Sashe 11
Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Motar dake dauke da Alh lbrahim ta danna kai shiga gidan nasa sai lokacin ya sauke ajiyan zuciya yana gyara zaman shi. Kananan yaran yan wirin hjy karima ne a waje su biyu suna saye da dogon wandon jean blue da riguna ja riga haka take masu shiga kamar su din tagwayene don ta hada kansu tun suna kanana a nata hikimar. Murmushi ya sake ganin yaran daga kofan glass din gidan suna yan tsale tsalen a waje gida ke nan da iyali sai a lokacin yaji dan farin ciki ya sauka mai a zuciyar shi. Hankalin yaran ne ya koma wurin motan mahaifin nasu da sukai kwana biyu basu ganshi ba, yana wurin yafiya. Ya kuma dawo a yanzu a daidai lokacin da kowa nagidan bai tsamaci dawowan shi ba a ranan tsaye sukayi suna kallon motan suna jiran suga wanda zai fito daga cikin motan a lokacin. Driver ne ya fara fitowa da sauri ya zagoyo dayan gefen ya budewa ogan nasa mota a cikin mutunci a daidai lokacin yaran suka sheko suna ihun eh daddy daddy da gudun su. Hakan ya ankarar da hjy Addah dake zaune falo tana waya sai su Nabila da suma a zaunen suke suna tsabgogin su a lokacin. Nabila ta dan zabura tana fadin kamar daddy suke kira fa zai yuyu shidin nema don ba abin mamaki bane son a cikin satin nan yace zai dawo dama. Jin dan shirun da yaran sukayine yasa su daukan wasan sune kawai sukeyi a lokacin don kewan shi da suke ji a yanzu din. Kofa a katuro driver shine yake kokarin shigo da kayan shi ciki shi kuma yana bayan shi tafe da yaran kanana daya rike daya ako wani gefen shi suna dan hira. Mikewa yan matan sukayi suka hari mahaifin nasu suna mashi sannu da zuwa dukkansu su uku da yar kanwar hjy da riko a yanzu. Hjy ta mike a cikin kwaliyan da take na atampan super tana murmushi take fadin kwatsam haka babu sanarwan zuwa. Gida yayi kira banda saurin uzuri bayan hakan sannu da zuwa tayi mai a cikin ladabi duk yayan nasa na baibaiye dashi ya amsa. Zama yayi yaran suka zube kasa kamar yadda suka saba suna gaidaashi a lokacin hjy ta juya tana fadin bari a kawo abin sha bata tsaya ba ta shige ciki. Wayan ta dake hannun ta ta kalla ta dan fara neman layi a gagauce ta samu layin hjy karima data fita gidan tun dazun. Har ya katse ba,a dauka ba bata hakkura ba ta sake kira a karo na biyu kusan ya katse aka daga tare da fadin hjy Addah lafiya dai ko ? Duk inda kike ki dawo gida yanzun nan don Alh ya dawo yanzu haka yana cikin gidan nan ko ta fada a dan gagauce tana katse kiran a daidai lokacin da hjy karima ke fadin dama yau zai, , , , Munafuka wai Alh ne ya dawo ta fadawa kawayen nata da suke tare ai dama yau zai dawo ne kika fito dayan kawar ta tambaye ta. Ina fa nasan da zancen dawowan shi a yanzu din na a gaban ta fa nafito bata fada min zai dawo ba don nasan tunda munafukine shima ba zai rasa fada mata zancen dawowan shi yau din. Wai karima me kike jira da wanan matar har yanzu baki taka mata burki ba tun farko saida nace a fitar da ita kafin ki shiga kice wai ita din me wanan tsohuwar ba zata zama maki matsala ba sai dai uwarshi itace matsalan ki. Yanzu gaahi tana son ta zama maki ciwon ido tsakanin ki da mijin ki don tana munafuka wai zata kiraki tana kashe murya hjy karima kiyi sauri ki dawo duk inda kike Alh ya dawo. Mikewa tayi tana fadin ai ki barni dasu sai nayi maganin su dagashi har ita din zasu gane kuren su dan shimfida nayi masu inga iya gudun su yanzu ko nagani. Tabe baki yar dogowan daga cikin su tayi tana fadin na yaushe kuma wai an cuci na kauye yanzu ai ki mike din ki daina kwana kina sake AC kega wace ta samu wuri. Alhalin mai miji tana can rike da mijin ta sai abinda ta fada kuma ta shimfida akeyi a gidan ke kin koma yar kallo kawai. Binsu tayi da kallo don suna kara mata takaicine kawai da wanan maganan a yanzu don takai iya kuluwa da zancen yau. Boyar Allah hjy Addah kuwa tana can tana kokarin kare kariman don da tafito dauke da kayan ta mufo falon har lokacin yana zaune da yayan shi suna surutu. Tana direwa yake fadin wai ina karima ne ban ganta ba me yuyuwa tana bandakine ko tana barci bata ji shigowan ka ba sai kawai taga ya dan saki murmushi a fuskan shi. A daidai lokacin ne kuma karamar yar hjy kariman dake saman cinyan shi zaune ta sake fadin daddy I told you she went somewhare tunda safe wanka ma anty Nabilace tayi muna. A take ya kara daure fuska a hankali ya sauke yarinyar daga jikin shi kafin ya mike ya dago kai yana fadin kin gani keda ke kareta zaki koyawa yara karya, Wai ma yaushe kika fara karyane Addah ya tambaye ta yana tsure ta da idonun shi kafin ya juya yana girgiza kai. Kayi hakkuri Alh fitan ne ya kamata in bashi ba babu inda take zuwa ai tana gida baiyi magana ba sai hanyar part din shi daya dosa kawai. Ya barta tsaye kafin ta juyo tana fadin Amira waya tambaye ki sai mamin ku ta murde bakin nan mai surutu idan ta dawo. Fuska yarinyar ta tabe tana make hannu alaman kuka a lokacin daga haka hjy tabi bayan shi cike da fargaba don sanin halin shi da tayi. Ta sameshi zaune saman gado ya kwabe babban rigan shi dake saman jikin shi kamar yana tunane a lokacin. Tashigo da sallama tana fadin Alh kayi hakkuri ya dago tare da dakatar da ita yana fadin ki fita a cikin zancen nan don nafiki sanin waye karima . Ba yau ba nasan tana wanan halin da zaran na daga kafa nabar gadin nan zaman gida ya kare a gareta ita kuma ko kina dauka bansan da hakan bane wai har zaki wani tare kina rufe min. Ku daiyi hakkuri kowa da halinsa ake zama dashi inda sabo aika saba da halinta tunda yanzu an zama daya. Hada min ruwa in watsa ya umurce ta kai tsaye don haka ta juya zuwa bandakin don ta hada mai ruwan wankan. A daidai wanan lokacin kuma hjy karima ta shigo gidan su Nabila ta sama a falo ko kallon su batayi ba sai Aisha da zakiya ke fadin sannu da dawowa Anty . Ciki ciki ta amsa ta nufi part din ta kai tsaye saida ta shige Nabila taja dan guntun tsuki tana fadin Allah ya kara ai gwai kuma da har kuka tare ta ai. Ta shigo ta kallemu ta kawar da kai kune masu wani taron ta can ai kun gani yanzu wa zata zo tana budawa taje can ta hadu da daddy yau yar rainin wayau kawai. Hjy karima tana shiga dakinta ta wurgar da jakkan hannun ta da gyalen data yafa saman gado kafin takai zaune a hankali saman gadon tana tunanen abinyi. Yaran tane suka shigo dakin suna hayaniya mami kin sayo muna Sweet suna kokarin bude hand bag din ta su duba su gani. Hey Amira stop it bana hanaki wanan halin ba kina bude min jaka idan na dawo sai dayan ta biyun tace kada ki bata mami. Itace ta fadawa daddy wai kin fita tunda safe bayan mommy tace kina daki kina wanka ko kuma barci ya daukeki. Wani kallo ta watsawa yaran kafin ta kai hannu tana jan bakin yarinyar karama tana fada sai kuma taja tsuki tana fadin ita kuma munafukan wayace tace inayin wanka ? Ai daddy yayi fada yace wai ta fara karya ko yayi fushi ya wuce part nasa. Mommy ku tana ina yanzu tana part din daddy what ta fada tana mikewa yaushe ne daddy ku ya dawo ta tambayi yar babban dake magana ita kan Amira kuka ta saka. Don babban yarta tana makarantan kwana a lokacin tana jss one don ba babba bace sosai shikuma a ka,idan gidan shi makarantar kwana yara suke zuwa bai yarda da jekaka dawo ba a lokacin. Yarinyar kan bata san time ba don haka tace da uwar tun safe daddy ya dawo hakan ya harzuka karima din sosai watau tun safe ya dawo shine saida suka gama cin amanan ta yanzu zata kirata do munafunci wai tana fada mata dawowan shi a yanzu. Tamike tana fadin sai nayi maganin wanan tsohuwar banzan da bata san ta tsufa ba wallahi. Part din maigidan ta nufa da dan fushinta saidai tana zuwa dakin ta nemi fushinta ta rasa don yadda ya hade rai data shigo dakin ko sallama ya zama mai dole ya amsa ne ya amsa mata. Yana zaune saye dogon jalabiya mai laushi a jikin shi medan karmin hannu ya mike kafafun shi saman gadon dakin daya ya gyara. Alh sannu da zuwa ta fada da dan fara,an kissa a fuskan tare da fadin ashe kana hanya bamu sani ba ? Ke dakata fice ki ban wuri dan Allah banda lokacin wanan shirmen naki yanzu ya fada yana lumshe idanun shi don takaici yana maijin zafin wanan halin yan barikin na karima. Yanzu yake daya sanin kara aure da yayi yana zaune kalau da yar uwanshi wace aka gina su da tarbiya irin na islama tun a gida yanzun kuma itama tana gina mashi zuri,a da wanan dabi,an da suka koya gun iyayye da kakanni. Sai gashi kwatsam ita karima din ta shigo rayuwansu da rana tsaka tana batun tabarbare masa tarbiyan gidan shi da suka taru suka gina da yar uwarshi kuma matar shi a yanzu. Tsaye tayi tana kallon shi da mamaki a fuskanta kafin tace me kuma nayi Alh har kake korata haka a dakin ka yau ? Oh baki san kinyi komai ke nan da izinin wa kika fita daga gidan nan waya baki izinin fita a cikin gidan nan ya kara nanatawa gareta.