Sashe 35
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
rike addua sosai a bakina kafun na fita. Haka din ne kuwa don dana tashi zan kwaba sai nayi addua idan kuma zan fitar da kayan sai na tsaya naja abinda umma ta koyar dani daga bakin ta na addua. Amma duk da hakan suna biye damu yauma din na tashi a makare don mafalkin da nayi gabanin asubahin. Sai mafalkin ya tsaya min a raina sosai haka na fita na fara share wurin kafin na fitar da kayan mu da dan tocina kamar ance na haska tsakiyan wurin da muke aje murhun da muke suya dashi. Sai na hasko tsakiyan daya nuna alaman an gina wurin anyi wani abu da sauri naja baya ina fadin back to sender may evils eyes rich his sender oba my deat bodi notin will happen to me insha Allah. Hakan ya jawo hankalin sauran abokan kasuwancina da suma sun fito a lokacin suna gyara wurin da zasuyi sana,an su din. What happen omo wata yar matashiyar dattijuwa da itama ta kama wanan sana,an na suyan fanken safen da mukeyi don ma,aikata da sauran masu samakon fita suna saye su tafi dashi don muna a saman hanyane sosai mu. Nace see di tin somebodi do for my place ta duba da sauri taja baya tana fadin eh wai holy ghost fire. Who send dis for u ? somebodi wan see ur down fall at dis place ta fada tana kara ja da baya insha Allahu d evil tin may go back to his sender, notin will happen to me , Wata ta karba da insha Allah ban san ya akayi ba har yan cikin gidan mu sukaji sai gasu sun fito Ladi na fadin. We will see notin insha Allah noti go rich our daughter we no put our eyes on person business, why somebodi will put his eyes on her ? Tazo dauke da wani sabon kwarya a hannun ta da wani ruwa a cikin sa tana ta zage zage tana yayyafa ruwan a wurin kafin ta dakata tana fada. Ranan dai sai da kyat na iya suya sai ummace ta ansa ta karasa min duk da ba lafiya hakan ke bata ba shiyasa ban yarda umma din tayi wani abu nike komai idan ina kusa dasu don yanayin jikin ta daba lafiya. Daki na koma na kwanta ranan banyi sana,an rana ba sai hakan ya tayar wa umma da hankali sosai. Addua ta fara min tana dafe da goshina cikin ikon Allah har na sami barci a lokacin . Ladi kan hankalinta ne ya daga saboda zama a cikin yarbawa duk tasaba da al,adun su nacan bale wa yan nan dake da akidun al,adun su kala daban daban na kauye zama dasu duk yasa ta iya wanan al,adan da akidun su. Ladi farace bakatsina da kalagun ta irin na katsinawa gata dai dattijuwace amma ko yaushe zaka samu tana busa karan sigari ko goro a bakin ta. Yarbanci ko abakin ta kamar zuban ruwa zakace a iko din aka haife ta kana ganin ta kaga tsohuwar yar dandi data sha bariki a zamanin kuruciyan ta. Saidai dadina da Ladi akwai ibada duk da wanan kallon da nakan mata in tsane ta wani lokacin sai wanan ya dan gusar min da abinda nakan ji na tsana game da ita. Ni dai na bude idanu naga umma zaune kusa dani har lokacin tana min addua ga kuma muryan Ladi daga waje yana tashi tana fadin . Turancisu na bariki any person who de try to inter my road i wil show dat person my juju pass am meke hi quick quick live my daughter to live in piece. Da kyar dai ranan na samu nasha tun wanan lokacin umma tace indai sana,a ce a nan na daina ke nan ayi da wani kuma suje suyi tayi. Ladi tace don su za aki neman kudi tun farko sakaci mukayi ai ba a barin irin yaran nan haka su fada gari kai tsaye ba a nema mata tsari ba. Tunda su shegen tambaye tambaye ke gare su da zaran sunga bako yazo cikin su yana samu sai sunyi tambaya a kanshi. Allah ya taimakemu yarki tana da wayau bata dora tunkunya a wurun ta fara suya ba ta farga da hakan wanda nasan karfin adduan kine a garesu Allah ya tsare da sai ta kwanta ciwon da sai Allah a yau din nan. Hankalin umma ya kara tashi ta kara miko min ruwan maganin da ladin ta kawo aka bani sai zufa nake karyowa a jikina. Wanan ne dalilin dana dakatar da duk wani sana,a a cikin semi boda ga baki daya don umma taki yarda in kara yin wani a garin kuma duk da na roke ta ko a cikin gida in dinga yi idan ladi ta yarda da hakan. Amma umma tace sam idan dai wani zaiyi ba bakin ciki ba kyashi amma nikan nagama wanan sana,an kuma. Ganin da umma tayi yau ciwo gobe lafiya yasa ta yanke shawara muje asibitin nan da Amar ya taba kwamciya . Don likitan yace muna da sauran kudi da zamu dinga zuwa ana dubamu a cikkn kudinganin da umma tayi taji sauki yasa ta tattara ta aje zancen asibitin a gefe daya. Gaba dayan mu muka shirya ranan wata alhamis da jikin nawa dai ya kiya muka tafi asibitin bayan likitan ya dubanine ya bamu magani har umma mun fito naji umma tace. Tunda akwai sauran lokaci in kaita gidan hjy na tayi mata gaisuwa tare da godiya ga alherin data aiko muna ranan danaje gidan. Mun sameta a gida tayi maraba da zuwan mu kallo daya tayi min ta fahinci banda lafiya take tambayan umma . Umma ta labarta mata komai daya faru dani tun lokacin nan dai ta tausaya min ta bamu wani maganin gargajiya in shaka nakafa atishawa a nan sai can ya tsaya sai barci. Ba yadda hjy batayi da umma ba kan mu kwana har washe gari mu tafi amma umma takiya haka muka fito bakin titi neman motan da zai kaimu semi boda bamu samu mota ba. Na who be dis iya sahiba na u aka fada a bayan iya bisi ne tana tallan kayan maganin agumo na yarbawa akai. Take fadin ah long time no see dat day one man come to our house e de look for u nd sayiba. He say e bi sayiba father d man look rich he even say he go give amount for person when bring ur torry. Where are liven naw ta tambaya kamar umma ta sani tace da ita we de obalade now we de sell food there. Zama nayi don ban iya tsayawa a lokacin na kurawa titi ido daga can gefen da suke tafiya ya hango mu wani irin burki yaja don shi ke jan motan. Saida na bayan shi yazo ya dakeshi abinda ya dauke mai hankali ke nan a wurin kafin ya juyo har mota tazo mun fada da gudu don kada mu rasa mun bar wurin. Matar da yaga muna magana da ita din ya sama yana tambayan ta ko ta sanmu take fadin eh sai kuma ta nuna shi tana fadin na u come to our house dat day looking for dem ? Yace eh nan dai ta fada mai kamar yadda umma ta fada mata ya ciro dubu goma ya bata ta wuce tana murna shi kuma ya koma masaukin shi saidai bai yadda ya kira daddy ya fada mai ba don so yake ya tabbatar da hakan kafin ya sanar da daddy din. Saboda ya kula akwai wani abinda bai sani ba a cikkn maganan don haka sai yayi bincike kafin ya taimakawa daddy nasa akan mu. Duk da sun kirashi da dare suna sanar mashi da irin haukan da Alh Nuhu yazo har gida yayi masu ya kuma ce ba za a fasa auren ba shi yayi kadan ya basu kunya a gari. Da wanan bakin cikin ya kwana har ya mantar dashi zancen yarinyar daya fara nazari akai dole washe gari ya shirya zuwa gida don ayi ta ta kare a lokacin.