baida matsala tun farko na fada maki ai idan da abinda zan taimaka maku dashi dai ki nemeni na danyi murmushi ina fadin lokacine baiyi ba na neman ku idan yayi zamu neme ka mun gode. Nidai ban yarda na fadi komai ba cikin zancen su don sai naga zancen manya ne bai shafeni ba ai. Mikewa tsaye ya don tafiya bayan ya dan duba agogon sau barkatai umma tayi maigodiya da kulawan shi a kan mu ya fice daga gidan har saida ya tayar da motan shi na sauke ajiyan zuciya a hankali. Bayan tafiyan shi zancen su da umma ne na auren baby ya tsaya min a raina akan me za ayiwa baby aure ga su anty Nabila da anty hauwa a gida. Amma sai baby din ce zatayi aure toshi wanda zata aura din waye shi waye mahaifin ta kuma danaji suna magana akan shi. Shi kawai nake son sani dan haka naji kawai duk yadda za ayi zan halarci wanan bukin da zasuyi a gidan su saidai ta yaya zan tunkare su gida.