← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 197 OF 337

Sashe 197

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

bani son zancen yaron nan a gabana kwata kwata wallahi na tsani wanan dan iskan yaron a rayuwana mai kafiya kamar irin na ubansa. Hakkuri za ayi Alh tunda aure ya hada harda zuri,a uwargidan nasa ta fada a sanyaye ya mere baki yana fadin to tunda ya hada ai sai ta koma can wirin su baffa Amadu su mayar da ita. A daiyi hakkuri Alh abi abin a sannu zaifi hannun ka baya ruba ka yanke aure ya riga daya gama yanzu kuma kaga dama kuma ga zumunci a tsakani. Bai kara magana ba don bacin rai har ta karasa zaman ta tashi ba tare daya iya furta komai ba a lokacin don yakai wuya makura da zancen. Wasa wasa sai gashi ana share kwanaki ba wanda ya biyo bayanta daga can gidan shima ba, a jishi balle a san inda suke da yaran. Wanan ya tayar da hankalin mommy sosai ga zancen bukin su daya doso kai sai abin ya taru ya zame mata biyu lokaci guda. Anty Amarya taji komai amma tunda ba a fada mata ba sai ta share saida tana gulma da mutanen ta idan sunzo su kuma in zasu fita hjy Addah na falo zasu sake mata haibaici da cewa aikin huta ki aurar da yarki ki huta ba sai ta girma maki a gida kuna gwada sa, a ba. Wanan irin zancen yakan dagawa mommy hankali sosai saidai bata nuna tasan dasu akeyi don kada ta biye masu a tafi da ita ana yadawa a gari. Daddy ko a waya mommy ta kirashi ta fara fada mai abindake faruwa da Abubakar din tun cikin wayan ya fara sababi dasu . Daya dawo kuma ya dora a inda ya tsaya inda yake shiga ba nan yake fita ba dama uwa itace mai daukan kwaram ko yaushe. Bukin kan an farashi gadan gadan ba kama hannun yaro saidai kuma dan cikasa din da aka samu daga bangaren ango don yaki sake hannu yadda uwar yar keson ayi a bukin. Gidan baffa Abdullahi kanin daddy za, ayi kamu ban samu zuwa ranan ba yadda naso saboda na dade a wuein aiki sai washe gari da za ai mother's day a gidan gwaggo hari ne na samu halartan taron . Mun isa musalin biyar da rabi duk girman gidan ya cika da mutane tun daga waje har cikin shi da jamma,a wuri na samu nayi parking din motana na fito tare da Ammar da babban dan Abdul sai muniya da mukazo tare. Dogon riga ne dark blue har kasa yaji duwatsu daga sama zuwa kusan cibiyan rigan muniya ma ba a barta a baya ba tayi shiga na abaya mai kyau sosai. Shigan mu kawai zai nunawa mutum cewa mun banbanta da yanayin yan wurin dole wanan idan na gitta a sau anjuyo ankara kallon mu karo na biyu don shigan yai min kyau sosai a ranan don ko takalmana da jakkana abun tsayawa a kallane a wurin. Wayata na jawo iphone thirty ina kiran layin Faiza dake can cikin taron jama,a a lokacin sai can taji ana kiranta ta dauki wayan tana dubawa taga sunana da mamaki take kallin kiran ta fita daga wajen taron zuwa cikin gidan tana daukan kiran. Kwana biyu sahiba ina ta kira bani samun ki nace ayyah kina ina yanzu tace kin san an fara bukin baby muna wurin mother's day yanzun haka . Ki fito gamu a waje ki shigo damu nace mata a takaice don bana jin ta sosai a lokacin kai abin sherine aida nasan hanyar lagos wallahi da kin gani watarana. Ki fito mana na fada a dan tsawace ta sake fadin wai iskaci sheri wai zaki min don kinki zuwa ko ke wata iri ce wallahi zan koma donke fa nazo wurin nan . Waida gaske kikeyi ko wasa nace ke bakiji kidan wurun nan na tashi a wayana ba aiko inaga taji din don wani irin ihu data sake lokaci guda. Baifi yan mintina ba tafito waje tana raba ido gamu a gabanta ta wuce tana basarwa na kara danna wayana nace wai kinyi haukane zaki wuce duk a cikin turanci muke magana don shi na shirya yi a wurin . Juyowa tayi inda muke ta kara kallin mu saida ta tsaya tayi min kallin tsab kafin ta yanko da gudu ta rugumeni nima din rugumeta nayi muna murnan ganin juna. Wai sahiba kece nan ko gizau idona ke min kece kika koma wata lady dake haka don Allah ? Murmushin cikin aji wanda a yanzu ya zame min jiki na sake mata ganin hankalin mutane yana dawowa garemu muniya na gefe tana muna murmushin ganin yadda mukeyi. Ina Ammar da umma na nuna mata Ammar a gefena dake tsaye Ammar kaine ta fada tana nufar shi ta rugumeshi gaisuwa irin na yaran lagos yayi mata. Goodevening ya fada tare da dan rankwafo kai yana dan daga kafa daga baya itakan mamakin wanan sauyin namu takeyi har kasan ranta. A tare muka jera zuwa cikin wurin taron da ita sai hankali ya dawo garemu don yadda aka jera kujerun na zaune zasu iya hango masu shigowa gidan. Tun kofa naji an fara tambayan ta su waye wa yan nan faiza sister din mu ce take fadawa mutane kawai. Murna yayiwa faiza yawa bakinta bai rufuwa a lokacin sai yankawa mommy kira takeyi alokacin cikin taro tana rungume dani mommy ta juyo tana fadi mommy ga Sahiba. Fatima dake can tana magana taji ana fadin sahiba ta juyo ai muna arba ta sake kara ta kama bangaje mutane tayo wurina tana ihu jin dadi tare da kiran sunana. Hakan saiya kara jawo hankalin mutane garemu sosai kowa na kallon mu Amira ce tasani kaiwa da dan sasarfa muka rungume juna a wurin . Mommy ta taso anty amarya ma taso ina binsu muna rungumar juna ina gaidasu saiga Nabila da hauwa muka rugumi juna gaba daya yan gidan sun nuna inada ma,ana a wurin su. Kafin muka dan zauna na dan lokaci dana dago kai zanga yadda mata ke kallon mu suna magana muka dan juyowa nayi ina fada mata muje motana su kwaso kayan gift suna a bayan mota mu zamu tafi. Ina zaki ta tambayeni nace inda muka sauka fatima ce aka tura ta fadawa Anty Amarya sai gata da kanta lokaci guda muka mike don barin wurin idone ya bine caaaa. Takawa nayi inda mommy suke zaune tare dasu gwaggo hari har kasa nakai ina sallaman su don ladabi ban damu da idon mutane dake kanmu ba a lokacin. Hakan ya kara nunawa taron cewa suna da ma,ana a wurina sosai yadda nayi masu din lokacin kuma anty Amarya ta iso tana fadin Sahiba kuyi hakkuri ance zaku tafi ba a gida zaku saukabane ?. Kaina girgiza ina fadin akwai inda muka sauka ko tunda nan za ayi yawa ta kara fadin fatima tace kince azo a kwaso serbeniya ko nace eh Anty na kara juyawa nayiwasu gwaggo sallama muka tafi harda anty din son rashin yarda da bata dashi. An bude ta cika da mamaki sosai manyan kwalaye ne na jug masu kyau tun gida umma tasa na ware ma mimmy nasu da yanzu naga kunya a idon ta karara don ganin mu da tayi. Faiza na dankawa nasu naba mommy saura haka aka kwaso zuwa cikin gidan gwaggo hari gaba daya don anty tace basu rabuwa a wurin lokacin. Ido caaaa suna tsaye har na tayar da mota muka barsu cike da mamakin ganin mu a ciki bakon yanayin da mukai masu na bazata lokacin.
Chapter 197 · 0% Book details