Sashe 330
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
su suka nuna nadaman su sosai. A Wanan zuwan munje har lagos wurin su umma mun gaidasu mun kai masu dan abin azumi inda umma tayi ta murnan ganina a lokacin. Sai bayan mun samu kebewa da itane ta kallani tana fadin sahiba naji dadin yadda kika kwantar da hankalin ki haka sahiba don da farko hannuna a gaba yake yadda akai auren nan. Amma yanzu ganin ki haka hankalina ya kwanta sosai wallahi gashi ina ganin har da rabo a jikin ki idan ba karya idona ke min ba kila ? Dan murmshi na sake kawai Allah ya taimakeni fatima uwar baki bata jin yarbanci data kaini inda banso don ni cikin jikina bai hana min yin komai kamar yadda na saba ba haka kuma ina cin komai da nake ci a baya . Nafi da son sai cikin ya fito da kansa a gani bawai na dinga fadawa mutane ba don wanan camfin yarbawane haka don baka san bakin wani ba. Haka mukai kwana biyu tare dasu ummu a lagos muka dawo Maiduguri a wanan lokacin ne tawagan yan uwan mu maza da mata sun kai su ashirin sukazo mashi godiya kan tsimakon da yaiwa ya mustapha tare da abin alheri iya karfin su da sunan sun kawowa yarsu garan taron azumine. Yace ai ba sai sun taso ba don sunci albarkacin yai masu hakan a wurare da dama don haka ba sai sin wahalal da kansu ba illa iyaka dai ya kara kula sosai tunda ana binshi da sheri irin haka dole yana da makiya a wani wajen da bai sani ba. Gwaggo hari kasa ne kawai bata kaiba wajen mashi godiya a lokacin na dauka zasu kwana sai gashi sunce a ranan zasu dawo kaduna. Nagode Allah ba wanda ya farga da cikin dake jikina wanda zaikai wata biyar ko shidda a lokacin a jikina amma ya shafe ba a ganin shi sam. Har shi maigidan baisan da cikin ba Inda uwargida falmata duk da abinda ya faru haka baisa ta saduda ba don kullun a cikin barazanan fadi take ba aiwa diyanta yan uba ita. Yadda nazo haka zan koma don kullun a cikin sabon shiri take a kaina duk da bata samun nasara hakan baisa ta daina ba ita. Gashi a yanzu duk wani kafa da zata samu labarina a toshe yake tunda bana hurda da kowa in kin debe yan uwan mijina na kusa su kuma ba zataji komai a wurinsu ba don ba yarda a tsakanin su. Gashi dole zamu bishi zuwa Hong Kong saboda azumi da za a fara haka muka bar Nigeria zuwa kasan amma mun tafi da fatima da har yanzu itace zaune tare dani. Mun isa lafiya an kuma tashi da azumi saidai saboda wahalan tafiya kuma ga laluran ciki da zan iya cewa wanan ne wahalan farko dana farayi kan cikin jikina gaskiya. Wanan yakai saida mukaje asibiti dole aka bani gado na huta don ina bukatan hutu a lokacin barci sosai nakeyi yayin da yabar komai nasa ya dawo jinya ta asibitin. Ina bude Ido shine naga a zaune yana karatun kur,ani ya saka glass a idanunshi hankalinshi ya dauku ga karatun da yakeyi a lokacin . Haka yasa na samu daman kare masa kallo sosai a lokacin don banyi motsi ba shima bai dago kanshi ba a lokacin yana duke yana karatu. A hankali na mayar da idanuwana na rufe lokaci guda ina sauke ajiyan zuciya a hankan na tsukayo muryanshi yana sadakallahullazi. Jin hakan yasa na bude idona muka hada ido dashi yace kin tashi na dan gyada kai ya samu wuri mai kyau ya aje littafin ya mike tare da zare glass din daya manna a idon shi na karatu. Ya karaso zuwa inda nake kwance yana fadin sannu ya jinkin naki yanzu Alhamdullahi na fada ina lumshe idanuna lokaci guda. Yanzu ina ke damun ki yana kai hannunshi a saman wuyana a lokacin ba ko ina na fada a hankali ga abinci nan ki tashi kici . Fuska na bata lokaci don sam yanzu ban son cin komai a cikina duk kwanakin nan ga baki daya duk da ina kokarin wurin ganin ban zauna da yunwa ba. Baki isa ba ya fada yana kokarin jawo basket din abincin tare da fadin kina son ki wahalar da kanki ne da abinda ke cikin ki ku wahala ? Da dan mamaki a fuskana na dan kalleshi sai kuma na dan turo baki lokaci guda ina kawar da kaina gefe abincin ya fara zubamin har lokacin ban kalli inda yake ba. Aje min yayi a gabana sai na kalli abincin wanan dahuwan nasan na fatimane don yadda akayishi ya hadu ba irin da yan aikin gidan da muka sama suke muna ba. Mikewa nayi ina kokarin sauka saman gadon da nake kwance sa sauri ya kalloni yana tambaya ina zaki bandaki na bashi amsa. Bayan na dawone na zauna bakin gadon ya miko min abincin na karba cibi biyu kawai nayi na aje spoon din cikin plate ina kokarin komawa na kwanta ya sake fadin. Likita yace idan baki cin abinci akai,akai zaku samu matsala dake da abinda ke cikin, cikin ya fada yana kallon fuskan nikan dukar da kaina nayi. Banda abinda zance dashi tunda ya riga da yasan abinda nake boyewa a yanzu shi yasa nayi shiru a lokacin cikin jin nauyin hakan da kunyanshi. Kaina na kawar gefe daya na sake jin muryan shi a kusa dani yana fadin akan wani dalili kika boye min alheri da ubangiji ya azurtani dashi tsawom wanan lokacin.? Nasan dole kina da dalili naso ba kaina hakkuri in biki a yadda kike so amma zuciyana ya kasa daure hakan a yanzu don farin cikin da nake ciki duk da kin rage min hakan . Ciki a jikin ki fatima har tsawon wata shidda ban sani ba sai wanan lokacin daya rage saura kiris ki haihu ? Amma banyi mamakin hakan ba don koshi likitan da kyar ya iya gano hakan don da farko ya nuna babu komai a jikin ki. Forget about that yanzun me kike son kici ya sake tambayana yana kallon fuskana dake daure tamau a lokacin kamar banson zancen.