Sashe 62
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummace kawai ta iya budan kayan da aka shigo muna dashi din nikan ina zaune ina faman tunanen rayuwa a zuciyana. Ina tunanen wai wani irin kiyayyane tsakanin mu da yan uwan mahaifin mu haka da har yasa umma ke gudun mu dasu haka ? Idan ita ummace basa so aimu ba zasu kimu ba tunda sune mahaifan mu ai dole ko su so yayan dan uwan nasu ai na fada. Abinci mai lafiya aka kawo muna wanan daren kan naci nasha na koshi na kuma yi barci mai dadi a ransn duk da tunanen yadda zan ga yan uwana ganin farko a rayuwana. Asuba mun tashi lafiya bamu kara barci ba sai mudin ganin yan uwa da zamuyi mukeyi a tsakanin mu inda nake cewa Amar ai suna da kama da wanan boda din namu sosai. Umma dai dake jin shirmen mu kamar almara wai muna zumudin zuwa ganin yan uwan mu a cikin ranmu muke wanan shirmen haka don tasan shirmene sai anje can gida mun ganewa idon mu abubuwa zasu rikice muna a can din ai wanda bata fatan komai ya samu wani daga cikin mu kuma. Shiru shiru a ranan bamuga wanan boda din namu ba kuma bai leko mu ba tun hakan yana damun umma a zuciya har dai takai ga yin magana a fili game dashi. Nace umma ba zai manta da muba ai tunda kinga ya kawo muna abinci da safe munci don haka muna a ransa wata kila akwai abinda ya tsare shi ga zuwa ne. Wasa wasa har magariba babu almanan shigowan shi dakin da muke din har zuwa lokacin da muka shiga barci. Abubakar din ne zaune a dakin mahaifiyan su bayan sun gaisa sun dan taba hira ya jefo mata tambaya da fadin. Wai umma meye dalilin barin gidan iyalan Abba sambo ne da har yanzu naji ba wanda ke zance a kansu. Wani irn juyowa hjy din tayi kamar ta kadu da jin sunan daya ambata din yanzu a gabanta din tace ina ruwan ka da wanan zance na manya ta fada a cikin daure fuskan ta gareshi. Shiru yayi ya dukar da kanshi kasa kamar mai tunane muryan mahaifiyar nasa ne ya katse shi tana fadin kada ma ka kuskura kace zaka tsoma bakin ka a cikin zancensu a yanzu. Koma ka tsoma din dawa zakayi mutanen da da suka bata cikin duniya ga baki daya babu labarin su har yanzu ina ruwan ka da zancen su kuma. Tunda yake bai taba mamakin kalaman daga bakin hjyn tasu ba irin yau din nan don bai taba zaton zaiji hakan daga bakin ta ba ma. Sai gashi ita da kanta take masa warning kan hakan da ya fitar da bakin sa a cikin rikicin gidan su ya rufa masu asiri. Idan har yaya Nuhu yaji wanan zance ai sai ka lalata komai a tsakanin mu kuma a yanzu gashi Addah Dada daga ranan da tayi zancen su a gaban shi tun ranan ya rufe da ita dashi da wasu yan uwa namu sam basu sin zancen shi a cikin mu ko kadan. Ajiyan zuciya ya sauke tare da mikewa tsaye yana gyara rigan shi yake fadin nizan tafi don ba dadewa zanyi ba na dai shigone kawai. Don a yanzu ya kara tabbatarwa kanshi cewa akwai wani al,amari dake boye tsakanin wanan ahalin dasu yara basu sani ba. Haka ya tafi cike da mamakin yadda hjyn ta nuna mai nan take inda ya doshi gidan shi kai tsaye har ya shigo Nazifa na kan waya don bata dauka zai dawo a lokacin ba . Don shigowan safe yayi masu a bazata kuma hakan bai hana shi sauke mata hakkin ta ba dake kanshi a lokacin. Shine take waya da yar uwanta kuma aminiyarta tana fada mata irin yadda suka kasance a tsakanin da yazo din duk a kunnen shi tsab yaji komai haka yasa ya juya zuwa dakin shi ba tare da tasan da ya shigo gidan ba lokacin. Dakin shi ya shiga ya kwanta cike da takaici da jin haushin wanan yarinyar mai tonon asiri haka garesu. Haba abu yayi mai yawa a zuciyar shi da zancen hjyn su zaiji da shi da sukayi dazun nan ko da zancen wanan sakaran yarinyar da take wai matsayin mata a gareshi yanzu. Wani iri yake ji a zuciyar shi haka yasa ya dauko wayan shi ya kunna kira,a a cikin shi ko zai rage jin abinda yake ji a ranshi din lokacin. Cikin ikon Allah kuwa ya fara jin zuciyar shi tana sauka masa har zai iya yin tunanen mafita a kan mu a lokaci don duk wani zafi a yanzu ya daina jin shi kuma. Baida wani manufa a yanzu daya wuce ya tunkari daddy su da wanan zancen yaji ra,ayin shi akan hakan. Wayan shi ya dauko ya kira layin mahaifin nasa duk da yasan ba lalai bane ya sameshi a yanzu don yasan lokacin aikine a lokacin. Sai gashi cikin sa,a daddy din ya dauki wayan nasa suka gaisa bayan sallama dashi suka dan taba hira kafin ya jefo mashi tambaya da fadin. Wai daddy wanan zancen iyalan Abba sambo da suka bata a ina ya kwana yanzu ne don gaskiya bai kamata ace an fita batun su haka ba suna can cikin duniya suna wahala. Tun bayan da mukaje neman su din nan wanan zancen yake damuna daddy sosai wallahi ya fada cikin sanyin rai. Mahaifin nasa ya tare shi da fadin ka samu wani labarine game dasu a yanzu ya tambayi dan nasa cikin kaguwa Abubakar din yace. No daddy naji kawai ka daina wanan zancen ne kuma shine na tambaue ka ya fadawa daddy din a sanyayye kamar bai damu ba. Watau Abubakar idan har bamu taimaki ahalin nan ba nasan sai Allah ya tambaye mu gobe kiyama don yadda alhakin neman nasu ya rataya yanzu a kan mu . Sai dai nasan da yawa daga cikin mu basu damu da hakan ba ni kuma yanzu abubuwa sun hanani wanan binciken a kansu yanzu. Daddy ka ban baki tun ban bar lagos ba na nemo makasu a garin nan idan suna nan cikin sa don wanan yarinyar da na gani gaskiya tana mugun kama da jinin gidan namadi daddy sosai. Moddibbo kabi sannu kada wani yasan da wanan zancen koda mahaifiyar kane don sanin hakan yana iya jawo maka matsala da yan uwana a yanzu. Duk da nasan kai din namijine jan gwarzo zaka iya komai kace zakayi a rayuwan ka a yanzu saidai ina kara fadama da kabi wanan maganan a sannu har in zaka iya hakan . Don nasan ba banza suka bar duk wani wanda yayi yunkurin dawo dasu a cikin muba a yanzu din don muggan mutane masu amfani da al,ada bisaga addini shine kawai akidar da suka rike don jahilci. Kada kaji komai daddy a yanzu a kaina insha Allahu adduan ku yana amfani a gareni a kullun dan guntun murmushi mahaifin nasa ya sake mai don jin abinda ya fada a lokacin. Wai rikici ya fada a fili bayan ya kashe wayan yana mamaki kan wani shirka can zasu jefa wa yan nan mutane haka a cikin wanan ukuban rayuwa. Abu na farko da zai fara shine ya tabbatar da mun samu mun murmure kafin mu koma a cikin yan uwa din sai kuma zancen karatun yara idan bai manta ba ai ya taba ganin yarinyar saye da uniform a tsohon unguwar su da suka baro. Jin an shigo mai dakin yasashi kara daure fuskan shi sosai a lokacin don yau zai nuna mata ko shi waye don taji dadin gulma da tushe. Har kwana uku bamu ji duriyan shi ba a wanan lokacin gaskiya ba umma ba har mu din mun fara shiga halin damuwa ga hakan. Muna zaune dakin munyi shiru tv kawai da nayi karanbanin kunawa a dakin ke aiki don hankalun mu baya wurin saboda bamu saba da wanan kalle kallen ba a rayuwan mu. Shiyasa ko yanzun ma din muka barshi yana aiki shi kadai don amar ya fara kallo sai barci ya dauke shi a hakan. Sahiba tsoro fa kar mutanen wurin nan su kai ga koran mu nake ji gashi yaron nan tun shekaran jiya rabon shi damu a wurin nan. Kardai ace ya gudu ya barmu don nasani dama ba zasu barshi ya mayar damu gida ba kamar yadda muma gidan ya fice a ranmu ga baki daya. Idan ko har haka din ne har yanzu tsugune bata kare muna ba don gara mu tattara inamu inamu mubar wurin nan baki a lekum idan bai dawo ba gobe. Wani irin ba dadi naji har kasan raina saidai ba yadda na iya ga hakan shiru nayiwa umma din nake hango abin kamar shirine hakan sukai muna dama. Bana fatan goben yayi don abinda umma din ta fada a kan zaman mu a cikin wanan gidan da bamu san kanshi ba muna dai cikin sa zaune kawai ana kawo muna abinci muna ci ga kuma kulawan da muke samu din a wanan wurin. Haka din kuwa Allah yai dare gari ya waye ina ta tunane da zullumin akan zancen mukaji anyi sallama a kofan dakin namu za a shigo. A Yanzu kan na sheda muryan shi ko a ina naji don saurin fahintar da nake dashi din a kaina, ummace ta amsa mai ya karaso ciki ya samemu. Muna zaune a cikin kayan da dai ya san mu dashi har lokacin don ba wanda yai amfani da nasa kayan da ya sawo muna din. Da alaman baiji dadin hakan ba daya gani ya dai daure suka gaisa da umma yana bata hakkuri kan rashin ganin shi da bamuyi ba na yan kwanakin wai tafiya ya kamashi ya tafi kuma ga ba waya a hannun mu yasa bai sanar damu ba. Umma tana fadin ba komai ai tunda Allah ya dawo muna dakai lafiya nika har na yanke shawaran yau idan bamu ganka ba sai mu bar wurin nan a yau din. Haba umma ai ba zan kawoku nan in tafi in barku a nan din ba cikin hotel koda bansan darajan ku ba nikan hausan da sukeyi sai nake jin shi a kunne na wani bakon hausa ne ba wanda muka