← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 289

Sashe 96

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

dana zarta akan ya'yanka ne. ina son yusif dan gurinka ya aure fajira yar gurin zakiya abdallahi ya auri sharbasiyya yar gurin hajara hk gaddafi ya auri mariya yar gurin bilkisu ita km saleema ta auri yakub dan gurin hafsatu wato dan babbar diyarta kenan. , tunda hjy harira tasoma mgn mahaifina ya dauke wuta yayi shr tare da dukar da kasan kasa yana sauraronta har ta dasa aya batare da yace mata komai ba... ganin yayi shr yaki cewa komai yasa ta murtuke fuska tare da kiran sunansa dawood da sauri ya dago a zabure idanunsa cikin nata tace ina kama mgn ka min shr ko bazakayi abinda nace bane ? yayi girgiza kansa da sauri tare da cewa hb hb hjy wannan ai ba wani abun damuwa bane dukakansu naki duk abinda kika zarta akansu ya zartu sannan km zumunci za'a sake kullawa wanda a gsky lamarin ba abinda yayi niyyar fada kenan ba. amman hk kawai ya tsinci kanshi da gaya mata hk. tayi murmushi mugunta tare da jin dadi acikin ranta yauwa dan albarka Allah yayi maka albarka maza tashi kayi tafiyarka kasoma shiri koma nace ka kirasu su yusif su dawo gida. basun kare karatun ba? tayi masa tmbyr tana tsareshi da idanu . da sauri yace eh sunkare wasu takardu suka dan tsaya jiran kammaluwarsa . dayake alokacin duka yayyena uku suna America a can suke karatu. har zai fito daga dakin ya sake komawa ya zauna inda ya tashi yace hjy.. a zabure tace uhm ina jinka ya danyi shiru yana tunanin abinda zaice. ina jinka kakirani km kayi shr. ya bude baki da kyar daman akan ita saleema ce kinsa ita yanzu take matakin farko a university shine nake son nace idan ranki bazai baci ba ita me zai hana abar zance nasu auren zuwa wani lokaci daidai ta kammala karatu. sai data tabe bakinta tana zabga masa harara kasa kasa sanan tace zuwa yaushe kenan zata kare karatu.? jikinsa na rawa yace zuwa nan da shekara 4. shi km yaron sai yayita zama baiyi aure ba har tsawon shekaru 4 kadai canza dabara ina ma laifin idan taci rabi. yace shekenan hjy babu damuwa Allah yasa mu dace adakile tace ameen. jiki a sabule mahaifina ya dawo gida bai sanarwa kowa abinda ke faruwa atsakaninsa da hjy harira ba. amman ranar kusan kwanan tsaye yayi idan ya kwanta jim kadan cikin tunani sai ya zabura ya mike yashiga zariya cikin dakin ya kai gauro ya kai mari. yarasa abinda ke masa dadi shi dai akaron kansa baya son wannan hadin ba dan baya son karfafa zumumcinsu ba. hk kawai yaji hadin bai masa km bai kwanta masa arai ba. amman babu yadda ya iya da hjy harira har washegarin da wannan tunanin ya tashi ya nufi dakin da hjy babba take kwance tmkr matacciya amman fess take bakace mara lfy bace sbd tattalin datake samu daga ya'yanta da sarakuwarta dan kusan duk karshen wata ya'yanta ke zuwa taya mamma jinya idan wannan tazo tayi wata daya zata wuce wata zo hk suke tun farkon ciwon har bisa ga yanzu da halima ce tare da mamma. ahankali ya zauna kusa daita ya kamo tafin hannu mahaifiyarsa cikin nasa yana kallonta sai kamshi take xubawa ansaka mata duguwar riga har da lalle an mata . ganin yadda har yanzu jiya iyau akan ciwonta ne ya taba masa zuciyarsa bai san sanda ya fashe da kuka ba. kuka yake har da shesheka tmkr ba babban mutun ba .sautin kukansa yasa mamma shigowa dakin ita da aunty halima. kuka yake sosai a rude suka karaso gareshi suna kuka suna mbyrsa me samu hjyr. ganin yaki yin mgn yasa sukayi kan hjy babba kowace tana kokarin kai hannuta gurin hancinta jin saukar numfashinta yasa suka sake yowa kanshi suka shiga bashi hkr suna cigaba da kuka kayi abban yusif da wannan lalura ta hjy da yarda allah hjy zatasamu sauki. tuno da abinda hjy harira ta labarta jiya ya sake sashi shiga tashin hankali. yana bukarta kulawar mahaifiyarsa ahalin dayake ciki ita km ga yadda Allah yayi daita. yana jin kmr ya tattara kan yan'uwansa su tautauna akan lamarin yana jin ana danneshi. gbdy ya tattara komai ya watsar yasoma shirin dawowar su yaya yusif.yau gidanmu a hargitse yake kasancewar su yaya yusif sun taso suna lagos dan nan jirginsu ya sauka daga nan zasu kwana a hotel washegarin su biyo jirgin safe zuwa Cotonou tsaye muke gbdy ahlin gidanmu banda mamma a airport domin tarar su yaya yasif lokacin da jirginsu ya sauka inata murna zan ga yan'uwana mafi soyuwa gareni. byn wasu mintoci mutane dake cikin jirgin suka soma fitowa daga cikinsa 1 byn 1. ahankali idanuna suka sauka aka wani kwakkwan matashi yana saukowa daga cikin jirgin kai tsaye wajen direver dake jiransa ya nufa fari ne sosaa kusan har yaso ya zartani a komai . km dogo yana sanye da royal blue thrre piesce suit sakale yake da bakar jaka kana ganinsa kaga wayayye wanda yasan duniya . ko nace wanda duniya ke damawa dashi ,yayinda da kalleshi zaka dauka dan shekara talatin da biyar ne amman azahirin gsky duk da bansan iya yawan shekarunsa ba ya zarta hkn zai iya kai shekara arbain da biyar kai tsaye yashigewarsa motar dake tsaye zaman jiran isowarsa batare da yasan wata halita a gun na kallonsa ba. motar taja ta wuce ina tsaye ina cigaba da kallon motar . yayinda zuciyata ta darsu da jin wani abu agame dashi wanda bata jin irinsa ba. abinda na dinga ji alokacin bantajin irinsa ba a tun iya tasowa kasancewarsa lamuran maza baya gabana. ba dan na rasa masoya ba hk kurin bani da ra'ayin sauraronsu. asalima kusan na tsanesu idan kinga ina dry tare da yanvuwa na ne . har sanda su yaya yusif suka iso garemu tare da rungume mahaifinmu bana cikin hankalina da natsuwata . gbdy tunanina ya tafi ne gurin matashin gayen dana kwadaitu da son cigaba da kallonsa. sanda yaya abdullah yakaraso ya rungumeni ajikinsa bansani ba. da sauri nayi frigib na sauke naunauyen ajiyar zuciya tare da dawo natsuwa ina kirkiro murmushin dole . muka nufi motocinmu zuwa gida. koda muka isa gida tuni mamma tasa an gama gyara musu part din kowannesu . tasa an shiriya dining kowa part dinsa ya nufa domin kimtsawa. amman ban da yusif wanda yace shi lallai sai yaje ga hjy babba ya ganta tukun zai iya autar da komai . ai koda yaje yagan halin datake ciki da kuka ya fito daga dakin.yana mata adduar samun sauki. washegari ban samu zuwa school ba kasancewar bani da lectures dan hk nayi zamana acikin yan'uwana muta hirar yaushe gamo .ina tsakiyarsu su km sun zagayeni kowanensu da special tsarabar dayazo min daita. har sulaiman me bina ya kulu ya dinga jin haushi wai komai komai kuka ciro sai kuce na aunty saleema ne mu ina namu? gbdy mika muka sa masa dry yaya gaddafi ne yace ka saurara man dan wutar ciki kagani ba yanzu aka bude jakar ba.to ai naga bakwa ganin kowa anan sai ita nifa kubani tawa tsarabar kafin zuciyata ta buga dry muka sakeyi sannan aka bawa kowa tashi tsarar ba. nan dai muka yini muna shan shapta alokacin mamma na gurin hjy babba. daman yawancin lokaci bata fiyye zama hira cikinmu ba yanzu tunda hjy babba ta dawo gida zaka iske tana tare daita tana karanta mata alqurni ko addu'oi .ko tsabihi acikin kunneta HILL CITY UNIVERSITY COTONOU mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE
Chapter 96 · 0% Book details