Sashe 146
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsatsaye muke duk kan mu a falon nasa daya ban mamakin sabon gyaran da naga anwa falo din a cikin kwana biyu haka har center kafet din nan daya dauke min hankali a ranan babu shi yau dana shigo. Dukkan mu farin tufafine a jikin don wanan sha, anin na dinka farin less da akai min dinkin buje da riga kuma dinkin ya karbeni don zamanin buje darigane abin yayi sosai sai kuma dogon riga wanda ni nafi saka dogon riga redmade ba wanda aka dinka ba. Takon ogane ya fito ya samemu inda muke tsaye muka shiga gaidashi ya nuna muna kujera mu zauna shima don ya kai zaune yana fuskantar mu. Jimoh ya fara kira ya dago kai yace kasan wanan abu yashafe ku dukkan ku tunda ya shafeni don haka zaka kula da komai dake gudana a wurin taron nan har abincin da za,aci ka kula da lafiyan shi you know you people are special from d other and kuma ba kowane yasan alakata daku haka ba a cikin family dina so take care. Oga Jimo din yace yes sir ya juyo kan Felix yace make sure u felix kana hankalce da duk wani motsi na kowa a wurin ka kula da abinci da abin sha wanda bakin mu zasu ci baida illa ko kadan yace yagane. Sai ke yemisi bakin mu mata su samu kulawa sosai ta hanyar directing din masu kula da bangare su yaza kina kulawa da wanan banda rawan kai ya kara mata hakan aka kwashe da dariya sabanin nida ban ko murmusa ba don nawa dariyan zai kona mata rai fiye dana saura. Kaima Adnan aikika kenan a bangaren maza a yau don Allah ku kula suka amsa da yes sir sai ya kallo inda nake yana fadin u Sahiba you will be with my family i mean my mother and my sister and others take care of their needs please kada ki yarda ki daga a inda muke komai taro zaki saje a cikin mu tare damu kamar yar family din kike kina saka ido a kan mu. Felix yace baby girl ke nan dai ya watsa mai harara kafin ya fara fada yana fadin ka kula ba aikin wasa nake so ba don nasan akwai makiya a wurin dole zai kasance da hatsari a wurin sosai don kaga wanan taron yafi na wanda mukayi a baya cika sosai . Ya amsa da zai kula kudi ya fito dashi ya mikawa kowa wrafer yana fadin a samu na badawa kunsan komai na bayerabe kudine shi don haka ya bamu namu rikon . Kowa ya mike nima haia ya juyo yana fadin Sahiba go inside now zaki samu mahaifiyana tare da yan uwanta suna shiri kufito tare. Gabana ne ya fadi lokaci daya idan na shiga wazance dasu nake amma a fili yes sir na amsa mai ban ko juyo gun yan uwa ba ma sakai na shige ciki. Cikin babban wurine sosai mai dakuna da yawa a ciki akwai kuma katon falo maidan girma daga ciki din na samu wuri na zauna bancewa kowa komai ba ina kallon zirga zirgan su da kowa keyi na shiri. Sautin wani waka ana salati na fara ji haka yasa nasan zasu fito daga cikin zuwa wurin taron ke nan son nasan komai akan taron na tashi naga anayin sa tun ina karama kuma duk wankan da zasuyi na iyasa sosai nima. Na mike na gyara na fara dan takawa na shige cikin su muka jera tare zuwa waje a falo muka sameshi nan ma tare da wasu yagama ya tako zuwa gaban uwan shi ya duka ta dafa kanshi tana mai addua sauran masu kurciya a wurin duk suka kai duke ana fadin Amin amin amin ya Allah. Lokacun da aka mike din ne na samu kustsawa nakai kusa dasu na tsaya har aka fito inda za a shiga mota motocine bakake wul dasu tunda zamu shigo an wankesu sai walkiya sukeyi suna sheki da daukan ido. An bubudesu da sauri ya nuna wanda mahaifiyar nasa zata shiga suka nufi wurin alokacin naja na tsaya ya kalloni da sauri nabi bayan su nima. Kowa ma yabi don ga masu kirarin su nan suna kirari har muka isa wurin motan suka shiga suka zauna uwar da kanwarshi a baya sai ya bude gaban a zaton kowa a wurin shine zai zauna sai juyo yana fadin in shiga gaban motan. Na shiga na gyara aka rufe ya koma baya tare da mahaifiyar shi suka saka kanwarshi a tsakiya sauran yan uwan su suka shiga sauran motocin dake wurin. Idona na lumshe tare da ajiyan zuciya lokacin da naji motan ya tashi ya fara tafiya damu zuwa wurin taron ke nan. Sha,aban waye wanan daka hada mu da ita ban gane ba mahaifiyar tasu ta fada abinda yasani bude idona ke nan lokacin. She is my new sectrary ya fada wanan karamar yarinyar haka aini na dauka ka hakkura ka samu wace kake sone yanzu but wanan ai tayi karama sister shi Aisha ta fada. Stop dat Aisha ya fada a kausashe ya zama dole sai ta kasance damu ke nan mahaifiyar su ta tambaye shi. Aikintane ta kula damu a wurin shine dalilin zuwa da mukayi tare ita don ta kula damu a wurin ya fada yana kawar da kai gefe daya. Shiru motan yayi har lokacin da muka isa wurin taron addua inda wani filine babba da aka ware dan shagulgula a garin banyi tsamanin taron zai tara jama,a irin haka masu yawa a wurin. Saigashi indama zamu aje mota ya zama aiki a wirin saida kyar felix suka samu a can ciki aka shiga da motan muka samu muka sauka. Dakyat suka samu kaiwa inda aka tanadarwa su iyalin shi don bayan su yan dakin su su biyu akwai wasu mata biyu da mahaifin nasa ya haifa mahaifiyar su yan yare dayane da mahaifin nasa. Yasha aure basa haihuwa ko kuma idan sun haihu diyan su mutu sai aka camfashi cewa da diyan kudin shi ke hafbaka don haka aka dinga tsoron auren shi. Lokacin daya hadu da mahaifiyar Sha,aban bai boye mata komai ba duk abinda ake zarga mashi din ya fada mata da yake bahaushe akwai karfin hali su hakan bai basu tsoro ba ya aureta ta haifa mai diya biyu kuma sunanan raye. Sai kuma suka juyacewa ai ba diyan shi bane su shiyasa yaran suka tsaya jin haka shikuma lokacin yana raye yace gaba daya duka iyalin shi za,aiwa gwajin jini sai sukaki yarda wacan da diyanta suje tun lokacin yaran suka fita rayuwan shi. Amma bayan mutuwa shi an raba gado dasu an basu kason su kamar yadda musulunci ya shimfida . Saidai Allah bai raba daya ba don yanzu su saidai sunan mahaifin nasu dasuke amfani dashi don na komai daga cikin abinda aka raba din nagadon su. Duk a wanan taron na tsunci maganganun a wurin matan dake gefena ta baya inda Allah ya rufawa Sha,aban da mahaifiyar shi asiri shine kamar su sak da mahaifi nasu har dabi,un shi duk na mahaifin nasu ne . Lokacin da aka kirasu zuwa wurin babban limamin don suyi addua ne, nabar jin me suke fada don na tashi na barsu a wurin suna hiran su na gulma. Lokacin da suka tashi din don zuwa gaban liman din banyi niyar tashi na inbi bayansu ba tunda iyalan mamacin akakira zallah. Amma tun da natuna da worning din da yai min yasa da sauri na mike nabisu a bayan muka fita tare dasu zuwa gaban liman din. Yadda suka rusunna haka nima na rusunna adan baya dasu kadan ana addu,an ina amsawa da amin amin har na gaji da duki can muka taso muna bin limaman dake zaune muna zuba kudi kamar yadda akeyi dai. Muka dawo wurin zaman mu muka zauna bamu dade da zama ba aka kawo masu abinsha dana taunawa gaban su aka aje nabi drinks din da kallo na dago kai muka hada ido dashi na girgiza kai alaman kada su taba komai fa. Zaune nake kawai amma na mayar da hankalina ga abinda ya kawoni tun lokacin da naga an fara yawo da abinci don kada a samu matsala a bangarena. Zakace hankalina yana gun program din da akeyine a wurin saidai a zahiri ina kallon abindake wakana dasu ne a fakaice a wurin. Can sai ga wata mata fara tas irin hajiyoyin lagos din nan itama mai jiki kama mahaifiyar oga din daganin ta da yanayin shiganta zaka gane itama hamshakiyace dai tazo ta rungumi mahaifiyar Ogan namu sun dan dade tare haka suna magana. Sai bayan tafiyan ta matan ta wuce ne na farga da abinda ya faru a lokacin saboda baka dauka yadda sukayi da junan su kadauka akwai wani na mugun nufi a tsakanin su. Na rasa yadda zan sanar dashi an samu matsala sai dabara ya fado min wayana na tura mashi text da fadin if possible kasa mahaifiyar ka ta canza gyalen jikin ta yanzun nan akwai sherin da aka shafawa gyalen kada ya taba jikin ta . Sai aka samu akasi bai dauki wayan ba a lokacin don mutanen da sukai yawa a gaban su suna kawo gaisuwa lokacin. Na rasa yadda zanyi kawai saina danna mai kira ba kakautawa na matsa da kiranshi ina kashewa har yakai ya ciro wayan nasa ya duba sai yaga sakon da sauri ya dan juyo na gyada mashi kai alaman eh. Rubutu na hangoshi yanayi ga wayan shi ya turo min What would we do now ya aiko min da sako na tura mai da fadin mu tashi zuwa resting room zan kawo mata gyale yanzu kada kowan ku ya bari gyalen ya tabeshi. Ya gyada min kai bayan na tura mai da sakon sai kuma na turawa Adnan ta wayana nabi bayan su zuwa dakin hutun da zasu jira din. Muna kai kofan nake jin uwar na masifa don me wai ya dago dasu zuwa nan sai da muka shiga ya kalleta yace akwai matsala don akwai abinda aka shafa maki a jiki ki a wurin rungumar ki yanzun nan shi muke son ki cire wanan gyalen da sauri ba tare da maganin ya taba jikin ki ba . What ta