← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 268 OF 337

Sashe 268

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Affuwan yan uwa kwana biyu bakujini ba wallahi ba laifina bane matsala wutan neper ne da muka samu har tsawon kwana hudu dan Allah ai min affuwan yan uwa. Ina zaune sakon ya Abubakar ya shigo min na duba naga lambane da sunan maishi na dade ina maimaita sunan a raina kafin na aje wayan don nasan a lokacin dare can a kasan da mai layin wayan yake yanzu. Don akwai wanda zan iya samun shi a nan idan yana Nigeria saidai ban gwada kiran wanan layin ba tunda yace baya kasan yanzu yana kasan waje. Washegari kan kona ce ina da karfin gwiwa a tare dani nasan karya na fada don bana jin wani lakka a tare dani har yakai umma ta fahinci hakan a gareni . Take tambayana abinda ya sameni nace nima haka na tashi ina jin raina yana baci sosai a ranan gashi kuma dama na boye mata zancen wayoyin kowa da nayi jiyan don fada mata zai iya saka umma tace zata ban wani shawara dagane da hakan. Kallona umma tayi ta sake fadin anya kuwa ba abinda ke damun ki ga haka don yanayin ki gaba daya ya nuna kina cikin damuwa gaskiya. In kuma wacan zancen ne kika saka a ranki haka ai gara ki fitar da rai zaifi don su yanzu suke fuskantar nasu hukuncin abinda suka shuka din. Ba zancen su bane a raina kawai dai hakan na kwanta na tashi ina zama lokaci guda nake fadin hakan kafin na tambayi umma Ammar ko ya fitane lokacin ? Ta dan dago tana fadin koya fita bai wuce ya shiga part din Abdul bane don yau ba school ake zuwa ba balle ya fita haka da safen nan. Bata rufe baki ba ya turo kofan ya shigo falon mu nan ya fara min ina kwana na amsa a kasalance yake fadin jiya ban fito ba mun yi hira da dare lafiya nake kuwa ? Nace kalau jin suna yawan tambayana hakan yasa nayi kokarin nakai kwance a daidai lokacin da wayana ya dauki kara kira na shigo min a lokacin ke nan. Hannu na mika daga kwancen ina gyara kwanciya na dauki wayan na kara a kunne na ina fadin morning brother jin haka yasa Ammar ya matso kusa dani. Bayan mun gaisa ya tambayeni gida nace suna lafiya lokacin Ammar yace na bashi waya zaiyi magana dashi shi kuma din yana tambayana yadda mukayi da mutumin da alama zancen tsare daddy din yana damun rayuwan shi sosai a lokacin. Zankirshi ai na bashi amsa tare da fadin na bari time yayi daidaine da yadda nake son na kirashi kada muyi mai girshi. Ok kawai ya amsa min dashi nan ammar ya cabe wayan ya mike zuwa waje suna magana da bansan kona maye ba a lokacin. Saida suka gama magana da Ammar din kafin ya dawo min da wayan hannuna na karba naci gaba da magana yake fadin in ba Ammar kudi kafin yazo yayi registration din football team yake son shiga. Hararan inda Ammar yake nayi ina fadin shi da bai faye lafiya ba zaije shiga wasan kwallon kafa a yanzu. Nan dai ya din ya kara min magana na amsa da zan bashi nayi dan mamakin abinda ya hana ya turo maahi din ya amma kuma sai dan tunane yazo min lokaci guda na kodai ya dan shiga matsalane rashin daddy din nan na dan lokaci sai kuma shi ya Abubakar din naji tausayin sa sosai kan hakan. Bayan gama wayan mu na dannawa wanan layin kira har sai dayayi ta ringing ya kusa katsewa aka daga a cikin wani muryan maza mai amon wani sauti dake kada zuciyan ya mace lokaci guda. Hellow2 yake fadi daga ban garena na amsa nima da kya kafin nace i am Sahibat from lagos calling now. I know miss sahiba where d you get my number nace daga wani na sama kafin na juye zancen da fadin ya kake ya family din ka. Well, anyway duk muna lafiya nagode ya fada a gurguje kafin yake fadin ya mahaifiyar mu da dan uwana nan ma na bashi amsa da suna lafiya. Sai dan shiru ya biyo baya kafin yace dani anything else miss sahiba na nisa kadan tare da fadin nothing much dama akan case din su yan uwan mahaifina dakasa aka tsare a Abuja yasa na kiraka yanzu. I know saboda shi kika kirani din don idan bashi ba ba zaki kirani don mu gaisa ba ai ina da labarin cewa wanan dan iskan yaron yana neman layina ninace a bashi ai. Amma ban dauka take zaibi yai amfani da layin ba na dauka shida kanshine zai kirani kan barawon mahaifin shi da baida imani idanuna na dan runtse don jin zagin da yakewa iyayyena din da a yanzu su nake gani a matsayin iyayyena a duniya kaf. Enough mr mukhatar wanan matsalan mu ya shafa family din daddy mu bakai ba banga dalilin da yanzu zaka saka kanka a cikin family issue din mu ba. Dan murmushi ya sake kafin yace good ashe kuna da family yanzu har kin sanda dasu suma sun san dake da kike ikirari a kansu. Amma suka wullakantaku suka barku a cikin duniya kuna yawo ba wanda ya tausaya maku sai yanzun ne da sukaga bayi suke son ku har kike ganin su a yan uwanku yanzu ? Good idan wanan ne ai basu kade bane da irin laifin nan naga wa yanda ma sukeda karfi fiye dasu basuyi yunkurin neman mu ba sai wanan lokacin. And beside mu musulmaine musan cewa bawa bai wuce kaddaran ubangijin shi dan haka mun yarda da wanan a yanzu munyi imani da hakan. A takaice dai na gane kamar neman jin dadin yan uwa a yanzu ya rufe maki idanu har kina ganin kowa mai laifine a wajen ki don kawai , , , , Look mr ban kiraka don dogon zance ba a yanzu kawai kayi abinda ya dace kasa a sako masu mutanen su final mu mun barsu ga Allah understand na kashe wayan. Duk da umma bata jin turanci amma ta fahinci ba maganan dadin rai mukeyi da sunan wanda taji nakira din wanda tun lokacin ta dago kai ta mayar da hankali garemu. Meya hadaki dashi koba mukhatar din maiduguri bane kuke waya dashi yanzu na gyada kai alaman eh shidin daine . Maimaita tambayan ta gareni tayi ta sake jefo min tambayan da tayi min da farko meya hadaki dashi yanzu kuma ? Akan case din su daddy daine ya Abubakar ya matsa sai nayi magana dashi don a san abinyi don hankalinsu a tashe yake nan dai na fada mata yadda mukayi dashi din a cikin yare yadda zata gane. Wanda tun kan na kai karshe nake ganin wani irin kallo a fuskan umma din da take jefo min na takaici da jin zafin abinda nake fada mata din. Yanzun Sahiba kinga kin kyauta ke nan yadda kike kokarin watsa mai kasa a ido haka kan kokarin da yakeyi don mu ? No umma idan ba hakan nayi maiba a yanzu ba zai dauki maganan da muhinmanci ba sosai don kinga ya Abubakar a yadda ya daukemu bai dace muki nuna mashi goyon bayan hakan ba. Dan shiru tayi kamar tana nazarin zancen nawa kafin tace nasan da hakan amma shima bai kamata ace kin masa magana haka tsatsaye ba a yanzu. Shiru nayi don an riga an gama ko yanzu saura naga ranshi zai baci ya fitar da hannun shi a case din ko kuwa don yadda naji ya kira daddy da macuci yana da wuya idan bai saka anyi masu wullakanci ba fiye da yadda bamu zata ba ma. Shiru falon yayi kowa da abinda zuciyar shi ke raya masa lokacin kafin wayana ya dauki kara lokaci guda banyi saurin dubawa ba sai kusan ya katse na dauka ya Abubakar din ne ya kara kira wanan karon muryan shi da rauni yake magana wanan karon. Sahiba wanan guy din ya kirani kece kika bashi layina nace bani bace dama ya fada min yasan kana neman layinshi shi yace a baka. A zaton shi kaine ka turoni nayi masa magana sai naji ya Abubakar din ya dan sake murmushi kafin yace dani yace zai saka a daure ga baki dayan mu idan bamu fitar da baki cikin wanan zancen ba a yanzu. Ko muka kara matsa maku kuka kirashi zaici muna mutunci fiye da zaton mu kawai dai shike nan yanzu ai ku barshi yayi abinda zaiyi a yanzu din. Kada ki kara kiranshi a kan zancen ki barshi tunda har yake zargin mune muka turoki wai kici masa mutunci muna ganin idan munyi hakan zamuyi nasara kanshi don baida karfi kome a cikin zancen ko ? To mu sani ba wani barazana da yanzu zai dakatar dashi kan matakin da yake shirin dauka ku kyaleshi shida bakin shi zai furta ya janye akan zancen. Ok kawai ya iya ce min lokacin naji ya kashe wayan don wani murya dayazo wurin shi suna magana tunda na kwanta na juya ban kara magana da kowa ba don raina daya baci da maganganun dayayi din gun su yaya. Kai duniya bata da tabbas abinda baffah hamza ya fada ke nan kafin ya kai zaune yaci gaba da fadin dama na fada maku ai da wuya yadda mukayi da yarinyar nan ta canza magana kuma yanzu. Eh yanzun dai ai gara da mukaji daga bakin ta kaga mun fitar da zargin komai nasu a zuciyan mu, dama ai nasan Sahiba ba zata fada mai komai ba. Ya dai yine kawai yaji idan mun tursasatane kan haka kawai kowa ya kyaleshi yanzu a zuba mai ido. Ayi hakan mu dai dan saurara mu gani nan da dan wani lokaci kafin mu kara tuntubanshi da kan mu wanan karon. Da wanan shawaran har suka isa Abuja da yanzu zuwa abuja ya kamasu a cikin mota don dole ya Abubakar da bai saba da wanan harkan tafiya da mota ba ya kowa don dole. Saidai duk yadda sukayi don a bari suga su daddy din sun kasa ganin su don tausararan matakan da aka dauka a kansu. Wanan yasa dole suka juyo zuwa gida duk rayukan su a
Chapter 268 · 0% Book details