Sashe 47
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abu sun mai yawa lokaci guda na rashin nasaran kama wanda suke nema da rashin sanin koshi waye har yanzu don sunayen da maishi ke amfani dashi na bugi. Sai kuma case din yarinyar nan daya dauka yasa a ransa zaiyi bincike da kyau yasan meye tsakanin su da mahaifin shi don shi hat ya fara zargin ko dai yaran diyan daddy sune a yadda yaga damuwa a tare da daddy din. Hakan bai mai ba yayi saurin kawar da wanan tunanen a zuciyar shi da sauri ya koma wani tunane semi boda ya kira a fili inda hjy halima tace muna zaune yanzu. Kafi kuma yaja tsoki yace wanan wani rayuwane ku kaka gudu kuna canza wuri kamar marasa gaskiya dasu aiko fulani yanzu basu yawan canza wuri haka barkatai kamar ku. Dole yasan hanyar daya bullo wa yarinyar nan ya gano komai nasu kafin daddy ya sake juyowa zancen nasu koma meye idan ba mai yuyuwa bane ya yi maganin abin kafin a farga. Chuku ya fado mai a rai don shine kadai zai iya bibiyan lamarin ya gano gaskiya kamar yadda a yanzu ya gano masu dollers boy dake ta faman yi masu yawo da hankali saidai har yanzu din basu gane taka maimain ko waye shi ba sosai. Amma har kasan zuciyar shi ya fara zargin wani a tare da boy din yanzu wanda kuma yake fatan kada abin ya kasance hakan gaskiyane nan gaba. Waya ya daga ya kira chuku tare da mai bayanin komai yace ya gane yarinyar sosai kuwa kuma zaiyi aikin nan da gobe in jesus name yafada. Ya tura mai kudin zirga zirgan da zaiyi wanan aikin yayi ta faman yi masa godiya yana jin dadi har cikin zuciyar shi da wanan kudin daya turo masa haka masu yawa don wanan dan karamin aikin daya sashi kan mace. Ya mike daga wurin da yake zaune din zuwa gado don tunda yayi sallah yake zaune yana azzakar har ya fada tunanen duniya kuma. Bai dade da kwanciya ba wayan shi ya fara ringing ya ya mika hannun shi ya dauki wayan dan tsuki yaja don ganin mai kiran nasa a lokacin don ba wani bace sai Nazira amaryan shi daya bari gida kullun tana masa korafin ya tafi ya barta a gida ita kadai. Dauka yayi da sallama saidai muryan da yajine sabanin nata din ya bashi mamaki har ya dan daga hannu yana kallon lokaci tare da mamakin me ya kawo uncle Nuhu gidan a wanan lokacin takwas saura na safe. Wani gaisuwa ya shiga yi kafin Uncle din ya katse shi da fadin kai ba gaisuwan ka nake so bani dalilin tafiya kabar min ya zaune a gidan ka ita kadai nake son ji ? Idan ma aiki kake takama da ka tafi yi meya hana ka dauki matarka ku tafi tare don ka rainawa mutane wayau ne kome da bakatafi da ita ba can ku zauna tare. Shiru yayi yana sauraren mahaifin matar nasa kawu a gare shi har lokacin da yaji ya tsaya da magana yace kawu ayi hakkuri tun farko abinda na guda ke nan don kowa yasan yadda aikina yake. Dakatar dashi Alh Nuhu yayi a fusace yana fadin kai idan ka rainawa iyayyen ka wayo niba zaka raina min don na gane komai da kakeyi a yanzu da sanin su kake iskancin nan. Dan murmushi yayi kafin ya ja nunfashi yana fadin ayi hakkuri na kusa kamala abinda ya kawo ni nan zan dawo a cikin satin nan insha Allah. Ka saurareni Alh Nuhu yace na baka yau zuwa gobe duk abinda kayi ka dawo gida idan ba haka ba zamu saka wando kafa daya dakai a garin nan don naga nema kake ka mayar dani mutumin bamza a garin nan yanzu. Idan na gama zan dawo ya fada Abubakar din yana kashe wayan bai jira cewan kawun nasa ba ko yaji abinda zai kara fada gaba ya kashe wayan kai tsaye gaba daya ta dauke a cikin kunan rai yayi cilla ta gefen shi yana huci. Nagane mutumin nan sai nayi da gaske idan ba haka ba raina min wayau zaiyi a garin nan ya fada a cikin hasala ran shi yana baci sosai da halin son kai da Alh Nuhu ya nuna mai yanzu din. Daga nan ya wuce kai tsaye ya shiga bath room wanka yake yana faman jan tsuki shi kadai a ban dakin har ya fito ya fara shiryawa. Yau tun tashina nake jin raina na baci gaba na kuma yana dan faduwa lokaci lokaci wanda ban saba da irin wanan yanayin ba a baya sai ranan nake jin hakan. Ko umma ta fahinci halin da nake ciki na rashin walwala a tare dani don ta tambayeni lafiya nake kuwa nace lafiya ta kalau kawai dai yau bana jin dadin rayuwanane kawai haka na tashi. Koma meye Allah zai kare min ke don nima a yan kwanakin nan ina yawan yin mafalkin da baida kyau a gareni addu,a nakeyi da neman tsari a kan hakan . Dan murmushin yake nayi ina fadin balle ba wanda ya sani don ba wuri daya nake zama ba a garin nan ko ina ina shiga ina yawatawa gobe kuma na canza unguwa. Amma sai naki fada mata komai wani tunane nayi akan kudin nan ranan dai na bata kuma nasha fada sosai kan yadda na bari har muka kara haduwa dashi duk da alherin da yaiwa umma amma tayi min fadan hakan ni dai ban damu ba tunda na rabu da kudin a jikina. Kwana biyu ke nan bayan bata kudin nake jin yawan faduwan gaba a tare dani yau da zan fita amma don karfin hali haka na daure na shirya na bar gidan. Nayi duk wani shirin da zanyi don fita na zo gaban umma na rusunna ina fadin zan tafi a cikin harshen yarbawa tayi min adduan tsari na kalli amar dake kallona na nace me zan sawo ma yau idan zan dawo yace min nama dariya nayi nasa kai na fita ina tunane don mun kwana biyu gaskiya rabon mu da nama a gidan. Saidai muga mutane nacin nama muna kallo don umma ta saba muna da hakan zamu iya zama da dadi da wuya duk wanda ya samu a rayuwa zamu iya kasancewa a hakan. Kuma hakan yana da kyau sosai don uwa ta nunawa yaro jin dadi da halin wadata a kullun abune mai muni da iyayyen yanzu basu gane ba ka koyawa dan ka ba kullun ne ake zama a vikin daula ba koda kuwa akwai wadatan ga mutum ya daure ya koyawa dan shi zaman duniya a yanzu. Haka nabar gida ina tafiya kamar wace wani abu e damuna a lokacin har nazo bus stop na shiga motan Obalande duk da nasan yan wanan yakin yarbawane zallah a cikin sa sai yan yaruruka kalin dake zama a cikin su duk da hakan kuma ba jittuwa a tsakanin su amma haka na hau mota a ranan sai obalade din. Tunda na sauka nake bin ko ina da kallo tunda ba unguwar na sani sosai ba aharawa daya na fara yankewa shine in bi layin mabarata don yanayin da nake ciki ranan ba zan iya tallaba. Har na zauna na hango wani tsoho mai sayar da maganin gargajiya zaune na nufi wirin shi na dan dade tsaye ina nazarin shi kafin in ce ya ban ko kadan sari. Kallona yayi yana mamaki yace zaki iya nace eh zan koma wani side in zauna ba a wurin da yake zan tsaya ba a cikin gurbatacen hausa na nake magana haka dashi. Na dubu biyu na sara don ban yarda na sara da yawa ba tunda gwadawa zanyi ina murna har na daga yake fadin in tsaya ya bani wani siri da zanci kasuwa dashi na tsaya. Yace in miko hannu na mika mai yake fadin don su yarda da ke kinga wanan layin na tafin hannun ki guda uku nace eh . Yace don a gaskanta maganin ki sai kice wa mace ta baki hannun ta ki duba idan namiji ke bi mata a wurin haihuwa zakiga layin nan biyu sun hade dayan ya ware nakasan ke nan. Idan kuma mace ce wace ke bi maki a wurin haihuwa zaki ga daga sama basu hade ba sun dan rabu wanan kawai idan kinyi zasu gaskanta magabnin ki su dinga saya zaki dawo idan kin kokarta na fada maki. Har kasa nakai ina masa godiya na karba na fara tafiya ina dan waigen tsohon a cikin tsoro don taba min hannun da yayi tunda umma tace mu daina yarda ana taba mu . Idan an tabamu mubi mutum mu rama ko waye a haka ake daukewa mutum kurwan shi a cinyeshi ko a bashi wallaha gashi yau rigima yasa na amfakawa tsoho waini tallan mahani. Sai da nakai titin babba inda ake hada go,slow na tsaya na fara bin motoci ina fadin by local medecine for ur body medecine de here. Wata mace ce naga ta tsaya a tana kallona na je dan kusa da ita ina fadin buy medecine madam. Meka give u d one when ur ogo no go look anoda woman again tace dani (waire,) wai ni mahaukaciya tana fadawa na gefen ta wani magana suna dariya. Nace madam no be lie i talk woo na true true i de talk make show u something ban tsaye ba na figi hannun ta daga cikin yaga motan ina bude tafin hannun ta nace. Na woman de follow u for d birth abi na dago ina kallon ta ta dan fisge hannun ta tana cewa woman for where ? Nace emm after ur mama born u d one who de follow you its a girl abi ? Kallon yar uwar nata tayi tana fadin see dis small girl how d u know all this nace eh na my work naw even you can ask me sometin now apart from dis. Kallon juna sukayi kafin dayan dake gefen ta tace oya look here who de follow me na rike hannun nata da sauri kafin ince na boy naw. He naw tall dan u na kwatanta shekarun tane na fadin hakan da wasa ashe gaske ne haka dinnne kuwa. A wai