← Book details Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 327 OF 337

Sashe 327

Ana Dara Ga Dare Yayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

akwai mutane a gidan da dole suzo su zauna dani din. Ranan kan ba abinda ya faru bayan kunyan hakan da nake danji duk da ina kwance ba lakka a jikina hakan bai hanashi gwada rungumana ba a Darren kamar yadda malamin yace su gwada hakan a gani. Dole haka ya barni ya koma don dama zuwan banana shirin bane yazone ya dan Kwan daya sai gani gani kwana uku don Lauren daya sameni bayan Susan nasa din. Fabian morrow nake ina kallon kaina yarda na rame na nayi duhu don abinda ya faru din dani lokacin a wurin Fatima nake jin abubuwan daya faru dani lokacin naji komai daya faru dani daga bakinta bata boye min komai ba. Yanzu kunne aka kasa ashe don sun ce zasu koma gun wance ta turosu su zo gareni su bata min jin dadin aure da farin cikina da sauran sheri . Na daina ji nauyin shi da kunya ayanzu don yakan bugo waya mu dauki lokaci muna hira har yakai na dan fara sakewa dashi sosai yanzu din. Ina da wata daya da kwana biyu a garin maiduguri muna kuma zaune lafiya da kowa kullun kuma ina waya da umma har Ammar ina jin lafiyan su sai hakan yazo min da sauki don kamar muna tare a gari dayane dasu sai kewan nasu ya rage min a raina lokacin. Kwatsan ya fado muna kamar wancan zuwan saidai wanan zuwan na safe yayi muna tunda ya shigo yayi wanka bai leko falon ba. Don hakane muka samu daman yin aiyukan mu wanda nida kaina na tuka mashi tuwon amala miyan ewedo da tantakwshi sai kuma naman dana watsa kamar yadda mukeyi a can. Bayan mun gama an shirya komai wanka nafada yi na fito na gyara jikina tsab cikin wani shadda kamfala milk colour dake ta maikon sabontaka a jikina. Part din nasa na nufa a kwance na sameshi ringine ya kwanta ya dora hannu daya a goshin shi kamar me tunane jin sallama na yasa ya dan dago daga yadda yake. Yana kallona na karaso ina fadin good day sir how was your jorning saida ya dan dago tare da mikon hannun shi zuwa gareni na karasa takowa a hankali har Inda yake kwance din jawoni nayi na fada a saman jikinshi. Ya maida hannun shi ya rufe yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda sam wanan karon banji komai da nake ji ba a lokacin shima sai ji nake yana dan sake ajiyan zuciya na dan lokaci. A haka yaso wasan ya canza lokaci guda amma sai nayi saurin mikewa ina fadin your food is ready na barshi a kwance . Murmushi yayi ya bini da kallo yana fadin ya kamata by now a tausaya main hakana a barni naji dumin amaryana ko zan samu relief a zuciyana. Nima dan guntun murmushin na sake cikin kunyan shi nace ai ko yanzu kaji dimin jikin nawa me kuma ya rage a yanzu din. Ohh realy ban iya bashi amsa ba Allah ya taimakeni wayanshi ta dauki kara haka yasa na samu na fice daga dakin zuwa nawa dankin. A gaba mirrow na tsaya ina kallon kaina tare da sake ajiyan zuciya ina bawa kaina shawaran abinda zanyi a lokaci don kawai na nunawa wanda ke bina da sheri a kan auren sherin shi baicini ba. Yaji dadin abincin sosai har yana rokon aje mashi ya kakara da dare gidan hjyn shi ya tafi bayan fitan shi mun zauna da fatima a dakina muna hira tana ta kara nausar dani yadda ya dace na dinga yi idan yana gari wanda sai kallonta kawai nakeyi ni. A ranan kan komai ya wakana tsakanin mu saidai kafin hakan ya faru shi kanshi yasan abinda ya taba don bani kadai bace naji jiki gaba dayan mu kowa ya ji nasa . Abubuwane dake dukkan bangaren mu sai dai da taimakon ubangiji har aka samu kadarin abin ya karye inda a wani bangare kuma faruwan wani abu ya faru don the massage back to sender now. Badon komai ba sai dan yawan alherun mu da tsare ibada da bada sadaka da Allah ya hore munayin shi gaba dayan mu nida shi duka. Wanan yasa duk wani sherin da mugun nufi da aiken sheri na sihiri baya tasiri a kaina gashini alherina gun kananan yarane da bukata na sosai haka zan aiki yaron dake zama damu ya bi hanya yabawa mabukacin daya hadu dashi alheri ko nasaka aimun kosai da manja ko na sayi gishiri mai yawa na bayar akaiwa mabukata unguwar tallakawa .
Chapter 327 · 0% Book details