Sashe 9
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
dole sai ka kula da kanka sahiba yau kaji wanan ya samu wance . Gobe kaji ai wancen ga abinda ya sameshi shiyasa a kullun nake kafa kafa da rayuwan ku da nawa a garin nake zama wawiya mara wayau ga kowa a garin nan . Badon komai ba don kawai mu tsira da mutunci mu a garin nan yanzu kinje yau kin karbo kudin wanan mutum gobe kuma da wata zance zaizo maki don ba zai baki abinsa a banza ba. Yanzu zan fita in masa kashedi a kanki yayi nisa dake kema hakan ki nisance shi kada ki kara yarda da kalaman sa a gareki . Don dan adam mugun ice ne wanda ka yarda dashi ka amince masa shine zai dawo ya cuce ka akarshe. Koda kuwa dan uwankane a wanan zamanin zai iya cutama idan ba,yi dace da dan uwa na gari ba sai a hada dashi a cutama. Tashi mu fita naga maishi ta fada tana mikewa tsaye sahiba ce ta fara fita a dakin umma tabi bayan ta zuwa wajen saidai suna zuwa babu kowa a wurin sai mutane dake dan gittawa a lokacin. A nan na barshi fa umna na fada kafin in sake cewa na barahi a bayana tafe na shigo in fada maki nan dai ta kara kwashe yadda sukayi har ya bata kudin da tafiyan shi. Yazo neman wanine a garin nan umma ta sake tambayan sahiba wanan kalmam daga ida take tsaye da sauri a cikin yanayin damuwa da tsoro na,amsa da haka yace umma . Don dai ni bai min magana ba ban iyaka yaga wani zai mun rashin mutuncine yazo inda naken ya kori mai shi. Shige ciki mu tafi umma ta fada da sauri suna shiga suka hango Amar a tsaye yana kallon iya wale dake fada a kofan su ta dauki tsohon abin gashin masaranta data arawa sahiba din a cikin masifa irin nata maineman nayi a kullun. Bayan sun shi aka kara gwaucewa da wani ruwa mai karfi dole kowa ya nemi mafaka saidai hakan baisa sahiba ta zauna ba. Nan ta shiga gyaran dakin su da tara masu ruwan amfani ga yan kayan dake garesu na aiki sai yamma sosai aka dakatar da ruwan zuwa lokacin yunwa yaga halaka haka ta fito neman abinda zasuci a cikin duhun nan bread da shayi ta dauki kudin jiya ta sayo don wanan kan da aka bata ta gama tsorata dasu a zuciyan ta. Kodata dawo ta samu Amar har ya soma barci a lokacin ta tayat dashi suka sha suka kwanta bafon sun koshi ba. Washe gari bata so fita school ba amma umma ta gargadata dole ta tafi har lokacin data dawo bata sake jiki ba a gidan. Wajen gidan su ta fita ta samu dan karafuna tayi dubaran hada hada abin da zata gasa sauran masaranta na jiya ta fita dashi duk da umma bata so hakan ba sai dai don kada ayi hasaran kudin da aka saya ta barta ta fita dashi hakana . Allah ya taimaketa ta sayar da wuri don haka taje kuma ta sari katin waya tana bin motoci dashi har zuwa magariba ta dawo gidan da abincin data sayo masu don tasan ba wani abin kwarai a cikin su tun jiya. Bayan sun gamane suna zaune ta kwaso littafanta tana assignment din su na makatanta, Muryan ummane yadaki kunnuwan ta tana fadin ina kudin da mutumin nan ya baki taji gabanta ya fadi don tsoro a sanyayye ta dago kai tana fadin yana a cikin jakar kayana na boye. Dauko mu kirga nawane a gani ta mike da sauri ta dauko kudin suka kirga tayi wani irin zabura lokaci guda don ganin yawan kudin dake hannun ta a mike sabbi fil dasu. Dubu saba,in ne cif a hannun ta ta dago kai da sauri ta kalli mahaifiyarta dake kallon ta daga gefe itama a tsorace. Wanan kudin ya baki su duka zama guda Sahiba da alama wanan yana so ya shigo rayuwan mu da yaudara dole akwai abin da yake so a gurin ki. Tsorone ya kara kama Sahiban don zancen akwai abinda yake nema a wurinta da umma ke yawan fada din nan ko yaushe.