← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 337

Sashe 29

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Sai satan kallon juna sukeyi a dakin an rasa wanda zaiwa wani magana a cikin su balle har su kai ga gaisuwa wa junan su.
Waini kan moddibo ka gaisa da dan uwan ka kuwa tun da suka shigo dakin nan hjy ta fada tana kallon yan samarin dake zaune a gaban su kowa na busan iska a lokacin don isa da takama da suke ji dashi.
Don kada ya bayar da mahaifiyan nasa a gaban yan uwata ya nuna masu shi dane maijin magana a take yake fadin ban ma kula dashi aka shigo ba ai.
Yah kana lafiya ya fada cikin dakewa shima ya amsa masa da lafiya ya mai jiki thank god ya samu sauki ai ya fada yana mayar da hankalin shi gun wayan shi dake hannun shi.
Ai wanan din ne babban bazan daya kasa gaida mutane a wurin ya shigo kamar wani dodo dashi yana tsoron mutane.
Halin the boy ne baku sani ba kuma da kyaluwa shi haka Allah yayi shi shine kuma yake son biyewa halin nasa ai hjy Addah ta fada.
Alh dake kwance yana jin su ne yace wai ba zaku daina kiran shi da boy din nan ya nuna diyan hjy Altine yana fadin jifa inda kanen sa suka kai yanzu da girma za,a wani saura kiran shi da boy.
Murmushi wanda aka kira d boy din yayi ya mike daga inda yake zaune yana fadin uncle ashe ka tashi ke nan na zata barci kakeyi ai.
Ya mike daga zaune da yake yana saye a cikin kananan kayan da sukai matukar mashi kyau a jikin shi zuwa bakin gadon da daddy yake kwance din a sama.
Kamar yadda yakanyi da danshi modibbo hakan yakanyi da dan kanwar tashi ba ita kadai ba har hjy Atine dake da yan mata guda biyu suma suna samun kulawan kawun nasu sosai a cikin so da kaunan junan su.
Yaushe ka dawo ke nan daddy ya tambaya yace yau da safen nan daddy nazo gobe kuma zan koma don yau naso in juya sai na samu bakaji dadi ba kuma.
Dan murmushi ya sake yana fadin suka kwantar dani a nan ba badan naso ba don kawai dai banda yadda zanyi ne na yarda na kwanta din.
Amma dai yaya ai kwanciya yana da amfani a gareka tunda kaji doctor yace sai ka dan kwanta din kwanciyan a yanzu shi yafi ga lafiyan ka.
Kofan aka turo hjy karimace da wanan kawar nata suka shigo duk suka kalketa suka kawar da kansu gare ta don yanayin wayewan ta ya nuna yar bariki ce ita bata da isashen kamun kai sosai.
Alh ashe jiki ya ki karima ta kira tana fada min tana magana tana wani kwarkwasa a gaban shi abinda ya kara basu takaici ke nan a dakin.
Allah ya gani abinda tun farko suka guda a auren shi da karima ke nan abinka da namiji ga abinda ya gani yana so yace yaji ya gani sai yayi.
Gashi har yanzu rabo ya ratsa a tsakanin su yan maya uku resas suka haifa bai kuma sa ta natsu ta daina wasu halaiyan da basu so a gareta ba.
Da shima kanshi Alh da alama yaji nauyin hakan sai ya basar yana fadin ya gode ya juya yaci gaba da zancen shi da boy din yana tambayan shi yanzu kana wani kasane boy ?
Ya dan yi murmushi yana fadin daddy ba inda bana zuwa saidai yanzu din nafi bada karfi a kasan Ukraine don shigo da alkama a nan kasashen muna Africa da muke karancin su sosai.
Masha Allah ashe kana wanan harkallan hakan yana da kyau sosai ina dai fadama duk lokavcin da kake bukatan wani taimako a cikin sana,an ka ka nemeni zan taimaka maka insha Allahu.
A daidai lokacin hjy karima ta wani tabe baki tana fadin muje ko kubura sai kawar ta juya tana fadin Alh ya ya kara sauki ta juya ba tarewa kowa magana ba a dakin ta fita.
Boy da moddibo kawunan su yana kasa kowa da iri takaicin da yaji a hakan saidai kawai a shanye ba dan anso ba.
Babu wuta a cikin hasken farin wata muke zaune sai dai ina can dan nisa dasu kadan ina jin hiran su da nake tsunta guda guda.
Ko barci yarki keyi a zaune koko gajiyan aikin da tayine yasa ta shiru matar da umma ke kira da Ladi ta fada.
Kawai dai nasan bakuntane ba wani abu ba tana tunanen wancan unguwar da muka barone don bata so tasowan mu ba can.
Ikon Allah yarinya nan din ai zaifi maku saukin komai dama ai don hjy nana ne kuka koma can Allah kuma baiyi zaman naku mai tsayi bane a can din da ita aka rabu.
Wacece hjy nana na tambayi kaina don ban taba jin umma na zancen ta ba a gabana har yau wama umma ta taba zance ni a gabana na ba kaina amsa da hakan.
Mikewa nayu tsam na hankade labulen zuwa cikin dakin namu din na kwanta ga duhu ga kukan wasu kwari a bayanbdakin masu shegen kara a kunnen mutum da zasu hana mutun yin barci da dadi.
Allah ya gani ganin farko da nayi wa wanan unguwar na tsaneshi ga baki daya a rayuwana a haka nayi barci sai dai banfi awa biyu ba dole na falka don yunwa ga kuma karan kukan wanan halittan dake ban tsoro.
Duk da duhun dakin amma hakan bai hanajin muryan umma ba tana fadin nasan dole ki falka dama don babu komai a cikin ki tun karywan safe da kikayi kafin kije school.
Gaskiya ba zan iya cin wanan abincin ba dana gani kamar ma bayin yau bane guntayen tuwon masara da miyar kubewa fari tas dashi an zuba miyan a ciki.
Bana jin yunwa umma kukan wanan abine ya dameni na bata amsa a cikin duhun nima ina gyara kwanci saman tabarman da nake kwance.
Shiru naji umma tayi bata kara tanka min ba har wani barcin ya kara daukana bayan na gaji da tunane ni kadai a cikin dare.
Washe garima haka na tashi sukuku dani bayan na gama sharan fadin kewayen mu da aka mayar kamar juji a gidan wanda a yanzu duk na gyara shi tas da wanab safiyan.
Na debi ruwa na watsa a jikina na dawo na zauna na shafa mai naji umma na fadin ki karbi ga dari biyu ki fita ku samo abinda zaku karya dashi kafin mu san abinda zamuyi nan gaba.
Karban kudin nayi na fita na fara dan zagayawa ina kara kallon yanayin wurin da hausawane zube ashe kamar mutum yana a cikin arewa ne zaune.
Saidai kowa kuma a wurin da irin sana,an da yafi kwaraiwa akai ga masu tallan abubuwan da ban san suba nan ina ta kallo na nufi wata mace dake soyar masa na mika kudin ta bani masan tana ta zuba duk sai naji kazantan hakan nayi dana sani banje gurin ta ba saye don akwai har maza dake wanan sana,an a wurin.
Haka na dawo gidan da jan kafa na zauna tare da dangware kwanon abincin a gaban Amar na koma na rakube gefen kofan dakin nayi shiru ina tunane.
Ba zakici abincin bane ke umma ke fadi tana bude kwanin dake rufe ta girgiza kai ta jawo kwanon zuwa gaban Amar yana gani yake tambaya na waitin bi dis ?
I no sebi eat dis kind of food wooo u ko ta kalleni tana tambaya nace i no go eat now i don bele ful na fada ina kawar da kaina gefe daya.
Tace no be u buy yam for breakfast ta dauki daya tana kaiwa bakin ta kagin tace eatam naw go enjo am is test good now.
I no sabi eat dis kind of food before i will drink gari da gradnut later na fada ina mikewa tsaye don barin dakin na fito na tsaya ina kalle kalle a wajen gidan.
Sai ga wasu tafe da ganin su mata da mijine zasu fita na bisu da kallo matar tana saye da hijab a jikin ta shigan ta ya banbanta sosai dana wanda na saba gani.
Har suka fice a gidan na sauke ajiyan zuciya ina mamakin su a raina kafin naji muryan ladi a kusa dani tana fadin yanzu nake zancen ku ai a zuciyana ko kunyi dabaran neman abin karyawa nace ?
Dan juyowa nayi ina kallon ta kafin na dan kago murmushi a fuskana ina fadin A karo ma tace adukwbe yar nan haka uwar ku tayi sakacin da yaren wasu ya shige maku harshe haka ?
Tana inane ita uwar taku na nuna mata dakin mu da iska ke dan kada labule a hankali ta juya ta nufi can din da abu a hannun ta zuwa aurin umma din.
Ta dan dade a cikin dakin tare da umma wanda bansan ko akan me suke tataunawa ba har tayi wanan dadewan haka a ciki.
Ni kuma ban shiga ba tunda bansam zancen da sukeyi kada in shiga injiwa kaina haka din ne kuwa don ta shiga tawa umma zancen sana, a ne sai aka kira wayan ta ta tashi.
Ganin ta fita din daga dakin yasa na koma dakin na samu wuri na dan kwanta sai barci a can cikin barcin nake jin muryan ladi na fadin.
Ke yanzu ai ko baki fita kin nemo kudiba yanzu kina da jari don wanan yar zata iya nema maki duk wani abinda zaku bukata idan tana da kwazo da basira.
Ga wanan unguwar namu cike yake da samari majiya karfi suna harbin iska ga banza balle sun kyala ido sunga wanan yar taki ai kakanki ta yanke saka ke nan ke.
Haba ladi ni kaina bayi shanshamci ba tun barin gida danayi kin sani balle na saka yar mutane ga hanyar halaka.
Kin dai fadi gaskiya kan da kikace gani da ita a gaba tunda ba issashen lafiyane dani a yanzu .
Eh ko can din inda muka baro itace tsaye damu ga komai tana samo muna dan abincin da zamuci a cikin wuni da dan kwabon da zamu sarafa rayuwan mu a kullun.
Amma sam ban yarda ta aikata abinda kimarta da mutucin ta zai zube a idon duniya ni banyi ba ita kuma bazab sakata ba son bamu da gadon yin hakan.
Cikin dadin baki irin na Ladi din tace yo ai ba gado bane abun indai ka riga ka shigo bariki ai shike nan ka zama dan gida ga wanan harkan.
Ladi ina da abinda yarinyar nan zata dan rika juyawa yana zama kudi a yanzu a hannu na muna samun rufin asirin mu a cikin sa insha Allahu ba sai mun zubar da kiman mu ba.
Kin sani kuma kinmafi kowa sani yaran nan ba shegu na haufesu ba suna da ubansu da yan uwan ubansu nadai gudu da sune don sun rasa mahaufin su ana son a juya a kansu yanzu kuma.
Yo ai shike nan dama ni abinda nake jiye maki ke nan a yanzu kuzo ku zauna kuna zuba ido sai anci an raga a baku shine banso daku .
Ko a can ma idan muka fito basu san mu bamu san suba ban yarda mun zubar da kimar mu a can ba balle nan da yake kamar kasan hausawa a wanan wurin.
Har ladi tabar dakin ban gama fahintar inda zancen su ya dosa ba sai daga baya na fara gane kan zancen su ina hada kalmomin ina fahintar zancen su dana ji din sunayi.
A raina nace ke nan dai ya tabbata umma ta gudu daga gida damune don kada a cuta muna ke cikin wanan halin na wahala data kwanmace ma ganun mu hakan.
Su waye suke neman rayuwan mu bayan sun ga na mahaifin mu har mu suke son su karasa ake nufi.
Idan har hakane kuwa zan kara taimakawa umma wurin ganin mun kula da rayuwan mu kamar yadda umma ke tunanen yi akan mu ko yaushe.
Chapter 29 · 0% Book details