Sashe 196
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
murmushi "babu wani tunani da zanyi kawai abar mgnr kar amata zance dan nasan ita bazata taba amincewa ba, nan sukayi sallama dady na sake jadda masa ya duba lamarin yayi tunani me kyau . yadda dady yayi da minister hk ammi tayi da ummun su'ad ita sam kin amincewa tayi har da kukanta ,yayinda mgnr ta tado mata da tsohon mikinta da bazata taba mancewa dashi ba, ranar tayi kuka sosai hk ma ammi suka taru sukayi ta kuka ita kanta ammi tarasa wani irin so salema kewa dan'uwanta wanda yasa ta kasa manta shi takasa ciresa aranta tsawon shekaru 23 da kenan darasuwarsa amman takasa ciresa a zuciyarta .. da kyar ammi tasamu ta rarrashita ta bar kukan amman taki amincewa da shawarar ammi . koda zance yazo kunne su'ad itama goyon baya tabayar shi kan ak tabe baki yayi ,shifa hk kawai yake jin bai son umman su'ad da shi kansa mahaifinta arayuwarsa, ganinsa sune silar haifo masa mata amatsayin shegiya ... acikin tsakanin wannan lokacin wata irin kulawa ammi take bawa su'ad ta fanin gyara jiki da kasanta ,a cewarta gara ta dinga gyara diyarta ta yadda zata samu matsayi azuciyar mijinta. yayinda shi mijin da'ake wa gyaran sbd shi, kwata kwata ya tattarata ya watsar, sha'anin gabansa kawai yake ,dana ayukansa sai shirye shiryen tafiyarsa koria. a cikin tsakankanin wannan lokacin ya dinga amsar sakonin kala kala daga zeey na ban hakuri da nuna , nadar mata akan abinda ya faru. sharrin su'ad ne da gang dinta bayin kanta bane,ita kanta taso kawo masa badurcinta gidansa. gbdy kalamanta basu taba zuciyarsa ba ballantnana yaji tausayinta asalima tsanarta yaji ya sake nunkuwa acikin zuciyarsa. dady da kansa ya sake samun AK akan zance dawowa da zeey ,amman kiri kiri ak yace masa baxai dawo daita ba ,dan ko ya dawo daita zai dinga zarginta ne ,aure km da zargi ya haramta babu yadda dady baiyi dashi ba hatta hjy kakarsa sai data saka baki amman ak yace sam idan km sun matsa masa zai dawo daita amman duk abinda yaje ya dawo kar su kuka dashi. ****** wata daya da sati daya kenan wanda yayi daidai da sakin zeey, wace zuwa lokacin kallo daya zaka mata kasan bata cikin natsuwarta da kwanciyar hankalinta tayi baki tayi wata uwar rama sbd rashin kwanciyar hankali uwa uba rashin cin abinci, wanda hkn yayi matukar dagawa mamanta hankali idan kaganta zaka dauka jinya tayi na tsawon lokaci ko km wani mummunar bala'i ne ya afka mata . ta kwallafa ranta akan soyayar AK most especial idan ta tuna irin cin kacar dayayi mata a daren farkonsu abun ya tsaya mata arai sosai , sabuwar kaunarsa ce ke fixgarta gareshi ,gbdy zaman gidan ya gundireta ,so take ta saci hanya taje ga bokanta na kan dutse ko zata samamma kanta mafuta da sausauci amman mamanta ta kasa ta tsare bata barinta fito koina , sannan ta sanya ido sosai akanta bata yarda ta fita ko nan da can wanda hkn bakaramin sake dagawa zeey hankali yayi ba, daman samun damar iskancinta na zaman gida biyu datake yi ne.. yanzu km ta dawo zaman guri daya har karya tayiwa mamanta akan tana son zuwa gidanta ta dauko wasu daga cikin kayan sakawarta, kasancewar batada kayan canzawa, amman sam mama tace ta bari kawai zata saka a dauko mata ,ko ta dinka mata dogayen riguna tasamu na canzawa kafin lokacin da zata koma dakinta, dole babu yadda ta iya hk ta hakura takame guri daya sai dai kullun cikin turawa AK text take ta inbox data what's app tana kuka tana rokonsa ya meidaita dakinta yana bude message's dinta sai dai baya bata amsa mata kullun kwana take cikin tashin hankali da tsiyaya sbd yadda take jin ak ajikinta tabbas ak nmj ne guda har da kari duk mu'amularta da akil bata taba jinsa har cikin makogaronta ba, hk ma boka ,amman shi har cikin makoshinta da dinga jinsa kmr zatayi amai duk dai cin wahala yayi mata amman taji dadinsa sosai hk take son tsayayen nmj wanda ya iya sarrafa mace akan bed ta kamkame jikinta cikin bargonta tana mammatse kafafu wayyohlly allah ,addua take son yin Allah ya meidaita gidan mijinta amman ta kasa sbd tunanita tasan zata gurin bokanta me zai sa tai addua ai Allah bazai amsawa masu gurin boka ba . ta bangaren akil ma yasan komai dangane da dukan da AK yayi mata amman bata gaya masa gskyr lamarin ba , karya tashirya masa cewar akan su'ad ne yayi mata duka har ya korota gida bata gaya masa ya saketa ba, dan tasan halinsa karshe ya bata mata plain dinta akan komawarta gidan farincikin rayuwarta . yau ma hk tai baccin wahala kmr koda yaushe tatare da kewar abdulkabir dinta ta dauko wayarta tana kallon hotunansa daya byn daya tana kuku har gari ya waye bata runtsa ba da tunanin yadda zatayi taje gurin boka na dutse take. washegari tun da sanyi safiya takira number bolaji byn ta dauka cikin mayen bacci tana cewa "ya'akayi ne kawata kira da sassafe hk ? cikin sarkewar murya zeey tace "yi hkr kawata na tasheki kina bacci... "karki damu ina jikin me faru ? " daman cewa nai ko za'a ki taimaka min kije min gurin boka na kan dutse, wlh babu yadda banyi ba amman mamana ta kasa ta tsare ta hanani fita koina gashi abubuwa sai gaba suke suna rincabewa ,kwata kwata babu cigaba har yanzu abdul bai waiwayoni ba takarasa mgnr muryarta cike da rauni. ... "bj taja numfashi da sauke naunauyen ajiyar zuciya wanda sai da zeey taji saukarsa cikin kunnuwanta sannan tace "gsky zeey kiyi hkr zan iya miki kowani irin taimako da alfarma amman banda wannan dan bazan iya zuwa miki gurin wannan bokan ba, ida dai gurin wani bokan ne wallahi zan iya zuwa miki kinga nima yanzu ina cikin condition yaron ciki gareni shi km kinsa kaida ne sai yaci mutun .. dukkaninsu sukayi shr babu wanda ya sake mgn daga karshe zeey tace "shikenan kije min wani gurin ,ni dai duk abinda za'a yi ayi kawai ni dai abdul yadawo gareni ya meidani gidansa, "yanzu idan kinje gurin wani bokan duk abinda ake da bukata kimin mgn zan miki transfer . "ok karki damu zanje miki gurin oluw'o shima aikinsa kmr yankar wuka ne sai dai gsky bai kai na kan dutse iya aiki ba.. Zeey tayi saurin cewa "shiyasa kikaga nafi son nashi aiki wlh sha yanzu magani yanzu. "idan wannan kike so sai dai ki fito da kanki inje inji cewar bj.. "shikenan kije min gurin oluw'o din. "naji ni yanzu bacci nake ji duk abinda ake ciki zakiji idan naje ta katse kiran takoma ta kwanta tacigaba da baccinta. zeey ta dade zaune rike da waya a hannunta tana saka da warwara akan lamarinta kullun kwanan duniya sai tayi mamakin yadda abdulkabir ya sauya mata da irin dukan mutuwar da yayi mata har gari ya karasa wayewa batasamun damar komawa bacci ba.. ******* cikin sauri yake shirinsa na zuwa gidan senator bankole aminin dady ne sosai da sosai tun duniya na kwance sakamakon wasu baki da zai hadasu dashi akan cigaban kasuwancinsa na gida dana kasoshin ketare. bai dauki wani lokaci ba ya fito cikin sauri sauri yashiga part din ammi yayi mata sallama har ya juya zai wuce takira sunansa abdul ya juyo tare da tsayawa yana sauraronta "bazaka tsaya kayi breakfast bane ? "bar abincin nan kawai ammi sauri nake "ok Allah ya tsare a dawo lfy. "Ameen . cikin sauri yashiga motarsa ya bar gidan. tunda yashigo dakin daza'a gabatar da meeting din gabansa ke tsananta faduwa har ya karasa shigowa cike da girmamawa dan duk cikin mutane dake zaune agurin babu sa'ansa senator yace "yauwa gashin nan yakaraso mr abdul ga gurin zama nan ya nuna masa wata empty chair wace daman zaman jiransa take, AK yasoma kokarin zama yana gyara zaman suit din dake sanye ajikinsa. makeken table ne zagaye da tarin jamar dake zaune agurin gaban kowane da ruwan nestle water sai wasu file file agaban kowanensu da abin laud din mgn wanda zai bada sound din duk wanda yayi mgn damar daza'a ji sosai . mutumin dake zaune a opposite dinsa ne ya dago ahankali idanunsa manne da farin glass,shima mutumin fari ne tasss tmkr yadda farin amminsa yake basu da wani banbaci sai dan yanayin jiki shi wannan bashi da jiki kwata kwata sannan km bashi da rama sabanin amminsa dake da kiba kadan ahankali mutumin da yasoma mgn tare da gbatar da kansa cikin harshen tsadadden turancinsa kai kace asalin baturen England ne kalmomin turanci yake fitawar ahankali game da abinda ya tarasu anan kafin daga baya ya zarce da mgn akan kasuwancinsu na yau da kullun da yadda yake bukatar gayon bayansu akan sabon kanfanin sadar waya dayake son budewa yakarasa mgnr yana lumshe ido atakaice sai daya dauki sama da awa daya yana bayani sannan yayi shr yana me bada damar idan akwai wanda zayi mgn acikinsu. kwata kwata AK ya kasa yunkura balle yace komai duk da shine mutun kusan na uku a jigon wad'anda ake jidasu a nigeria ta fanin kasuwanci amman tsananin mamaki mutumi dayake kallo agabansa yanzu yayi dalilin dayasa ya kasa cewa komai. this face is familiar to me ko km yace yasan wannan fuskar farin sani amman yadda mutumin yayi bayanin kansa , yake tamtamar kmr bashine mutumin dayasani ba tsawon lokaci . gsky yashiga comfuse tare da tarin mamaki . daya daga cikin members din dake zaune agurin ne yake bayani dalla dalla akan cigaban da wannan haduwar tasu zai haifa wanda daman sun dade suna jiran wannan ranar ya dauki lokacin ana tautaunawa kafin daga bisani ak yayi dogon bayani akan yadda zai bashi hadin kai akan cigaban company dinsa na airvioce shima km yana fatan zai bashi goyon baya akan companies na sarrafa kifin gwangwani da zaiyi akasar koria . tun daya fito daga dakin taron yashiga motarsa a guje yabar gidan duk wanda yaga irin gudun dayakeyi sai yayi mamaki hk dai Allah ya kawo shi gida lfy. ko tsayawa rufe motar bai gamayi ba yace wasiu ya rufo masa motar ya kawo masa key din