Sashe 200
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
masa da baccin take. ya jingina da kujerarsa shima yana lumshe idanuwansa dan shi kadai yasan yanayin dayake jin kasa akanta. kwana sukai suna tafiya acikin jirgi sai wuraren asuba suka isa Thailand daga nan suka dan huta na minti goma sannan suka dauki hanya zuwa koria atakaice sai da suka yi kwana da yini suna tafiya acikin jirgi sanan suka isa kasar koria. Cike da nutsuwa fasinjojin dake cikin VIP suka soma sauka daya bayan daya daga cikin jirgin wanda mafi yawanci yan kasuwa ne da masu fada aji a kasar Nigeria . ahankali ya waigo inda take tana bacci yana kallonta,bata motsa ba a hankali yasoma busa mata iskar bakinsa har gashin dake kwance a kyakkyawar fuskarsa gogor nata fuskar , ta bude idonta. fesss idanunta suka sauka cikin mayatattu idanunsa, idanunsu sukar sarke cikin juna batayi yunkurin dauke idanuta ba kmr yadda shima yake kallo cikin kwayar idanunta ahankali ta daga kanta daga jikinshi tana gyara zaman rolling din mayafinta daya dan zame,baice mata komai ba ya dauki jakarta ya riko hannuta cikin nasa yasoma tafiya daita tana biye dashi kmr wata hand bag dinsa. sir mahbub ne ya turo da manya manya motoci na alfarma dake mallakinsa tare da securities wadan nan ratsatsun motocin suka tsaya agabansu aka budewa AK byn mota wata hadaddiyar mota daga cikin motocin da suka zo daukarsu . tunda suka fito harbar inda motoci suke yaga yadda kamal ke bin su'ad da mayataccen kallo kmr zai ciyenta ,hkn yasa zuciya tazo masa wuya ahankali ya sanya hannunsa ya shafa sumar kanshi domin samun natsuwar zuciya yakasa shiga motar yakarasa har inda kamal yake , ya tsaya agabansa tare da zube duka hannuwansa cikin aljihun wandonsa yana kare masa kallo shi din ma kallonsa yake cikin sauri kamal ya mikawa ak hannu amman yaki bashi hannunsa hk jiki a sabule ya kawar da hannusa matso kamal ak yayi sosai yana Huci "ina bukatar ka dauke wad'an nan mayun idanun naka akan iyali if not I will suprise you.... kana ya juya cikin takunsa na isa yakarasa inda ya bar su'ad tana zare idanu. kamal yabi bynsa da kallo yana jin bugun zuciyarsa na karuwa gsky shifa yarinyar tayi masa ,gashi ta hadu iya haduwa bakaramin tafiya da eimaninsa tayi ba ai idan yasamu irinta bazai yi ganganci sakinta kmr yadda yake sakin sauran matarsa ba . take zuciyarsa ta buga da matsanacin karfi tuno da mgnr AK "ka dauke wadan nan mayun idanunnaka akan iyalina... kalmar iyali fa na nufin matarsa gsky ban yarda ba wallahi . badan tare da AK take babu wanda ya isa ya hanashi kusantarta koda kuwa ta karfin tsiya ne lasar lips dinsa yayi km duk AK na lura dashi. mutane dayawa suka zo tarbansa ciki kuwa har da musty amman bai yarda wani ya budewa matarsa mota ba shi da kansa yasa hannu ya bude mata motar yana tsaye abayanta ta shiga ta zauna daidai lokacin da kamal ya karaso daf dasu yana murmushin yake . cikin dakiyar zuciya ya shiga tare da rufe murfin motan yana bawa driva umarni yaja suka tafi kallonta yayi a fusace yana zaro ido kmr mayunwacin zaki yayi kasa kasa da muryarsa kmr zai mata mgnr azirki cikin rada yace "kalli dan iskar shigar da kikayi wanda hkn yabawa wani banza kallemeki, "duk tarin siturinki ki rasa kayan dazaki saka sai wadan banzayen kaya yaja tsaki yana kawar da fuakarsa jikinta tabi da kallo dan ta gano illar shigarta , koina ajikinta a lullube yake baya ga fuskasta da tafin hannuwanta idanunta ne suka cicciko da ruwan hawaye tare sa kawar fuskarta gefen hawaye na gangarowa ta gefen idanuta . Tun daga hanya take karewa garin kallo tare da mutane garin masu fasali da aljanu har suka isa kawataccen hotel din da zasu sauka. wanda ya amsa sunansa hotel ne wanda manya attajirai, ko kusoshin gwanati wad'anda suka ci suka koshi ne zasu iya zama cikinsa. hotel ne mai kyau da tsari,duk wanda kaga yakama hotel din to shahararen me hannu da shuni ne ,zamanka cikin hoter din tmkr kana rayuwa ne a muhalinka duk wani abun bukata akwai shi acikin wannan hadadden hotel din, daya amsa sunansa a duniya gbdy babu abinda zaka bukata ka nema ka rasa. ahankali motarsu ta tsaya cikin farfajiyar hotel din shine yasoma fitowa ya barta zaune cikin mota. shi da nustymusty ne tsaye suna mgn yayinda babban yaron sir mahbub ke kai kawo amsar musu daki kusan minti goma tsakani komai ya kammala ya budewa su'ad kofa ta fiti tafiya yasoma yi ahankali tana manne a gefensa yana rike da hannuta. ta kowani bangare ta kalla ma'aikatan hotel din ke kai kawo daga maza har mata sanye da wasu haddadun suit har suka karaso dakinsu hannuta na rike cikin nashi bai yarda yayi ganganci sakinta ba . suna shiga dakin sanyi Ac ya ratsa ilahiri jikinta Komai a gyare yake tsab a dakin. ahankali ya saki tafin hannunta zuciyarsa na harbawa har yanzu ya kasa hakurin iskanci da kamal yayi masa, yane shi da bai taba kusantar kowace mace da suna zina arayuwarsa ba byn matansa na sunnah ,bai taba tsayuwa da wata matar aure wace ba yar uwarsa bace ,shima tsayuwar baya wuce gaisuwa," ta yane wani kato zai dinga kalle masa mata har da lasar lip's wannan abu ya maseefar tsaya masa arai anya kuwa zai iya hakuri wannan iskanci wayoyinsa ya ciro gbdy ya watsar a saman gado . ma'aikatan hotel din suka biyosu da manya hakunkunansu . tsaye take har lokacin a gefesa tana dan kalle kalle a dakin kallo daya zaka mata kasan wannan shine Karonta na farko data sanya kafa zuwa wata kasa. takaicinta bai sa saurareta ba ya matsa kadan daga gefenta yayi tsaye gaban gado yana k'ok'arin sassauta tie din wuyansa,yana son rage daya daga cikin rigunan dake sanye a jikinkinsa . daya daga cikin wayoyinsa daya watsar a saman gadon ta dauki karar sauti me dadi sai da kiran ya katse bayan ya gama sassauta tie din wuyansa sannan ya dauki wayar yana dubawa,hannunshi daya riqe a kugunshi yana takawa ahankali zuwa bakin window hotel din,ya zuge labuyen yana kallon harabar hotel din , yana mgn atsanake ta dan saci kallon yanayinsa taga har lokacin fuskarsa a hade take kmr wanda aka aikowa da sakon mutuwa duk km sai taji babu dadi zuciyarta tashiga damuwa da halin dayake ciki kmr takarasa gareshi ta runguneshi tabashi hkr sannan tace ya dan saki ransa, ammam fargaba abinda zai mata ya hanata ta manna jikinta da bangon dakin tacigaba da kallonsa tana sauke jiyar zuciya .oh Allah ko ta ya ne zansoma rayuwa dagani sai shi ,ta fada hk cikin zuciyarta tana runtse idanunta Tare da dunkule hannaye. tsawon lokaci ya dauka yana waya da wanda taji yana kira sunansa da sir mahbub sannan ya katse kiran yashiga wanka cikin sauri sauri ya fito yace tashiga wanka shi km yasoma shirin fita tana tsaye tana kallonsa ya sake kaya zuwa wasu kananun kaya masu matukar kyau da daukar hankali kayan su amshi jikinsa matuka sosai suka sake fito da ainihin surar jikinsa ahankali muryarsa ta fito "ina zuwa zanje mu hadu da sir mahbub bazan dade ba zan dawo ya nufi kofar fita . "Allah ya tsare ya dawo da kai lfy .... da sauri ya dan dawo yana zaro idanu waje yana dubanta cike da mamakin jin furucinta ya lumshe mayattun idanunsa tare da furta "woww tun yanzu yarinya karki min hk man plz banason kiyi saurin yin ladaf tun yanzu ba gsky. yakarasa mgnr yana fice daga dakin ya kulleta ta baya. numfashi taja ta sauke da kyar tare da cewa masefaffe kawai , da ba'a ayi masa gwaninta , idan bakayi ba yace bakayi ba idan kayi ya gwasaleka.