← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 226 OF 337

Sashe 226

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mun fita da tawagan mu don yo sayayyan tsaraba a lokacin na dan sawo abinda nake bukata a zuciyana daidai wani har umma da Ammar da yaran Abdul makwabcin mu don sune yan uwa na kusa a gareni yanzu da nake ji dasu. Har lokacin sosai nake jin zafin zancen Ganiyat a zuciyana wanda ba ita nake jin zafi ba sai ogan mu da mahaifinyar su da suka dinkeni ta baibai ba gyara ba dalili zasu dora min wahala a kaina. Ni sam ba zancen soyayya a zuciyana don banma taba jin son wani ba balle harkan soyayya ya wahalal dani haka yadda ta dauko min din. Sai ranan da zamu tashi da rana ne an fitar da kayan mu gaba daya zuwa airport kowa yana mamakin irin kayan dana saya bance da kowa kala ba muka fito a nan muka hade da Alaja data fito don yin sallama damu gaba daya sun hadu a reception din wurin a lokacin ne muka fito ni da yemisi a karshe. Tun kan mu karaso wurin mukai arba nida ita haka kawai naji gabana ya fadi abinda ban saba jiba ga kowaye na kalla kuwa bana jin komai ga mutum ni. Amma haka na daure na karasa wurin har kusan inda take zaune muka gaida ita a cikin ladabi ta amsa ba yabo ba fallasa tana juyawa wurin jimoh taci gaba da fadin abinda suke fadi lokacin. Mu zamu tafi na fada kai tsaye ina mikewa a lokacin Aisha Ganiyat ta iso wurin itama a cikin fara a aka shiga mata barka da fitowa tare da sallama . Mun tsaya mun gaisa da ita kafin naji muryan Alaja na fadin munji dadi sosai da wanan ziyaran taku bisa ga aiyukan da kukaimuna shima kuma din ya biya kowan ku hakkin shi dake kanshi. Me yuyuwa wasun ku daga wanan zuwan shine na karshe a garesu wasu kuma zasu iya dawowa da fatan ba zaku manta da halarcin dana ba a gare ku. Don ba karamin kokarin bane daukan dawainiya haka ga mutum ga tallakawan shi harku shida kai tsaye don haka sai ku gudewa Allah ku kuma tsaya a matsayin ku na cin arziki a wurin mu kada mutum yace zai wuce gona da iri don yaga wuri. Saboda hakane tun farko bana son mu rabi tallaka don su ko yaushe gani sukeyi kamar a banza mutum ya samu dukiyan shi . Sai kaga sun rabi mutum sun shige mai jiki kwana biyu sai su bullo mashi da wani hali na daban sabanin yadda sukazo a cikin talauci ka mayar dasu mutane. A lokacin zasu nuna ai dakai dasu din duk daya kuke a yanzu don haka duk maison aikin shi ya kiyaye ya tsaya a matsayin shi na dan aiki ko ba haka ba ? Tana kallon Jimoh take karasa maganan kai haba mama i don't think a cikin mu akwai irin wa yan nan mutane don haka abar zancen nan zaifi. Idan kasan kanka kasan wanine Felix ka bari kawai in fadi maganata don in akwai mai niyar yin hakan ya bari yemisi tace gaskiyane sai dai bana tsanmanin cewa akwai masu irin wanan halin a nan gaskiya. Mu nan ai yarda da sanin ya kamata ne ya kawo mu wanan matsayin bawai on contrac muke ko wani abu ba so banga inda wanan zancem ya taso a cikin mu ba. Aka sari irin tallakan nan anfi samun su a cikin students ko wasu masu zuwa yin safara na kasa da kasa sai kiga sun samu wani mai kudi ko wani kusan gwaunati sun makale suna ha,intar shi ai amma mu nan mun san meya kawo mu na fada. Kai gaskiya kika fada Sahiba Ganiyat dake bayana ta amsa aka sari students haka suke sosai kuwa nace kwarai ma kuwa da sunga mai kudi zasu like su nace tundai mata koda ba kabilan su daya ba saboda kwadan abin duniya zasuma iya auren su don kawai su mallaki kudin shi suci su zama wani abu nan gaba su dawo suna raina mutane kamar da farko suma din abin tausayi bane. Shiru kowa dake wurin yayi lokacin da nake wanan maganan ido rufe Abduhamid ne yazo ya kama hannuna yana fadin ai bakiji ba Sahiba wai saida muka shirya mutumiyar ki ta bugo waya na sayo masu sarka. Da hannu yayi signal sai ga yemisi ta biyo bayan mu da sauri a tare muka fita da ita zuwa inda motocin da zamu bar haraban suke. Karshe ashe a can basuyi sallama da dadi dasu ba don yadda Alaja ta fara zage zage dole a bar wanan abinda yanzu yake ikirarin yasa aiki a gaba yana barnan kudin shi ga wasu. Sai zancen ya koma tsakanin ta da yarta dan a gaban kowa ta fadawa uwar cewa abinda takeyi bai dace ba tayi fada sosai har ran uwar ya baci itama ta fara mayat da amsa a gareta. Bamu dade a airport ba jirgin mu ya daga zuwa Nigeria kai tsaye har lokacin ina dai zaune ne banyi wa kowa magana ba saukan dare mukayi . Don haka saida safe muka isa gidajen mu kamar yadda ya umurci akai kowa har kayan shi gidan shi idan mun sauka mun gama clearence din kayan mu. Ni da Abdul ne zaune a baya sai Adanan a gaban motan tare da driver dake jan motan mu muna zaune a baya tunda naga na sauka kasa na lumshe idanuna a hankali don murna. Ban kara jin dadin hakan ba saida muka tun karo unguwar mu na hango gidan mu wani dadi sosai ya kumeni lokaci guda. Safiyane yara sun fita zuwa school sunyi resuming a wanan satin ya kasance unguwar ya kara yin shiru a lokacin kamar wani brack din sojoji. Motan ya tsaya a kofan gidan nikan tunda muka sauka na sauke ajiyan zuciya da har yasa Adnan juyowa yana min sheri dayin hakan nan na barsu zuwa ciki sai ganina kwatsam umma tayi na shigo gidan. Sun shiga muna da kaya cikin gidan har lokacin ina manne a jikin umma na ban iya yin komai ba sai da suka gama hawowa da kayan nayi godiya suka tafi. Mikewa nayi na shiga dakina dana sama a gyare tsab kamar ina kasan dama don kullun sai an gyara min dakin an saka kamshi a cikin sa kamar ina nan. Wanka na shiga na fito banko saka kaya a jikina ba na nemi wuri mm a kwanta sai wani irin barci mai nauyi koda umma ta lekoni ta samu nayi barci a lokacin. Fita tayi zuwa gaida Abdul da dawowa suna dan hira har take fada mashi cewa ai nayi barci ko a lokacin yace Allah yasa koda zata tashi abubuwan nan sun fita kanta. Nan dai yake ba umma labari sama sama sai kan umma din ya daure don ta kasa fahintar me ya kawo haka tsakanina da mahaifiyar ogan namu. Barci nayi sosai a ranan don sai bayan la,asar na falka nayi alwala na dan saka riga a jikina zuwa falo. Shidai a iyakan binciken shi ya kasa gano dalilin mahaifin su mm a boye wanan file di a lokacin yasa ya kara yarda dole akwai wata a kasa dai tsakanin daddy din da su yan uwan nasa. A hankali ya jawo mota zuwa gida sai dai bai samu Nazifa a gida ba kuma bata fada mai cewa zata fita zuwa wani wuri ba da zai fita. Har ya gama abinda yakeyi ya fito gidan bata dawowa ba restaurant ya nufa yaje yaci abinci inda sabo ya saba da hakan kamar wani gwauron da baida galihu. Yasan dalilin yi mashi hakan don sun kwasa da safe da ita da yake tana son kudi a wurin yau sammako ta buga mai a daki ta sameshi yana shiri take fadin tazo ne taji guduwan mawan da zasu aikawa Abban ta dashi. Do yan uwanta sun fara kawo mm nasu za a saka ido aga ita me zasu kawo a nasu bbangaren jin yayi shiru har ta kare zancen ta baiyi magana ba yasa ta kallo shi tana fadin kana ko jina. Indai jine ina jin ki mana tunda ba kurma Allah yayini ba ke yanzu bakiji kunyar tunkarana da wanan zancen ba ? Kallon shi tayi cikin mamaki tana fadin kunya a kan me don kawai ka taimakawa Abbana kome aida wanine a can gidan ku ko banyi magana ba zaka bayar. Wanan kalamin nata yasa bai kara tanka mata ba sai yaga magana ma zai tsaya ta kara bata mashi raine a banza don haka yai shiru kawai ya kyaleta. Karshema fita yayi daga gidan kai tsaye ya wuce headquater din su wurin aikin da yake son yi a cikin file din nan ranan haka kuma yasa ta fita zuwa gida don su tattauna da mahaifiyarsu. Tako samu a jirace mahaifiyar take da ita nan ta fara mayar mata aikuwa bata kai karshe ba tayi cikin ta da sababi sosai ta zage ta tas tare da mata fadan fitar arziki. Ta kuma umurce ta dace ta koma tayi mai magana a cikin lalashi da ban hankari don idan bai basu kudi mai tsoka suka ba Alh ba wallahi akwai matsala a surin su sosai. Shine ta dawo bayan la,asar ta samu ya fita baya gida kuma taga alaman ya dawo gidan saidai bai dadeba ya fita kuma. Zaman jiran shi ta zauna yi bai dawo ba sai gab da magariba ya shigo kai tsaye dakin shi ya nufa don yana son ya raba jikin shi da kayan daya saka lokaci. Saidaya gama duk abinda zaiyi ya hau gado ya kwanta yana tunanen duniya don shi yasan idan ba gaskiyan zancen nan ya sani ba baida sauran shakat a zuciyan shi don alkawarin daya daukan wa kanshi kan haka sai ya gano gaskiyan maganan. Duk da yana fargaban ace da hannun daddy su dumu dumu a cikin kisan baffan nasa da dawani ido zai kalli ahalin sa a matsayin dan wanda ya kashe masu uba. Ido ya runtse a lokacin yana maijin zuciyar shi tana mashi zafi sosai mutumin da duk wanda zai fadi wani zance akanshi na alherine da yabo. In ka debe wanan matsalan da yan uwa suka dora mai na cewa shi ya hanasu yin
Chapter 226 · 0% Book details