Sashe 203
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
bata sameni ba da yake ranan Friday ne ban jima a wurin aikin muba dana kammala komai a ranan a bangaren mu yanzu sai sammaci da za a turawa ko wanin su da dakatar da wa yanda zamu dakatar ne a wurin aikin ranan monday kawai ya rage muna kuma mun shirya yadda abi zai kasance a ranan. Tun bayan magariba muka fara shiri don ban son zuwa da wuri sai wajajen goma na dare tare da duk abokan aikina na da muke tare na gaiyace su don haka su zasu mara min baya a wurin an kuma tsara ga yadda abin zai kasance damu tunda rana. Yadda nake shiri haka aka wuni da kuskus a wanan wunin a gidaje da dama saidai abinda ke daure masu kai bai wuce tambayab kansu da sukeyi har in mune toshi dayanyaron fa dan waye ? Gabin ban zoba yinin bukin sai aka fara share zancen wasu sun manta da maganan amma manya kan yana a cikin zukatan su fam. Annoucement din da aka farane a wurin ya jawo hankalin mutane inda Bello ya samu sayen mc din da kudi mai yawa ya fara shelan sanar da mutane dake wurin zuwan mu hakan yaja hankalin duk hall din a lokaci guda. Ga sanarwa ta musanman ga amarya da ango cewa kanwar ango kuma yaya ga Amarya miss Sahibat Sambo Namadi yar uwa ga ango da amarya ta iso wanan wurin da tawaganta daga lagos zasu shigo don taya amarya da ango murnan wanan ranan. Ya Abubakar dake zaune shi da nazifa da sai ranan daddy yasa yaje ya dauko ta ba wani musu yaje gidan yayi sa, a Alh Nuhu baya gida ta biyoshi suka dawo har lokacin da suke zaune wurin dinne din ba wani sakewa a tsakanin su. Yayi wani irin juyowa shi tsorin shi a lokacin kada inzo da yaran shia san suna wurina yaji amma bana shigowan mu ba don yasan a yanzu zan iya yin fiyema da hakan ai yasani a yanzu. Cool music aka saka na hakan ya kara jawo hankalin mutanen wurin kowa na baza ido yaga wanan da aka fada an bude muna hanya sosai don aikin kudine bamu shigo ba saida aka shirya komai na shigan namu. Mazan saye suke a cikin suit mata mu hudu matar Adnan muniya da yemisi saini sai mazan majiya karfi wurin su goma a bayan mu dauke da manyan sacks dake dankare da kayan rabo. Kallo ya koma kanmu ina tsakiya sai walkiya nakeyi don bakin kayan dake jikina dare ne suna da shining dake sasu walkiya dinkin rigace daya matseni sharp din cock cola dina ya fito a fili kaina yasha ado shima ga sarka mai dan karen kyau a wuyana yana walkiya. Murmushi na fara duk table din da yan uwan mu suke kamar an fada min sai na dagawa mutanen zaune hannu hakan kuma baisa na tsaya sai nufar inda amarya da ango suke nakeyi sauran na bina a baya. Ganin na hau steps din inda suke zaune yasa suka mike Baby ta haroni da sauri ta fada saman jikina na dan bude idanun ta ina share mata fuska kafin inji muryan angon na fadin sannu da zuwa yar uwa na juyo gareshi har lokacin ina rugume da yarinyar a jikina tana dan kukan da bansan ko na meye ba a cikin harshen turanci nayi mai magana dashi kadai yaji menace ya danyi murmushi na nuna mai abokan aikina suka fara gaisawa dasu itama nasa ta gaisa da matan abin da muka shigo dashi yan matan dake tare damu da samar suka fara bi table table suna ajewa nan take wurin ya rude da hayani har muka samu gaba dayan mu muka sulale daga cikin wurin ta kofan baya ba bata lokaci muka bace wa kowa dake tare da mamaki. Kuwa bayan yaki don an turo wai abi bayan mu saidai ko kuran motocin mu ba a gani ba har na masu rabon kayan da aka raba din wanda shi ya dauke hankalin mutane suka hargitsa wurin jakkane wani dauke da kayan wanka wani kuma kayan shayi wani riga mai hoton amarya da ango haka kayan sukazo launi launi duk abinda ka samu shine rabon ka. Gara kafito kaji meke faruwa don abune daya shafi Sambo namu marigayi dai daka sani jin hakan ya tsaya sauran wayan har ya fito a gigice cikin dakin suke zayyana masa abinda ke faeuwa wai ashe tun jiya yarinyar ke barazana a ahalin mu amma an rasa wanda zai fada muna wanan zancen. Kai Sani kaga yarinyar ne da idon ka wanda aka kira da sanin ya gyara zama yana fadin umm,humm bari yayace wallahi naganta buhari ma ya ganta kama da uban su sak saidai don ita mace ce kawai ta dan bambamta da uban amma namjin kan ai kakine kawai na Sambo din. Kayan dake gabanshi ya kalla kamar mune kayan irin kallon da yaiwa kayan lokacin kafin ya nisa yace aikin banza ke nan har inma gaskiyane kowan ku nan ai yasan Sambo baida da namiji ko ? Alh ba wanan zancen a yanzu kamata yayi mu fara sanin waye wanan yarinyar wai kuma a ina take zaune amma kafin nan dole muga Ali dcp muji komai. Kuna bani mamaki wallahi matar nan da yarta fa wurin malamai bakwai sun sheda muna sun mutu kuma malaman nan ba wai hadin baki bane sukayi tunda ba wanda yasan wani a cikin su kuna nufin hakan karyane ke nan. Saidai dama idan ya zauna da watace acan daban irin zaman bariki tunda kunce yarinyar kamar kabilace ai haka yake don gaskiya shiganta kamar na kabilune nagani buhari din ya fada a sanyaye kafin ya fada cikin tunane. Falon ya kara shiru na tsawon lokaci karan wayan Alh sani ne yasa kowa ya daga ya kara wayan a kunnen shi yana amsa sallama tare da sauraren bayanin maishi din wanda ya kirashi a lokacin. Abinda ya fada tun kafa wayan a kunnen yasa su kara mayar da hankalin su wurin Sani din da yake fadin dama nima nayi zargin shi dcp Aliyu din don in bata da alaka dasu tun farko me zaisa har tazo bukin yar su yanzu? Ya kashe wayan bayan ya gama sauraren na cikin wayan yana fadin kuji a yadda ake fada yanzu wai yarinyar ta zauna a gidan Ali dcp na wani lokaci kafin su koma inda suka fito. Yanzu kuma wata babbace ake gani ko wani babban mutum a can kudu take aure amma dai za a binciko min ko yar Sambo dince ta asali. Shirmen banza ke nan shirmen wofi nifa duk wanan zancem a shirme na daukeshi a wurina sam ba zai yuyu ba son wanan rudani da kuke nuwa sai a gane da wata a kasa . Idan har yar Sambo dinne tazo mana mu kawar da ubantama balle ita me zata iya yi damu yanzu kuma ? Ina abinda dai kuke tunane ke nan sannan shi Alin har in shiya kulla wani makarkashi na zuwan wanan yar aiko shi bai tsira ba a cikin zancen Alh Nuhu ke wanan maganan rai bace. Falon yai shiru yaci gaba da fadin yanzu dare yayi koma me ke nan sai a bari har zuwa safe ba sai muga shi Aliyun muji gaskiyan maganan a bakin shi ba. Kallon shi Buhari yayi don jin abinda ya fada na a gaja dashi Aliyun aji me zai fada game da zancen don su san matakin da zasu dauka. Karfe biyu saura sai alokacin suka fito kowa ya shiga motar shi ta alfarma da sukazo gidan dashi zuwa gidajen su ciki da zargi da tunanen wani ne keson ya kulla masu shiri kaqai da hakan. Yadan dade a zaune yana tunane kafin ya mike zuwa wani daki dake part din nasa ya rufo kofa ya fara abinda yake sonyi a dakin lokacin