Sashe 226
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta dauro alwala ta fito ta shimfida katuwar sallayarta tare da feshe jikinta da turaruka masu sanyi kamshi ta tasoma sallah da niyyar kaiwa allah kukanta. daren ranar kwana ammi tayi tana kaiwa allah kukanta batare da ta runtsa ba, haka ma su'ad ba'abarta abaya gurin yiwa mijinta addua saboda tasan haka kawai mijinta bazai canza ma farat daya ba batare da wani dalili ba . kwana uku da dawowarsu ak ya addibi kowa acikin gidan da zance zeey duk wanda yazo masa sannu da zuwa zai dauko masa maganar zeey duk inda zeey tayi yana mane daita gbdy ya manta da wata su'ad a duniyarsa ballanatana rayuwar da sukayi. gani babu wanda ya kula da lamarinsa yasa ya tashi hankali kowa shi dai a meida masa da matarsa ,matarsa yake bukata hauka ya dingayi sosai . yayinda duk haukar dayake ko ajikin zeey sai ma wulakaci iri iri data dinga shuka masa su'ad kuwa tunda suka dawo bata zaman parlour ba tana daki ta kunshe kanta tana kuka da kaiwa Allah kukanta. ganin wannan haukar da ak yakeyi tayi yawa akan zeey yasa dady tattara kan jamar gidan har hjy kakar ak. zaune suke gbdy'su acikin parlour'n inda ak ya zabga uwar tagumi yana fuskatar zeey ko kifta ido bayason yi ita kuma sai wani shan kamshi take tana yatsina . su'ad kuwa tsurawa mijinta idanu tayi tana kallonsa tunda suka dawo bata sanya shi cikin idanunta ba gbdy duk sai taga kmr ya d'an fada . dady ne yasoma magana kamar haka "na tattara dukanmu anan ne domin samun maslaha da cigabanmu, abdulkabir ya nemi a meida matarsa dakinta sucigaba da rayuwa byn dagon fushin da ya d'auka daita, dady yayi shiru kana ya numfasa sannan ya meida kallonsa ga ak yacigaba da magana "wannan shine damarka ta karshen agurina dazaka wulakanta matanka ka dawo na saka bakina ciki , ga matarka nan zaune kaje yanzu agabanmu kabata hkr idan ta hakura taji zata iya koma gidanka fine mun yan addua ne, idan kuma tace bazata koma ba babu me takurata . tunda dady yasoma mgn jikin su'ad ke rawa har sanda ya dasa aya jikinta bai bar rawa ba. ai ak nagama jin haka ya miki zumbur jikinsa na kirma ya nufi inda zeey ke zaune tana ciccin magani ya zauna kusa daita yana bata hakuri tmkr wani zararre . "bazan koma gidanka ba abdulkabir naga ma rayuwar aure da kai ,ka wukantani ka tozartani akan laifin da bani ce sanadi ba tursasani akayi dan h ... jikinsa na rawa ya kai hannunsa ya toshe bakinta "plx my zeey dont say anything again i Realixe my mistake's, nasani ba halinki bane wacan yarinyar ce tajawo komai amman kiyi hkr ki dawo gareni zan rikeki amana, idan baki dawo ba zan rasa raina da komai na, dan Allah dady hjy ammi ku taimaka kusaka baki zeey ta dawo kar na mutu yakarasa mgnr yana jifan su'ad da mugun kallo . A razane su'ad ta Mike tsaye a zaunen datake jikinta na sake daukar kirma tasoma daga Zara zaran yatsun kafafunta ta isa inda yake tsaye tana dubansa cike da tausayawa hawayen damuwa da tashin hankali na tsiyayowa bisa kuncita . Tabbas hasashenta na son yazama gaske akwai abinda ke faruwa da mijinta ,koma tace abun ya faru yagama. abdulkabir Dinta ne zaune yarasa sukuni yake rokon zeey takoma gidansa idan bata koma ba zai iya rasa rayuwarsa da komai nasa " Allah ta furta cikin zuciyarta kirjinta na wani zugin azabar radadi ita ba bakincikin dawo war zeey gidansa take ba amman gadarar da xeey din ke nunawa Ahalin yanzu shine damuwarta kuma shine abinda yafi daga mata hankali . Hankalimta bai tashi ba sai data taji zeey na sake maimaita kalmar bazan koma gidanka ba abdulkabir sai dai idan zaka durkusa agaban iyayenmu ka rokesu su meida makani sannan ka dawo gareni ka rokoni ta tsigar data dace sannan zan koma gidanka mucigaba da rayuwar aure . Fadar hakan ke da wuya AK ya isa gaban dady da ammi dake zaune kujera guda ya durkusa har kasa " ammi dady dan girman Allah kuyi hakuri nayi nadama abinda nayi ku yafemin kubawa zeey hakuri ta dawo gareni idan narasa zan mutu . Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kalmar da ammi take furtawa kennan acikin xuciyarta tana sake mai maitawa ahankali ta runtse idanunta batare datace komai ba tana karato duk adduar datazo bakinta wannan wani irin tashin hankali ne ? "wai meke shirin faruwa da gudan jinita hakika wannan ba abdulkabir dinta bane, abdulkabir dinta me dakakkiyar zuciya ne da izza da nuna isa ,shine yanzu durk'ushen yana marairaicewa akan Zainab da babu yadda bazuyi dashi ba ya dawo daita ya lashe takobin bashi ba sake rayuwa daita har abada. Ita kuwa suad koma tayi ta jingina da bangon parlour'n tana dubansu ta dawo wata irin halitta gbdy ta dawo tamkar mutun mutumi atsaye . Wai meke shirin faruwa daita ne? ahankali ammi ta bude idanunta dake runtse ta daurasu akan suad batare da kalli inda ak yake durkushe agabansu yana faman rokonsu . Karema mata kallo tayi cike da tsusayawa da mamakin wulakacin da abinda abdul yayiwa suad din a yanzu , babu abinda ya kai wannan zamowa wulakanci da tozarci mijinka ya dinga nuna son wata agabanka. kowa dake zaune agurin da abinda yake ayyanawa aransa game da *sarkakkiya* sabon novel dina me zuwa. suna cikin haka ak ya mike zumbur tmkr wanda aka tsinkara ya isa gaban zeey su'ad batasan lokacin data isa garesa ba dan tasan durkusawa zaiyi agabanta da zumar bata hakuri yana kokarin durkusawa kmr yadda tayi tinani ta kai hannuta garesa ta dafa kafarsa ya juyo a fusace sbd jin wani kololon bakincikin tindaga tafin kafarsa har zuwa cikin zuciyarsa sakamakon jin hannuta ajikinsa hakan yasa ya buge hannunta cikin zafin nama yana hararata. a matukar harzuke yace "idan kika sake yunkurin kai hannunki jikina zan yi pata pata da namanki dole ne nace banson ki sake tabani ke bana ko kaunar sake sanyaki cikin idanuna ki shafamin lafiya bana kaunar sake ganinki,a yanzu komai kikayi bakya birgeni duk abinda kikayi ahalin yanzu babu abinda yake karamun illa tsanarki dake ruruwa acikin zuciyata ,plz su'adullahi kishafa min lafiya da wannan nacin naki na tsanake na tsanake on-expecting taji dauuuuu ta dauke shi da wani gigitacen Mari . Zaro idanunsa yayi wanda sai lokacin ya kalli kwayar idanunta dake cike da ruwan hawaye bashi da aka mara ba hatta jama'ar dake zaune agurin sai da suke mike tsaye suna duban su'ad. kallonta yacigaba dayi cike da sabon tsanarta dayake fadan yana mata a halun yanzu, ganin yadda yake kollonta yasa jikinta na rawa tayi kokarin sanya kwayar idanunta cikin nasa tana me fashewa da wani irin marayar kuku tana kallon tafin hannuta data mareshi dashi daga karshe tayi saurin durkushewa kasa agabansa tana yarfe hannuta tana jin nadamar abinda ta aikata yau itace ta mari mijin aurenta bata ta'ba tinani zuwan wannan ranar ba jikinta na rawa ta kamo kafafunsa cikin rawar murya tasoma magana "kayi hakuri mijina koda tsanar da kake mun zata zamo ajalina dan Allah ka kalleni ka sake furta min kalmar so ,zuciyar su'ad baxata iya daukar wannan tashin hankalin ba, bance karka dawo da zeey ba amman dan girman Allah ka fuskancin halin damuwar da zanshiga . Janye kafafunsa yayi yana mata wani mugun kallo" har abada bazaki sake samun wannan kalmar daga bakin abdulkabir ba ,marina da kikayi zaki san kin mareni wallahi sai kinyi nadamar marin da kika min yakarasa ya isa gaban zeey data cika tayi taff tana kokarin fashewa har ya karyar gwiwarsa xuwa kasa ammi tace kul! "Kar naji kar nagani ka durkusa min ka durkusawa wata, bance karka meida zeey gidanka ba matsawar kana bukatar hakan sabo da itama kmr ya' ce agurina amman batun durkusu shine bazan dauka ba .... Ammi takara mgnr tana takaicin ak cikin ranta Cike da sanyi jiki ya sake xuwa gurin ammi ya riko hannuta "karki ce haka ammi meye acikin dan na durkusuwa zainab matsawar zata dawo gareni zan iya durkusuwa agabanta na kuma roketa .. A fusace ammi ta fixge hannuta "tabbas ka haukace ,haukar da zainab takira dashi ta tabbata domin kuwa baka cikin hankalinka da natsuwarka gaban zeey yabada rassss sakamakon jin furucin ammi. ammi tacigaba da mgn "wallahi nasan da kana cikin hankalinka abdul bazaka taba yunkurin durkusuwa kowace irin mace bace aduniya bayan ni dana kawoka duniya amman duk abinda mutun yayi shi da Allah. hjy kaka ta amshe zance da cewa " me kike nufi da wannan maganar taki baraka ? "Kina nufin zainab tayi masa wani abu ne ya dawo haka ko me maganarki take nufi ? Ammi tayi shiru taki cewa komai sai girgiza kafa take tana kallon su'ad dake wani irin kuka . "Ince a gidan wani irin hauka ne abdul bai yi akan su'ad ba amman ko sau daya naji kince anyi masa wani abu oho ashe fa ita diyar d'anuwanki ce . "hjy ki fahimci zance na... "Dakata baraka babu abinda zan fahimta kai abdul kayi duk abinda zakayi ka dawo da matarka matukar hakan shine kwanciyar hankalinka . Cikin kuka su'ad takaraso gurin tace "ammi ki duba da kyau wallahi abdul baya cikin hankalinsa wani abu na damun tininsa, watannin baya da suka gabata babu yadda banyi dashi ba akan zance meida zeey yace sam bazai meidata ba sai km yanxu da rana saka ya dawo yana hauka akanta takarasa tana 'barkewa da sabon kuka me ta'ba zuciya .. ran hjy kaka ya sake 'baci sosai tace "Kinga yakike da suna ma ni manta su'ad ko me sai fa kiyi hakuri ,km tun farko kinsa bake kadai abdulkabir yake so ba, asalima zainab ce burin ransa kika yi wa rayuwarsu katsalandan dan haka addua zakayi akan zamanku dan zama da kishiya dole ,ni nasan komawar jikata gidansa baza'a samu wata matsala ba tunda tana da hakuri da hangen nesa muradinmu idan ta koma ku zauna lfy da junanku shine magana amman wannan kukan naki bazai hana komai . Jin maganganun hjy yabashi kwarin gwiwar tashi ya nufi inda zeey take zaune batare daya Kalli su'ad ,Yana gama isa ya kamo