← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 289

Sashe 137

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

watsa mu cikin cell . idanuna kuri akan yan'ta'adda nan da suka min sharri, banji ba ban gani ba gashi sun kullamin kullaiya , kallonsu nake daya byn daya hawaye nabin kuncina meyasa kuka min sharri alhalin kunsa tafiyarmu ba daya ba? meyasa kuka gwamaci ku tsomani cikin rayuwarku me cike da kalubali da tashin hankali? bancanci wannan rayuwar ba, ni ban kasance me irin halinku ba ,dan girman allah na rokeku ki fitar dani cikin wannan tashin hankali mamana na can na barota kwance tana bacci idan ta farka bata gani ba zata iya rasa ranta . dan Allah kuyi hkr idan wani laifi nayi muku kuka zabi ku hukuntani ta hk. daya daga cikinsu "yace ke meya fitar dake a daidai wannan lokacin ? "wannan lokacin da aka ganmu tare dake, ba lokacin mutanen arziki bane ,lokaci ne na irinmu masu hawan dare.. sauran biyu din suka hada baki. " ki gaya mana gskyr abinda ya fito dake a wannan lokacin mu km zamu fitar dake cikin wannan maseefar . nashiga girgiza musu kai wallahi bazan iya gaya muku abinda ya fitar dani ba, domin sirrri ne wanda bazan iya gayawa kowa shi ba, ok sai kiyi hkr ki dauki kaddara kasancewa tare damu gobe bazaki sake fita a daidai wannan lokacin ba. " ke ko gaba kika ga wani zai fita daidai wannan lokacin zaki hanashi, wannan ruguntsiin dazamu shiga tare ya isheki ajiye tarihi arayuwarki. cikin kuka nace allah ya isa tsakanina daku bazan taba yafe muku ba har duniya ta nade kun cuci rayuwata . "amman ina son ku san wani abu zan tabbata ina kaiwa ubangijina kararku Allah domin yabimin hakikana da kukaci. kun zalinci ne hk kawai zaku saka rayuwata cikin kunci rayuwa.... ko kallona basu sake yi ba suka soma hira kasa kasa a tsakaninsu, a yadda nake kallonsu banga ala'mun tsoro ko firgice atattare dasu ba ,da ala'mun sun saba kwana cikin cell. ni kuwa duk inda tashin hankali yake yayi min dirar makiya kuka nake sosai da iyakacin karfina ina kiran nayiwa kaina, meyasa na jefa rayuwata cikin tsaka me wuya ... washegari da safe daya byn daya aka dinga fitowa damu zuwa wasu dakuna dabam dabam. domin yi mana tmbayoyi lokacin da akashiga dani tmbyta aka soma yi tun yaushe nake tare da ganga din barayi, zuwa yanxu sata nawa akafita tare dani ? "nasoma kuka wiwi ina cewa wallahi bansansu ba sharri suka min asalima ban taba sata ba arayuwata .. "to me ya fitar dake cikin wannan daren har muka ganku tare dasu? nayi shr na kasa amsawa sai kuka da nake sbd bansa abinda zance musu ba. ai wannan shr danayi ashe karawa kaina laifi nayi agurunsu. aiko take sai ji nayi an rufe da wani irin duka ta koina ajikina sai da suka mun lilis sannan suka barni suka cigaba da aiko min da tmbayoyin. tsayawa nayi kan gskyta , "ni ba barauniya bace km bansan yadda ake sata ba. wani sabon dukan naci kafi kace me hancina da bakina sun balle da jini kamanin fuskata yasoma sauyawa dukana suke da iyakacin karfinsu dan kawai na amsa laifina, ni km naki amsa laifina na tsaya akan ni barauniya bace km bansan barayin ba... dan hk wani police ya bada umarni a sakani cikin under ground..under ground guri ne wanda ake saka rikakkun yan fashi masu taurin kai, waje ne dake da tsananin zafi da hudu dan ko tafin hanun mutun bazai iya gani ba. haka suka daukeni babu tausayi balle imani suka turani cikin Under ground kusan awana biyu ciki wanda zuwa wannan lokacin numfashina ya dauke ,dan koda suka fito dani na suma. da wani dukan suka farfado dani sannan suka cigaba da azabtar dani wanda babu shiri dana ga azaba ta isheni na amsa laifina, akan tare mukeyin harakar fashi da makami, aka tmbyeni inda muke ajiye makaman aikinmu nace gidanmu. aranar aka nufi unguwarmu dani byn an saka min handcop hannu da kafa . tunda muka shigo cikin unguwar idanun mutane ya koma kanmu, Jama'a suka cika makil akaina gbdy police suka firfito tare da tsayar dani , nan fa mutane suka soma gane ni dan da farko babu wanda ya. ganenice sbd kunburin da fuskata da kaina yayi kallona mutane suke suna alajabi ganina cikin wannan yanayin me cike da rudani ,duk wanda ka gani cikin yanayin danake, fuskarsa cike take da matsanancin mamaki sbd kasancewata shiru shiru marason mgn da hayani ,ahankali na nuna musu gidanmu da hanuna dan bazan iya mgn ba sbd muryata ta dashe, wani sabon tashin sai da mukashiga compound dinmu da muka hankalina ya sake tashi jikina ya dinga rawa hawaye yasoma bin kuncina ta inna zan soma hada ido da mahaifiyata alokacin babu abinda yazo zuciyata kmr tausayin mahaifiyata da halin dazata tsinci kanta, da bindiga wani police ya ingiza keyata nakarasa bakin part dinmu na tsaya suka shiga buga kofar da karfin tsiya cikin hk wata makociyarmu ta fito ai tana ganin police da ganin halin danake ciki tayi saurin komawa cikin dakinta ta sake danna key, police suka cigaba da bugun kofar ,daga bayana naji sautin muryar ore tana kuka ,a she anje an gaya mata gani can police sun kamani, na juyo ahankali ina kallonta da kumburarrun idanuna jikinta na rawa tashiga tmbyta abinda ya faru nan fa police sukayi caa akanta suna aika mata da tmbyr ko tasani tace eh tasani sosai. "wani sana'a nake tace ni student ce a unilag tare da tmbyarsu laifin danayi suka ce mata aikin fashi da makami nakeyi ..... ta naga ta daura duka hannuwanta bisa kanta tana kuka da kururuwa sharri aka min ita bata san ni da wannan aikin ba. asalima ni yarinya ce da babu ruwana, sannan bana shiga shirgin mutane , tana kuka take musu bayanin halina nima kuka nake alokacin. ina kallo police suka balle kofar part dinmu suka shiga sukayi iya bincike da zasuyi amman basu ga komai ba wanda ya danganci aikin fashi. ba dan hk suka tmbyeta inda mahaifiyata taje, ta dago jajayen idanunta ta saukesu akansu "tace tashiga gari nemana dan yanzu ma tabar gidansu. " ok idan ta dawo sai ki sanar mata da abinda ke faruwa sannan suka tasa keyata zuwa waje inda sukayi parking din motarsu . "hawaye ne suka shiga gangarowa daga cikin idana bakina ya kasa furta komai sai kallon dandazon jama'ar da suka cika unguwarmu makil nake, ina cigaba da kuka. jikina a sanyaye nashiga motar police muka bar unguwar. in takaice muku har school dinmu police suka kaini zuwa ga shugaban makarata amatsayina na rikakkiyar yar fashi da makami .. kwanamu uku cikin cell ban ci ban sha dan duk abinda aka kawo bana ci yunwar ma bana jinta tashin hankali danake ciki ya girmami abinci. sannan aka fito damu lokacin idan kagani bazaka taba ganeni ba sbd dukan mutuwar da aka min kaina ya sake yin wani irin kumbura ko iya bude idanuna banayi sai da wata police tace daya daga cikin barayin ya riko hannuna tunda shi da dan sauransa . kai tsaye koto aka wuce damu . a koto ma babu wata hujja data nuna ni ba yar fashi da makami bace. " ni kaina banida effidence din da zan kare kaina agaban majisret , tunda wuya tasa na amsa laifina da kaina a tun farko, batare da wani bata lokaci ba koto ta zartar da hukunci bisa ga laifin da wasu suka aikata har dani........ mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE
Chapter 137 · 0% Book details