← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 337

Sashe 22

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Likita yazo round ya duba Amar din yaga ya samu sauki sosai don haka yace zai bamu sallama zuwa yamma idan yaga yadda jikin nasa yakara samun sauki.
Ranan umma ta dan daure ta fita har ta shiga gaida hjy nan datake taimaka muna tun haduwan mu da ita.
Sun dan dade suna hira tana jan umma da dan hira sai dai duk dabaran ta umma bata yarda ta fada mata komai daya shafi rayuwan ta har ta fito.
Ta samemu zaune muna hira da Amar din dake zaune saman kujera tana shigowa dakin nake fadin umma kinji danki ko .
Wai keke za a saya mashi idan mun koma gida da kudin nan wani irin kallo umma ta watsa muna kafin ta juya ta kalli kofa ta koma da sauri ta rufo kofan ta dawo wurun mu duk muna binta da kallon tsoro dan yadda tayi din.
Ku saurareni kuji a binda zan fada maku dukkan ku a yanzu kada inji wanan zancen a bakin kowa duk tambayan da wani zai maku akan zancen yaron nan daya bamu kudin nan kuce baku sanshi ba.
Mena fada maku muka amsa da bamu san shiba har muna kada kai kada ku nuna tsoro a fuskan ku ko kadan don nuna tsoron ku zaisa su dauka mun sanshine.
Shiru mukayi gaba dayan mu na dan lokaci kafin can na dago ina fadin umma wani abune kuma yanzu ?
Babu komai jikinane kawai ke bani cewa akwai abinda bamu sani ba a game dasu kawai nayi shiru ina tunane saidai na kasa gano komai a yanzu.
Dakin yayi shiru na dan wani lokaci kuma kafin Amar ya mike ya koma saman gadon ya kwanta.
Allah ya gani nice duk silan jefa umma a cikin wanan halin damu kan mu ma yanzu idan wani abu ya samu umman mu fa ina zamu saka kan mu na tambayi kaina.
Dakin aka turo likitane tare da nurse suka shigo ya dan kara duba jikin yaron kafin yace zai bamu salama sai mu tafi gida.
Najin dadin jin hakan don na matsu mu bargidan saida likitan ya gama bayani ya mikowa umma wasu kudi yana fadin canjin mu ne da suka rage ta bamu kudine kuma masu yawa.
Saida muka shiga mukaiwa hjy nan sallama take tambayan umma lamban waya umma tace bata da waya ita ai.
Tana mamaki take fadin har da ke nayi murmushi tace a kwatanta mata gidan mu wata rana zata kawo muna ziyara.
Nan dai mukai mata kwantace ko ta gane ko bata gane ba muka kara gaba abin mu muka barsu a asibitin don sukan basu san ranan sallama ba sukace.
Kamar ba asibiti muka fito ba don yan gidan ba wanda yai muna an dawo lafiya ya maijiki.
Karshe mu muke gaidasu da u na weldone su amsa muna a gadarance da thank u jo mu wuce har muka kai dakin mu da har lokacin a hargitse yake.
Umma taga yadda aka tone dakin wurin bincike ta tsaya nikan ban tsaya ba dole na shiga gyaran dakin namu don ba zamu iya zama haka ba dakin a hargitse.
Nan dai har na gyara suka koma ciki ni kuma na dan tsaya waje ina wanke wasu kayan mu a lokacin ne naji gudu na dago don ganin me akewa gudu din.
Yan sandane cikin wani irin kaya mai ban tsoro suka shigo gidan yasa kowa ke gudu zuwa dakin shi ashe.
Nima na shige dakin mu na mayar da kofa da sauri na rufe suna shigowa gidan mukaji ana sanarwa kamaf haka.
Mun san kana cikin gidan nan don haka ka mika wuya a cikin saukin kai a hankali na kalli umma ina fadin wa sukazo nema umma ?
Bakina ta kaiwa duka tana fadin inyi shiru da surutun tsiya can mukaji na banke banken kofan muka kara make junan mu mu uku a dakin a cikkn tsoro har suka kawo dakin mu da ba wani kofan kwarai ke garemu ba dama.
Wani dan sandane ya shigo yana fadin ku shigo kofan a bude take ya shigo babu dadin gani yana bin ko ina da kallo.
Har kayan mu ya dan dadaga ya fita yana fadin bai wanan dakin karshe suka tataro kowa na gidan dayan su ke nuna muna photon wani guy yana fadin mun san wanan kowa yaba hirgiza kai mukace bamu sanshi ba.
Wani tsawa ya daka kowa ya firgita yace a gidan nan yake har tsawon mako hudu yake nan ma shiriru akayi ba wanda yace ya san shi a gidan.
Sunyi iya binciken su basu gane komai ba har suka aikinsu da yan tambayoyi akace ba a sanshi a gidan suka gaji suka tafi bayan sunce zasu sake dawowa

ZAINAB IDRIS MAKAWA

qANA DARA GA , , , , , , , , , , ,

1️⃣0️⃣

BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , ,

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM WA, LAL DALIN AMIN, , , , ,

YAR UWA PAID NOVEL NE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE KACAL YAR UWA.

Hankalin mu bai kwanta duk da sun wuce sun bar gidan amma kowa na waje cirko cirko ana faman mayar da magana kan zancen.
Dukawa nayi naci gaba da wankin kayan da nakeyi daga can bayana naji muryan wale na fadi.
U sahiba wen wan trobe for ur self thank god that day d man no kill u sai kowa ya kallo ni na daga ina fadi.
Wale, i beg , me i no wan wahala wooo, mey u no comfire me wit that men sha bi i no dem before ?
De fall me down, nd my food dont fawl, nayi i say mey de pay, nd de pay me , de give me anoda food ogwa ? witin consen me with dem again ?
Maman shi tace dashi, wale may u no cary ur wahala come rich me shabi u no say dat mater no be smol case wooo .
Uwar ta kwaba shi tana koran shi daga gidan ya fita yana wani irin tako na yan iska tabi shi tana zagi.
Na dauki kayan dana wanke na nufi wurin da muke shayi a nan idona yakai kan wayan dake kasan yashe bayan wani kwandon roba na kayan iya bisi dake kusa da dakin mu.
Na faki idon mutane na duka na dauka na tura a aljihun dan rigan dake jikina da sauri na karasa shanyin na koma dakin mu har lokacin umma na waje na bi wayan da kallon mamaki ni kadai a dakin.
Ko da ban san waya ba nasan cewa wanan wayan babbace kasancewa umma na waje har lokcin bata shigo dakin ba.
Yasa na fita don zuwa in debo ruwa a inda muke diban ruwa fitana yayi daidai da sake dawowan yan sandan gidan.
Suka zo neman wayan duk an tara mazan gidan da yan matasan mata kan wayan sai binciken su akeyi kan wayan.
Don ya nuna a cikin gidan wayan yake kuma yanzu sunzo signal bai nuna wayan na gidan ba duk an bincika ba a samu wayan ba .
Inda Allah ya taimakeni shine ba wanda ya kawo ranahi a kaina cewa wayan yana hannu na a gidan har yan sandan suka tafi don ya nuna an bar gidan da wayan lokacin.
Chapter 22 · 0% Book details