Sashe 86
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wasa wasa buki ya fara kan kama zakace ko a gidan daddy ake bukin duk wanda yazo ba zaice yaga umman mu ba a taron nan saidai nikan dani ciki tsunbul ake komai ko banzo ba fa,iza saita kirani a lokacin. Anko har kala biyar akai muna ko wani da sunan shi inda Allah ya kara rufa min asiri akwai baki da suka zo masu daga illorin da ibadan kawayen gwaggo Asiya da diyan su. Duk da manyane sun girme ko anty Nabila balleni karaman su sai ya kasance sunji dadin hakan a tare damu duk inda na shiga zasu nemoni su fada min abinda suke so. Sai itama gwaggo din hakan yai mata dadi don na zama kamar ta gida a cikin su yanzu din tunda ba sanin matsayina sukayi a garesu ba. A gaskiya naga mutane masu son junan su da kaunan zumunci a wanan bangaren nasu daddy don har daddy din da kansa saida ya shiryawa amarya dakin guda nasa na kansa hakama gwaggo Hari itama tayi nata bajintan sosai a matsayinta na kanwar mahaifiya kuma mai buki. Duka gidajen nasu ga baki daya ya kicime da baki yan buki don haka ko ina ba masaka tsunke a gidan lokacin haka yasa tausayin umman mu da azzalumi Nuhu yasamu zama a cikin hijabi don tsoron sherin sa da halinsa sai naji tsanan wanan mutumin a lokacin ya kara shiga na sosai wallahi. Tundai da Fa,iza ta nuna min iyalinshi a wurin kamu take fadin ga iyalin gidan matan yaya modibbo can sune iyayyen matansa da yayan su. Na kalli wurin sai wani hura hanci da jiji da kai da sukeyi suko mutane yan uwa sai wani basu girma akeyi a wurin ana fadin wai buki yayi buki tunda har yan gidan Namadi sun halarci wanan bukin haka kwansu da kwarkwata. Wasu dake kusa damu suke fada daya tace don sun san su din masu bukin masu hali ne kamar su da ai basu zo ba yo gwaggo Hari ai itama tana nuna masu itace ki duba shigan ta ki gani wane nasu Allah dai ya cece ta kada kuma a sakata a baki don kinsan su basu son suga kafisu fitowa a wuri yanzu suna nakasa mutum ya koma baya . Keko dai kinsan fa sune kusan abokan karawan su a cikin family din nan anty hauwa ce ta kwala min kira daga wurin da yan gidan suke zaune nazo. Tunda na tunkari wurin suka zubo min idanuwan su banjin zan iya gaida kowan su don haka ina zuwa nake fadin gani tace jeki ki kawowa su mommy wasu kujera guda biyu. Nace me i don no, where to find chair now, people are sitdown on it, who igo weak here ? Ina fadin haka na bar wurin don idanun da suka zobo min din suna magana a kaina don naji daya ta fara fadin wai wanan yar ce dama ba bahausa bace gata da ka ganta zakace yar filoce ita. Waima me sukeyi a gidan har wanan lokacin basu koma bane daya ta fada sai lokacin dana juya zan wucene na farga da matar ya Abubakar a wurin na sakai na koma inda na fito. Duk da bukin ya kawatar dani saidai hakan bai hana zuciyana jin bakin cikin dake damuna ba na duba duk taron nan amma ummana na gida a kumshe ta dalilin su. Taro yai taro don bansan kowa ba ga iya yi dana koya a geto kuma tun ina karamana na bude idona a geto ne yasa suka ban raba kayan buki don su yan gida kada suyi laifi a wurin su. Aiko ido rufe tunda ba sanin su nayi ba nake ba kowa daya daya ko kin dawo kina min guntun turacin ki bazan kara maki ba. Har kowa ya samu da hannu wata yar gidan ta kirani kamar in shareta sai naje take fadin i beg give three servoner for our moms na dan kara kallonta kafin in tura hannu cikin buhun na ciro jakkuna guda ukun daidai na mika mata da sauri tana magana na bar wurin. Idan ka jawo rigana ta baya zan sa gwiwan hannu in buge inci gaba da tafiya bana waigen bayana balle inga waye ke jana yar Geto ke nan sai ido. Anty amaryan daddy ta yafotoni da hannu nazo wurin take fadin in ba bakinta da yan uwanta baida yawa na mika masu buhun duka na koma wurin motan da muke dauko kayan a nan na samu gwaggo hari tsaye. Tana ganina tace dani ance ba a bani sai kinzo ki ban na mutane na gasu can dan murmushi nayi karo na farko a warin gabanta ne yayi mugun faduwa saida ta kadu ita kadai tasan abunda idon ta ya hasko min a kaina lokacin. A sanyaye nace gwaggo how many a cikin murmushin da har lokacin kesa gabata faduwa tace give me firty, na bata ashirin ina dariyan daya daga mata hankali don su suka san mahaifina da tashin shi sosai don a dakin su ya tashi in kin tuna da labarin mu. Tun wanan lokacin take bin na da ido da kallon tsoro a zuciyanta tabbas yayan su ya boye masu wani siri duk yadda akayi ba zata taba manta dan uwa kuma abokin shawara a gareta ba sambo. Kai yar sambo fa da matarshi sunyi tambaya fun ana cewa suna raye har aka koma cewa indan sunje gun malamai duhu ake gani ba a ganin ma,ana ke nan mun mutu saida kama kawai don haka taba zuciyan ta salama a kan abinda ya fara raya mata din. A can gidan ta muka nufa bayan an tashi a taron kowa yana mayar da fadi ina zaune nayi shiru don hankalina ya koma akan umma lokacin. Muryan gwaggone dake fitowa tana fadin yau kun bamu wahala kun dauki rabon abu kuba wanan bobanyan da bata san nagida balle na waje. Da sauri na dago kai don wanan hausan yaimin tsaurin fahinta take fadin ai kunyi daidai don da an wawashe shi duka lokaci guda amma yanzu kunga kowa ya samu ai . Wallahi gwaggo idan ba haka mukayi ba ba zamu iya da mutanen mu ba amma kinga ta raba an zauna lafiya har yan gidan kawu Nuhu daya daya ta mika masu shine suke fada wai ba,a karamasu ba a wurin. Kyale yan sallo da jin kai ai na hangosu suna min wani kallo na fita batun su wa zasu dinga hankadawa su a dole ga matan mai kudi dole a bisu da ace ma mutum baisan asalin kudin nasa bane zasuyiwa mutane iskanci. Wani irun kallo nayi mata kafin nayi kasa da kaina lokaci guda ina duban wayan Fa,iza dake hannuna lokacin don ni banda waya ba a sai min ba. Wayan gwaggo ne yayi kara lokacin ta dauka tana waya sai na bita da kallo don matar nada sha,awa gashi tasan kanta sosai irin wayayun matan kaduna din nan ne da suka san duniya ta waye har ta gaji gidan ta tsab dashi babune kawai babu a gidan don tsaruwan shi. Da murna ta juya tana fadin ashe kace yau ina da bako ke nan barin fadawa driver yaje dauko ka kome na wayan yace naji tace kwarai kuwa abokin kane dole kazo bukin shi saika iso din banda dare kasani. Gwaggo halan ya Mustaphane zai shigo hauwa ta tambaya tace shine dan ka,ida aikinji yace kada azo taron shi sai na ganshi dai kin san sune angon ne ai. Sune fa ya modibbo ma daya koma shekaran jiya na ji matar shi na fadin yau ko gobe zai dawo dazun . Mikewa nayi tsam dayan yan ibadan din bakin nan tace dani enbalalo nace i wan go see my mother nasan yanzu tana can ta damu da rashin dawowana gida. Na kalli inda fa,iza take ina fadin tashi muje gida tace min da wani mota mujira anty Nabila ta kaimu ai yanzu zamu wuce. I go track na fada tare da daukan jakkana na fita banyi sallama da kowa ba a get na hadu da motoci suna shigowa gidan sun wuce niko na fita na fara tafiya don nasan wani hanya kawai zan dauke ya kaini unguwar mu don na gane hanyar. Na shigo gida a gajiye kamar walkiya don saurin da nakeyi suma suka shigo suna tambaya ko na dawo mommy yayi min fada sosai da na biyo kasa ban jira yan uwa ba. A part din mu na shiga na samu umma zaune tana lazumi ga tv an kunna yana aiki gaida ita nayi ta amsa da kai na shige daki na kwabe kayan da suka dameni a jiki don ban saba saka atamfa ba a jikina haka. Duk dasun bani kaya amma nafi son saka yar katin dogon riga ko yaushe ko wanduna nafi jin dadin su a jikina idan suna saka din. Wanka nayi nayi sallah ban fito fallon ba na kwanta tunanene barkatai na dinga yi har barci ya daukeni a hakan sai safe harda makara don umma na tayar dani ina kin tashi don gajiya. Sai bayan na hada muna abin karyawane daga baya aka aiko muna da abinci part din mommy da aka kawo muna an dafa don bakin da suka kwana gidan. Haka dai nake jin kaina ba dadi a ranan don bakin rai dana wayi gari dashi haka kawai na dunga jin raina yana baci ga komai dan haka ban fita ba ranan saida yamma koshi Fa,iza ce ta matsa min na fito mu tafi wurin event din da za a yi a ranan yasa na daure muka fita. Saidai muna kawowa wajen gidan daddy din matasa ne a wuri sun kai su biyar ga daddy a tsakiyan su muka fito da sauran yan matan da sukazo ta hanyar su Nabila da hauwa. Ya Abubakar da fuskan shi ke fuskantar cikin gidan ya dan tsura muna ido har muka fito aka fara gaida su na kawo wurin ina gaida da daddy jin yadda na amsa yasa wanda yaba kofan baya ya dan juyo don ganin me maganan. Saida na kadu sosai don ganin wanan fuskan da ba zan taba mantawa ba komai dadewa a idona don ranan nayi mai kallon tsab a asibitin duk da kusan shekara biyu ke