Sashe 65
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bin ko ina na airport din nakeyi da kallo da yanayin wurin duk da garin ba zafi amma naji bambamci yanayi da can din don lagos akwai ruwa saidai akwai zafi sosai a can din idan an tashi yi hakan. Wasu lafiyayyun motocine guda biyu suka dauke mu daga airport din zuwa inda zamu don nan san ko ina ba ni kila gara umma idan bata manta ba ta sani ita. Unguwar su ya kaimu kai tsaye don motan mu daban ce da wace ya shiga shi saidai abinda na kula dashi tun shigan mub motan umma batai magana da kowan mu ba sai addu,an da take faman yi a bakin ta. Haka yasa nima nayi shiru ina yan adduan dana saba a bakina na neman tsari ga abinki da dan adam yakeyi don neman kariya. Daga can cikin motan da yaya Abubakar yake yake waya tare da tambayan daddy da fadin daddy na shigo kaduna kana gidane yanzu ? Daddy din ya bashi amsa da eh moddibbo ina gida ai kasan baja fita da dare ni bayan magariba ina gida ko wani lokaci. Na sani daddy zamu karaso yanzu mu sameka a falo ya fada kai tsaye yana kashe waya yabar mahaifin nasa da mamaki don sam bai kawo da mu din yake tafe ba saidai tunajen shi da wasu bakin abokan aikin shine kila yazo don yadda yaji yana masa magana a gurguje da alaman dai akwai wani abu. Don haka daddy din ya mike zuwa falo inda suke karban bakin su a gidan hjy karima da zata shigo da ruwan zafi a flask ta tsaya tana mamakin ganin ya fito take tambayan shi don a zaton shi wurin hjy zai tafi. Ina kuma zaka a wanan lokacin ta tambayeshi wucewa yayi inda zai tafi kai tsaye ta juya ta shiga da flask din dakin ta aje. Wani get da sojoji ke gadin gidan aka bude motoci suka shiga lokaci guda darene a lokacin don haka kowa na cikin gidan sa a lokacin. Saida yayi magana da umma kafin ya juya ya fara tafiya zuwa ciki muka fito daga cikin motan kai tsaye duk da tafiyan dadi mukayi ba mota muka bi ba jirgine kuma daga airport zuwa gidane a yanzu. A hankali muka fara bin bayan shi zuwa cikin gidan daya dosa din muna binshi a baya ya rigamu shiga ciki yake fadin daddy ashe ka fito falon ko ga bakin naka nan na kawo maka zasu shigo. Baki daddy ya tambaya a cikin mamaki don bai fahinci dan nasa ba sallama umma data daga labule tana shiga dakin tayi muna biye a bayan ta muka shigo. Da wanan bakon yaren da naji umma tayi nan ma din shi take magana dashi da wanan daddy din a cikin yaren filatanci. Naga ya daga kamar a firgice da mamaki karara a fuskan shi yana fadin Mairo kece ta hanyar nunata da yatsan shi har hamnun shi na rawa. Umma tace nice yaya ina wuni mun sameku lafiya ya bayan rabo takai kasa tare da dukar da kanta kasa tana hawaye. A cikin karfi hali na iya fadin good evening sir sai lokacin ya dan kalli inda muke ina saye da wando wanda ke hade da riga blue sai gyale fari da nayi rolling din kaina dashi. Innalillahi wa inna alaihim raji,un ya fada yana mai kura muna ido dani da kanina da muke tsaye kimkyam muna kallon shi muna na rike hannun Amar din koda taka taso a hakan. A hankali ya dago hannu yana fadin come to daddy kids da sauri kamar muna jiran jin hakan daga gareshi muka nufi inda yake tsaye din ya mika hannayen shi garemu muka fada mai sai kuka yazo min jin dumin jinina da nayi karo na farko da wayau na a jikina. Kuka sosai nakeyi shima Amar ganin inna kuka yasa ya barke da kuka daddy ma da ya Abubakar duk kukan sukeyi ba mai bawa wani hakkuri a falon. Jin kukan ne da iyalan shi daga ciki sukaji Nabila data fito zuwa kitchen taji ana koke koke a falon ta koma da sauri ta fadawa hjy yasa suka fito gaba dayan su. Anyi daidai itama hjy karima taji tafito duk sukayo falon gaba dayan su lokaci guda kowa yaja yayi turus a cikin katfin hali hjy din ta karasa tana fadin. Lafiya Alh suwaye suka zo haka ta fada don umma kanta yana duke tana rusan kuka don haka bata shedata ba a lokacin. Har lokacin da hjy ke maganan muna jikin daddy din muna kuka sosai shima yana hawaye maidan sauti kafin ya dago yana fadin . Addah kunga halin da rayuwan yan uwan mu diyan mu yau yake ciki saboda sakacin da son kai irin na wasu daga cikin dangin mu ko ? Jin an ambaci sunan hjy Addah da umman mu tayi yasa ta dago kai a cikin sauri tana kallon inda hjy din take tsaye suna kallon mu cikin tuhuma don irin hjy karima kan ta dauka mu din diyan daddy ne na cikin sa daya haifa da wata mace a ganuwar aikin sa a lokacin da yake fita garuruwa yin aiki. Hjy Adda ko ba wanan tunane tayi ba ita zuciyar ta yafi tafiya da cewa wasu ne dai can na daban da suke da alaka dashi daddy din. Dago kan umma sai a idon hjy Adda din wani iri tayi ta danja baya tana dafe kirji da fadin Mairo kece a gabana ko mafalki nakeyi. Sai ta kai zaune saman kujeran dake bayan ta tare da sake hawaye suna zuba mata lokaci guda. Da kyat ta iya budan bakin ta tace Mairo ina kika shiga haka tsawon wanan lokaci haka kin tafi babu labarin ki bana diyan ki. Hannu daddy ya dagawa hjy daga inda yake tsaye din hjy tayi shiru hannu daddy yasa ya dagoni daga jikin shi a hankali ya fara min magana kamar rada yana fadin. Stop crying my daughter daddy is with you now yasa hannu yaci gaba da share min hawaye kafin ya koma wurin Amar ya kara jan shi a jikin shi shima. Hjy karima dauke su ki kaisu part din can na ciki da babu kowa ku kuma ku dauki yar uwar ku kujata zuwa ciki . Yana fadin haka ya juya inda Abubakar ya ke zaune yana fadin jeka gida ka huta harda safe yana fadin haka ya mike shima dan nasu ya mike ba tare da yayi magana da kowa ba ya fice gidan zuwa gidan shi. Falon ya saura damu dasu hjy ana kalo kalo kafin hjy karima tayi karfin jalin fadin mujeku zuwa ciki ku huta. Da kyat umma ta iya mikewa har lokacin tana rusa kuka mai tsuma zuciya tabi bayan hjy zuwa ciki muma muka bita. Wani part din su dake can kuryan gidan aka kaimu kafin Asabe mai hirkin gidan ta kawo muna wani lafiyayyen abinci sai kamshin ke tashi na man shanu a cikin sa. Duk muna zaune a cikin dar dar har lokacin kafin hjy Addah din ta shigo dakin Asabe da yaranta na biye da kayan mu da muka bari a cikin mota. Hjy Addah din ce ta nuna inda za a aje muna suka aje suka fita yake fadin Asabe ki dauko abin shara ki gyara dakin nan don Allah. Kafin ta juyo tana fadin au har yanzu zaune kuke gara ki saki jiki ko yaran nan zasu sake nasu jikin ki tashi Mairo kishiga bayi kiyi alwala kiyi sallah kuci abinci lokaci yana kurewa. Tashi umma din tayi zuwa ban dakin data nuna mata kafin ta juyo inda nake zaune bakin gadon tana fadin . What is your name na dan dago manyan idanuwa da suka rine nace Sahiba ma ta nuna Amar tana tambayan shi yace Amar ta dan kura mai ido sosai kafin ta numfasa tace feel free tana dan taba kafada na. Dan murmushin yake nayi mata kawai na dukar da kaina kasa na dan lokaci saiga wanan mai aikin ta shigo take fadin yawa Asabe a canza masu zanin gadon nan a gyaro ko ina matar dan uwanane data bata da yaran da dadewa Allah ya baiyana muna ita. Aikuwa ga kama nan da diyan na gani sosai ta fada tana kallon mu tare da fadin sannu sannun ku da zuwa. Ai da alama wa yan nan basa jin hausa nake gani tare da dan kallon mu din kafin ta juya wurin Asabe din tana fadin don Allah fara da falon sai su koma can su jira har a gyara nan din. Daga haka ta juya ta fice dakin yadda tace hakan akayi don mun koma falo aka gyara bedroom din. Umma tayi muci abinvin mun kasa don wanan kamshin manshanun dake ciki bamu taba cinsa ba sai wanan ranan haka aka rufe abincin ko umma bata cisa ba. Haka muka kwanta a takure a dakin da muke din saman gadon dake dakin zan iya cewa ranan umma batayi barci ba don na falko da dare na sameta tana sallah. Na dawo na kara kwanciya sai barci don dadin barcin da nake ji a lokacin ban san a inda ma muke ba don ga gado ga sanyin AC duk a dakin. Washe gari koda muka falka gari ya waye umma tana zaune saman salaya din da tayi sallah a wirin tana dan jan tasbi ta tare da maida gaba gasbas tana kallo. Ban dakin na shiga na yo alwala nazo nayi sallah ina gamawa na gaida umma na shiga gyaran dakin da muke din har falo saidai ban yarda na leka wajen gidan ba don gidan ma tsit yake a lokacin kamar ba kowa a cikin sa. Bayan na gama na shiga wanka na fito na shirya a cikin dan wani gown baki mai dan adon walkiya a gaban rigan. Inda Allah ya taimakeni shine bai yarda ya dawo da mu gida ba saida muka zama mutanen arziki yadda ba za a gamu a raina ba idan anganmu a gida. Don haka kaina yasha gyara ban damu da dan kwali ba hakana na koma na kwanta saman gado sai wani barcin ya daukeni kuma. Muryan hjy Addahce ya tayar dani lokacin da take fadi mairo ya gajiyan hanya yaya yaran