Sashe 270
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
bazan ce kwata kwata basu damu daita ba, amman wallahi basu kaini damuwa daita ba babu abinda su'ad tasani wanda ya danganci rayuwar duniya batasan komai ba saini dana koyar daita bata da exprence din komai sai wanda na koyar daita ,kai kanka sheidani akan irin rayuwar damuka gudanar a koria daita ,komai a natse take yin sa ga hakuri dayanayina koda kuwa bata so ,ya runtse mayatattun idanunsa sosai hkn ne yasa musty jin kwalla ya kawo a idanunsa yayi saurin meidawa dan kar ak ya lura da hakan. yayinda shi ak bai lura dashi ba yacigaba da magana " musty yaya zanyi da rayuwata? " nasan damuwar rashinta shi zai yi sanadin mutu... musty yayi saurin toshe masa baki "karkace haka dan Allah idan ka mutu ita kanta bazataji dadin rayuwar da babu kai acikinta, dan Allah kayi hakuri har na dawo daga tafiyar nan da zanyi kwana uku kacal zanyi na dawo duk yadda zaayi yi mu gano inda take zan bada gudumuwa ,"wannan tafiyar kai ya cancata kayita amman saboda yanayinka yasa na ajiye angoncina domin cigabanmu yakarasa mgnr cike da zolaya yana murmushi. "kai kasani da wani banzar angonci ,duk abinda zakuyi , bazai taba kai wanda nayi da matata ba, zuwan musty ya dan kwantar masa da hankali har yasamu karfin gwiwa aiwatar da wasu ayyukan dake zube agabansa.. ********* bayan kwana biyu yana zaune a cikin office dinsa, aiki yake yi but lokaci zuwa lokacin zai waigo ya kalli hotonta sannan yacigaba da abinda yake ,bayasamu kuzarin yin komai sai wani abu daya danganceta na kusa dashi ,itace karfin ikonsa a wannan lokacin. "a duk lokacin dazai d'aura kwayar idanunsa akan hotonta jinsayake tamkar rudanar taimako ce agaresa. ya tsayar da aikin dayake tare da shagala gurin kallon hotonta wanda wani lokacin suke birkita masa tunani ya dawo tamkar mahaukaci ahankali yacigaba da kallon hotonta yana tunani baya ,tare da abubuwan da zuka faru kafin ya mallaketa matsayin mata sai dai kalma daya ce tafi kowace irin kalma mahimmanci da tsaya masa cikin kwalkwarsa har yayi mata babban ma'ajiyi a k'asan zuciyarsa. bazai ta'ba manta wanda ba zai taba wannan kalmar ba "ina sonka abdulkabir .. ba yadda na iya dole na furta maka ina sonka batare da na shiryawa hkn ba, dan Allah kasoni ka aureni zan zamemaka tamkar baiwa agareka duk inda kaajiyeni zan zauna zan bi umarninka ,ka aureni kar narasa raina akanka ... ya runtse mayatattun idanunsa "ashe sha'war dayake daita ma karfin ikontace ,damar samuwarta ta gahurta ajikinsa tunda ya rasa matarsa ya nemi duk wata sha'awarsa ya rasa amman tun asafiyar yau daya farka daga mafarkinta ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi jikinsa yake bashi komai ya kusan zuwa karshe garesa, domin kuwa yasawa ransa bazai iya aikata komai da wata mace ba byn ita hawaye suka gangaro masa "su'ad na hakura zancigaba da rayuwata haka babu komai.... wayarsa ce ta katseshi daga tunanin daya lula k'ara uku yana ji sai daga can ak yasa hannu ya lalubo wayar ya d'auka ya kara a kunnen daga dayan bangaren musty dake saukowa daga matattakalar jirgi yace "ak kana ina? jin murya musty cikin yanayin farinciki shima ya tsinci kanshi ciki farinciki maramisaltuwa "ya'akayi ne musty ina office yanzu. "gobe ne yakama dawowata amman murna ya hanani zama bazan iya jin wannan abun farincikin na kasa gaya makaba .. "menene musty kasamo min inda su'ad take ne domin shi kadai abinda zanji yasanyani cikin farinciki? "tabbass nasan wanda yasan inda take yanzu hk ina airport kazo kasameni yanzu "gaya min wace kasa taje ko garin dataje tabarni ina tangaliliyar rayuwa? "kai dai kasameni yanxu a she an dade dasanin indatake akace aboye kar asanar ma ..ai baigama jin mezai fada ba ya mike a zabure yana kiran sunan musty, musty kuwa tuni ya katse kiran da gudun bala'i ak ya fito mataimakinsa ya biyosa abaya yana tambayarsa kafin kace me tuni escort dinsa da securities dinsa sun zagayeshi bai tsaya sauraronsu ba yashige mota yajata a guje suma suka biyo bayansa . A airport din ma hk ya dinga gudu gudu sauri sauri zuwa lokacin har musty ya siya musu tiket din shiga conotoun yana tsaye yana jiran karasowarsa ak na arba da musty kuwa ya kankameshi ajikisa " aboki banida kamarka , ka nuna min kai masoyi ne na hakika tun da ake wannan tashin hankali sai yanzu ak yaji hawayen farincikin sun zubo masa . musty rungumeshi a jikinsa saboda yana goge masa hawayen dayake dan baya son mutane su fuskancisu .. mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE