← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 337

Sashe 180

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe goma na dare muka fito don nema inda zamu kwana ga yunwa dake cin mu lokacin don ma munyi dabaran odan abinci aka kawo muna har inda muke banci abincin ba don inada matsala a rayuwana. Bana cin kifi ko wani iri kuma bana zama a indama ake cinsa sai gashi anyi rashin sa, a sun kawo masu ferfesun kifi a cikin hadin haka yasa na dan fita daga waje don warin shi da aka bude yake son sani amai. A inda na zauna bayan ginan nake jin ana kuskus waya akeyi da wani kan cewa ya tabbatar ya shigo cikin dare yayi yadda aka umurce shi dayi. Fotowan da nayine ya ban dama samun lokacin don jin abinda suke shirin yi anyi yan wasu abubuwa a wurin. Aikin ne damuka dan dakata ya kaimu dare gashi shawarma da dan ruwan lemu naci shine a cikina har daren. Bello ne ya nema muna wurin kwana don gaskiya yana da kirki sosai ga kwazon aiki don ya iya computer sosai irin talent din nan ne shi. Wanka nayi tare da alwala nayi sallah na dade zaune ina addua kafin nashafa na mika hannu na dauko wayana dana makala a canji na kira umma nayi masu bayanin ba zamu samu daman dawowa ba a ranan. Addua tayi na Allah ya tsare ya kare na amsa da amin daga man na shiga duban sakon da aka turo min. Sakon farko daga oga jimo ne yana min fatan nasara da godiya kan aikin da mukeyi ya samu labarin yadda aikin ke gudana. Sai sako na biyu daga Faiza idan da sabo na saba da ganin sakon nita tana min fatan sake ganina a rayuwa a karshe tace kada nayi mamaki ganin ta lagos wurina wata rana. Sai na uku sakone daga oga Sha,aban shima din fatan alheri ya turo min da godiya sai tambayan umma . Dan murmushi na sake a fuskana don jin dadin wanan sakon kamarni mutum irin sha,aban zai tsaya ya turowa godiya irin haka ? Nagaji daga inda nake ni kadai ina faman tunane don haka na mike zuwa bandaki na fito nayi adduan kwanciya nakai saman gadon. Wasa wasa aikin da muke ganin na kwana biyu muka shigo yi sai gaya yakaimu har karshen mako a nan kano din sanam muka koma kaduna. Yayi sallama ya shiga fallon ya samu wuri ya zauna yana sauren wayan da daddy din keyi akan rashin lafiyane har yana fadin a kaishi waje idan nan din ba su gane komai ba. Daddy din ya gama waya ya juyo yana fadin kai duniyan nan wai Alh Bubane wanan aminin Alh Nuhu ya samu matsalan tashin lafiya da rana tsaka hannu ya rike mai. Allah ya sauka ya bada lafiya ya fada kafin ya zamo yana gaida daddy din sunyi kafin yace nazone kan zancen Summay baby don a tuntubi gidan mijin aji in sun gama hada inda zasu sakata a kai kayanta can don kayan sun iso ko a yanzu. Nan hjy karima ta fito daga uwar dakin Alh din datake ciki tana gyara sai taji abinda modibbo din kr fadi kafin daddy yace dashi kamar wasu irin kaya fa yana tambayan dan nasa. Ya dan gyara yace kayan dakine nayo mata odan su kuma sun iso dama nayi hakane don kada kayan su jima suzo daidai bukin ya kusa. Shine banda masaniyar hakan Abubakar bayan wancan kudin da tace ka basu a baya har kayan daki kuma ka hada mata ? Zaune hjy karima takai don ta rigada ta gama magana akan wanda zata sayawa yarinyar har hakan ya hadasu fada da mijin nasu sai da ban baki aka shawo kanshi ya fara bada rabin kudin kayan. Wayan shi yake duba don haka hankalin shi baikai ga kowa ba a cikin su balle yaga irin kallon junan da sukayiwa juna na zargin kin gani ko ko kuma don me zai mata haka a bangaren hjy karima din. Wayan shi ya mikawa hjy karima dake zaune a gefen mijin ta yana fafdin ga kayan sunce kalla biyune milk da purple suka shigo dasu shine na zaba mata purple din kamar zaifi. Wayan ta tsurawa ido tana kallon kayan da suka saka zuciyar ta kusan bugawa a lokacin yau yar tane da wanan kaya haka masu uban tsada. Ta mikawa Alh wayan shima ya dade yana kallon kayan ya mikowa dan wayan shi ta fara din modibbo wanan irin dawainiya haka mai yawa ? Ni zan koma dama abinda ya kawo ni ke nan ga takardun kayan sai idan an shirya aje da wanan idan za a kwaso yayi masu sai anjima ya fita ya barsu da mamakin shi. Mommy aka kira koda tazo dan nata ya fita falon lokacin sai mijin da hjy ta sama zaune zugun zugun ta zauna a cikin tsarguwa tana fadin gani Alh. Yace modibbo ne yazo da wani zance yanzu koya fada maki ta dago tana fadin zancen me Alh don ni bamuyi maganan komai dashi ba ya fita. Takardun photunan gadon ya mika mata ta dago ta karba ta fara dubawa kafin ta dago kai ta kallo shi. Modibbone ya sayawa kanwarshi kayan daki murmushin dadi mommy ta sake a daidai lokacin da ta dago don taga yanayin da fuskan mommy zai nuna a lokacin. Mommy ke fadin amma ya kyauta haka akeso babba ya zama babba a wuri ya fara daukan girman shi ke nan a yanzu. Nan suka dan taba zance irin haka kafin ta mike zuwa part din ta ta barsu a falon hjy karima tabita da kallo. Yau na tashi ina son sawo abin bukatan mune na gida don haka na shirya tsab cikin doguwar riga mai tsaga har gwiwa sosai sai dan gyalen dana yafa a kaina dayasha gyara. Nida Amar muka fita nake jan mu a motana dayasha wanki yana walkiya muka dauki hanyar cikin gari da zan iya cewa wanan ne karo na farko dana taba shiga gari da sunan wani bukatana. Tafe muke mun sake kida dake tashi na yarbawa aikin Amarne wanan yawo kawai mukeyi don haka kawai muke dan shakatawa kuma na fitone don Amar din lokacin. A daidai traffic muka tsaya magana nake a wayana hankalina yana saman traffic din dukda wayan dake kunnena a lokacin. Hannu aka bamu na ja motan da sauri kamar ance in dago kaina in dan kalli gefe Almustaphana ya kura min idanu na kawar da sauri ina kallon hanyana. Shi dine tabbas na gani don jikinane ya ban ana kallona na dan kallo wurin na ganshi a cikin wata mota fara. Mamakine ya kama shi don zuciyar shi bai gaskanta mai abinda idon shi ya gane masa ba harko in kamane wanan kaman yayi yawa sosai wallahi. Har motan ta wuce yana binta da kallon mamaki ta cikon glass yana fadin anya wanan ba sahiba bace kuwa ? Inhar itane tun yaushe take garin nan ke nan har yakai gida cike da wanan tunanen a zuciyar shi dabara ya fado mai yaron shi ya kira ya bincika mashi har in itace ko tana lagos din tunda yasan gidan yasan kuma motana. Wani shago muka shiga Amar ne zai zabi kaya a cikin sa shida kansa ya zabo abinda yake so muka juyo zuwa gida lokacin shidda na marance tayi ko. A wajen gidan mu muka samu umma zaune tare da muniya suna hira a nan na tsaya sai Amar ne wanda ya shiga da kaya cikin gida lokaci. Umma ke fada min yayan mu yazo bai samemu ba da sauri na juyo ina tambayan wani yayan namu a ciki tace Modibbo mana. Na sauke ajiyan zuciya don a zatona shima mustapha din yasan gidan nan ke nan don ko sun sani ba zan je gidan kowa ba a cikin su na raya a raina. Saida akai kiran sallah muka bar wurin zuwa ciki kowa ya shiga dakin shi don gabatar da sallah a lokacin. Ban fito tunda na idar din ina daki ina aiki har dare yayi sosai kafin na fara jin haushin karnuka daga wajen mu can nisa kadan damu don ina jin haushin da dan nisa da mu. A can kuma na dinga jin dan hayani kafin a fara kwankwasa muna kofan gida na taso da sauri na zura hijjab dina a jikona. Falo muka hade da umma tace waye a cikin daren nan haka karfe ukun dare yake kwakwasa kofa a yanzu ? Ba lafiya dai duk yadda akayi ta kara fada kofan na nufa da sauri umma ta tareni tana fadin waye daga ciki. Bude mama ya fada da hankali nine Abdulhamid jin hakan yasa na bude kofan da sauri ina budewa suka fado cikin gidan mu shida iyalin shi baki daya lokaci guda. Umma ta mayeastar da kofan da karfi ta rufe lokaci guda take tambayan shi meke faruwa ne wai ? Yace ki saurara kiji tun dazun ake wanan ihun hakan daga bayan layin mu nace ina sauran yace baisan halin da suke ciki ba a gidajen su. Mikewa nayi na nufi hanyar fita daga gidan da sauri suka tareni nace dole na dubasu ina fadin haka na fito shima ya biyoni a baya yana fadin su rufe gidan. Wurin yemisi na nufa ita da take mace bugu daya ta kara zabura nace nine sahiba saita bude tayi kuka har ta godewa Allah. Fitowa tayi ta rufe gidan jin cewa da nayi nice sahiba yasa su Adnan da felix dake tsaye a bayan mu bude kofan suma da sauri suka fito daga gidajen su nan sauran makwabta suka dinga fitowa daya bayan daya jin karan bude kofunan sauran gidaje da sukeji a lokacin. An hadu wuri daya ana shawaran zuwa duba abin ko a kira yan sanda suzo nace me zai hana muje mu duba kada ku manta bamuji motsin masu gadi ba kuma ya kamata a duba halin da suke ciki su ma. Kowa ya fara kallon dan uwa an rasa wanda zaiyi kundun balan zuwa ga karan abin kamar dabba yana ci gaba da kugi a cikin wahala sosai lokacin. Kallon Abdul nayi ina fadin yakai yemisi gidan mu wurin su umma ya dawo da sauri suka wuce don duk a tsorace take lokacin. Tafiya na fara yi ba tare da sun
Chapter 180 · 0% Book details