Sashe 162
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nashigo gida na samu umma na shago don haka kai tsaye na nufi cikin gida na bude kai tsaye dakina na nufa kaya na fara cirewa ina wurgawa saman gado kafin na nufi bandaki. Wanka na nufa na fito na saka daya daga cikin rigunan da nake zaman gida dashi ina fitowa kitchen na nufa na dora muna abincin na fara gyaran gida wanan duk aikinane kun sani bana yarda umma tayi don ba lafiya ya isheta ba saboda asman dake damunta. Har na gama girkin nayi sallah kamar kullun sai lokacin na fara jin motson umma sun rufe shagon sun shigo cikin gida saboda dare yayi bata kaiwa dare a ka,idar zaman ta. Nayi sallah isha,i na fito da wayana a hannu ina masu sannu da dawowa suma din gaisheni sukayi haka muka sabayiwa junan mu kullun. Saida muka zauna cin abinci nan na fara labartawa umma zancen kiran wayan da Faiza tayi min ta kiraki fa yau kikace wallahi umma akwai wanda kika bawa layinane ? Dan shiru tayi kafin tace dani kwarai kuwa don naba Abubakar ranan daya tambayeni da bakya nan. Nace haba nikan nayi mamakin hakan wallahi don gaskiya bana bada layina haka barkatai saina yarda da mutum sosai. Abubakar din baki yarda dashiba ke nan Sahiba shikuma macucin mune kome yake biyan mu dashi na girgiza kaina da sauri. To shina gani don yaron nan yana da kirki da mutunci sosai ya nuna damuwa da kuma tausaya muna fiye da kowa da muka sani. Shiru nayi ban bata amsa ba don bana son tana fadin haka dukda nasan gaskiya take fadi amma ni zancen sune gaba daya banson ji. Ban kaiga karasa tunane ba wayana ta dauki ringing na dauka na duba lanban umma itace ko yanzu ta kirani dauka kila shine ya basu layin tunda yaran dama sun damu damu sosai ko zaman mu a can. Dauka nayi tare da sallama muryan Faiza ne tana fadin haba Sahiba ko bakya son magana danine wai tun dazu ina ta kira yafi ashirin wayan ki yana kashe saboda ni kaka kashe wayan. A harshen turanci nake bata hakkuri aina fada maki cewa aiki nakeyi dazun din sai yanzu na dawo gida yasu mommy dasu Anty Amarya ? Anty Nabila da anty hauwa ya su Amira da fatima baby da kowa na gidan tace kowa na gida lafiya kalau suna jin ki ya umma ? Gata ku gaisa na fada ina mikawa umma waya ta dauka itama da hausan ta daya fara rikedewa dana yare a yanzu . Suka gaisa itama tana jero mata tambayan yan uwa da sauran tana fadin ga mommy naga umma ta kashe wayan a nan nagane itama akwai haushin su a zuciyar ta ashe. Ga Mommy ita mommy bata sanda mu bane saida kika nemo yar uwarki zata wani karbi waya wanan zumincin zamani haka dame yayi kama ace yan mahaifi daya amma basu san zafin iyalin dan uwansu daya kwanta dama ba. Wallahi irin wanan nakan tuna a rayuwa har wani lokacin in zauna inyi kuka ina meyasa gwaggo ta zaba min mahaufin ku a matsayin mijina. Da wanine yau muna can cikin yan uwa a mutunce sun san darajan mu muma munsam nasu ana damawa damu amma wa yan nan kan abin duniya idon su da kunnuwan su ya rufe sun manta da cewa akwai ranan hisabi yana jiran kowa. Duk da maganan umma din ya taba min zuciya sosai don ma kusan nafi umma din jin zafin amsam wayan da mommy din tayi niyar karba a wurin faiza din. Sai gashi umma takai ga daukan mataki kafin nina dauka ban taba tunanen jin haka ba a bakin umma danaji din tana fada sai kima gata ta furta hakan yasa nasan ankai karshen umma ke nan. Na bude baki ina fadin kiyi hakkuri umma saukin abindai akwai hissabi ga kowa idan suna ganin haka ba komai ko sunfi tsoron wani Allah da Allah din ai mutuwar data rabamu da mahaifin mu bata bar kowa ba. Shiru falon yayi don tunanen da kowa keyi lokacin shigowan Amar daya sauka kasa bayan fitowana yasani dago kai ina kallon shi. Leda ya shigo dashi gidan yana fadin saida kyar na wanan uwan kamshin da kuma maganan dayayine yasani dago kai na kalleshi da kyau har ya zauna yana aje kumshin a gaban umman mu. Kallon ledan umma batayi ba don ranta da yake bace a lokacin ina ganin haka na bude baki da kyar ina fadin meye a cikin ledan Amar ? Ya sunkuyo ya buda min ledan wani kamshin suya meat irin na hausawa din nan ne ya daki hancina ga naman an masa manyan yanka gashi yana maiko yana fitar da suraci acikin shi kuma na zafi. Jeka kitchen ka dauko plate ka zuba a ciki umma dana san zaku saya ai tun dazun dana tsaya na sawo maku ai saidai nakan ji kunyar in tsaya a irin wuraren nan ne. Amar ya fito da plate dauke a hannun shi yana wani rawan jiki nace kaikan kamar ba bafalatani ba kana rawan jiki akan nama haka Ammar ? Abine yabawa umma dariya tace ashe kin kula dashi kema kamar nayi magana yadda naga yana wanan sabarin jikin haka kamar bayacin nama a kullun gidan nan. Amar yafi ganewa magana da yarbanci don haka yake fadi da yarbanci aiba irin wanan bane muke ciko ? Inda na kara godewa Allah ina jin fulanci saidai banyi don tun ina karama na bude baki dashine amma zuwan mu lagos din mu a sannu yarbaci da pidin ya shige bakin mu saidai umma bata yarda da hakan ba. Tsoka biyu na iya ci a ciki koshi don ta sake jiki na kokarta naci na tsame hannuna na dan shiga tunane kafin nakai ga mikewa ina fadin zan tafi na kwanta kada in makara da safe. Saida na lwanta din amma juyi da tsuki yafi yawa kafin barcin yayi gaba dani nine harda mafalkin su a ranan don kawai dan wayan da mukayi dasu din a ranan. Washe gari kodana kunna wayana text massage na sama a cikin wayan mai tsawo nata banbi ta kansa ba a gurguje na shirya na fito na samu Amar ma ya fita ko zuwa school shi. A gurje na fita gidan don ban son abinda zai ja min matsala a wurin aikina ko kadan don sun tsani wasa da aiki ina ganin yadda sukan sallami ma,aikatan su kan makara shiyasa nake kiyayye hakan a bamgarena. Saidai kash duk saurina kuma na makara a yau don nayi saurin banza saboda ogan mu sha,aban daya zo ashe ba tare da sanin kowa ba ya zo tun safe ya kawo muna ziyara bazata don ko Felix ma kanshi baisan da zuwan shi ba asalima a club ya kwana don harshi na rigashi zuwa. Allah yai min katari a daidai lokacin da ma,aikata ke halartan wajen da muke ganawa dashi na iso don haka nabi layi a tsarge duk da yana tsaye a cikin fararen kaya bai kallo wurin da nake ba amma kuma ai yaga shigowata ciki na nasa a raina. A cikin takon shi irin na mazan da suka waye suka san kan duniya suka kuma zauna da kafan su ya iso har inda muke yana fuskantar mu bai aje idon shi kan mutum daya ba don sai bin kowa na wurin yake da kallo. Kafin yayi gyaran murya wanda hakan ya kara karkato da hankalin kowa gareshi ya fara da sallama a cikon taushin murya irin nasa. Ya fara fadin i am disappoint yau yadda na samu a wirin nan ada kune kusan wa yanda nake alfahari dasu gaba daya out of fiyty five ma aikar da nake dasu wurin tsare aikin su sai gashi yau idona ya gane min kun fara zama kamar kowa ku din ma. Shiru wirin yayi kamar yadda shima yayi shiru yana dan bin kowa da ido kafin ya bode baki da kyar yana fadin why zaku zama haka har yakai na kasa alfahari daku kuma ? Sorry sir aka fara fada maza da matan don ganin yadda ranshi ya baci yake nuna bacin ranshi kuma a garemu baki daya. Jakkata dake rataye a kafadana na gyara kafin na mayar da hankalina inda shima yake kallo din Felix ne ke shigowa da ganin sa a rude yake ya karaso bai tsaya ba sai inda nake tsaye nima a tsarge. Yayi fada sosai ranan duk muna tsaye muna sauraron shi kafin yayi sallama damu a cikin bacin rai ya juya ya bar wurin aiki babba na sauke ziciyana ina nasa hakan. Ba tare dana tsaya kula Felix ba dake tambayana kasa kasa how come oga ya shigo kasan nan ba tare daya sani ba ya jefo min tambayan ko ke kinsan da zuwan shine ? Wani kallo nayi mai ina fadi yaya zan sani shima da yake kusa dashi yace bai sani sai nice zan sani ta yaya kuwa ? Har mun kusa kaiwa inda zamu hau masarrafin da zai kaimu sama naji ana fadin kubiyin nan guys oga yana son ganin ku yanzu. Na kalli Felix a cikin zaro ido shima hakan ya kalloni kafin na juya na shiga masarrafin zuwa sama din inda office offices suke a can sama din. A gidan su ya bar yaran don bai nufi gida ba daga nan ya wuce zuwa wani wuri yana a tsakiyan aikine saiga kiran Nazifa tana tambayan shi wai ina suke ne har warhaka ? Ina wurin wani aiki ya bata amsa a takaice yaran fa ta tambaya da mamaki suna gida wurin mommy na barsu ka batsu can fa kace yace eh da matsalane barin su can din? A,a saidai gaskiya kasan basu saba dasu ba ai kuma mimi nono take sha kasani eh na sani saidai ai akwai abincin ta idan tayi kuka yaran zasu bata. Ji yayi ta kashe wayan sai yabi wayan da dan kallon mamaki kafin ya daga kafadan shi irin alaman ko a jikinshi din nan. Tana kashe wayan na mahaifiyar ta takira bata sameta don haka ta kasa hakkuri don in akwai abinda taki jini a duniyan nan shine yaran ta su rabi kowa na gidan mahaifin su don wai basu son ta. Daki ta mike ta