Sashe 121
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
AYSHA A BAGUDO dedicated to hauwa A usman allah's messenger saw said purication is haif of faith page 45 lokacin da aka kaini hospital rai hannun Allah sbd babu wani ala'mun numfashin atare dani. gadan gadan likitoci suka amsheni sukashiga aikinsu akaina ,domin kokarin dawo da numfashina . amman duk iyakacin kokarinsu naganin numfashina ya dawo gangar jikina ya gagara samuwa . yayinda ilahirin hospital din ya cika makil da dandazon dangina dana abokan ango. kowa kagani agurin yayi jugun tare da zabga tagumi. shi kansa ango hankalinsa a matukar tashe yake, so yake yasan halin da nake . mamma kuwa tafi kowa shiga tashin hankali kuka take wiwi tmkr zata mutu tana daura dukkan laifin kan mahaifina da danginsa fada take zasu kashe min yarinya akan ra'ayinsu na banza. likitoci kuwa sai kai kawo suke akaina abu kmr wasa sai danayi kwana da yini ban motsa ba yayinda likitoci ke kaina, daga karshe suka yanke shawara'r sakani cikin scanner domin asa a wani hali nake ciki ina raye ne ko na mutu.. byn awa uku da sakani cikin scanner aka fito dani . aka nufi dakin majinyata dani aka kwantar aka daura min drip sakamakon ganowa da likitoci suka ina raye numfashina yayi sezin . sai dana kusan sati daya kwance bansn a wani hali nake ciki ba ,sannan ban san hidimar da dangina da yan'uwana keyi akaina ba. lokacin dana farka babu abinda ke fitowa daga cikin bakina sai yakub ka sakeni ni ba matarka ba.. ce, kai ba mijina bane ...ni taufeek nake so km shi zan aura banasonka ka sake . hk na dinga sambatu ina fisge fisge sannan na lumshe idanuna ina jan numfashi da kyar wasu zafafan hawaye na zubo wa saman kuncina . lokacin da doctor yashigo dubani saurin karasowa yayi lokacin dayaga halin danake ciki yadda jikina ke kirrma zafafan hawaye na gangarowa ta gefen idanuna wanda ya jika pillow da kaina ke ajiye akai . ina jin motsin shigowa dakin na zabura na mike ina kasakeni yakub wallahi bazan zauna da kai ba.. sai km naga bashi bane likita ne dan hk na koma na kwanta ina sambatu allura bacci yayi min wanda take bacci yayi nasarar daukata amman har lokacin jikina bai bar rawa ba. Bayan alluran baccin da akamin ya gama aikinsa ya sakeni a zabure na sake farkawa ina ihun kuka ina sambatu ina cewa yakub kasake ni ka sakeni wallahi bana sonka kasakeni kasake bana sonka yakub wallahi taufeek nake so ba kai ba ina furta hk ina kuka kmr raina zai fita sai faman fisge fisge nakeyi a hankali mamma ta matso kusa dani takai hannunta kaina ta dafa tana shafawa tare da kama hannuna tana murzawa tace salimat kinatsu kidawo cikin haiyacinki wayace miki andaura miki auren da yakub ai ..ba'a daura ba... salimat tace mamma da bakinshi fa naji yana fada cewan andaura a'a salimat zeje dai daurin aure ne amma sam ba'akaiga daurawa ba. Kinjiko kisamu natsuwa dan Allah kiyita furta kalmar innalillahi zaki samu natsuwa zuciya kuma zakiga komai yazo miki da tsauki. kwana biyu tsakani aka sallameni. tundaga cikin mota da zamu koma gida naga yanayin iyayena da yayyena ya sauya ,sai kallo na kawai suke fuskarsu cike da mamaki ni km ko ajikina domin atunanina kallon tausayawa 'su kemin shi kuwa babana banda tsuma babu abinda yake na lura kmr ma Allah Allah yake mu isa gida. muna isa gida muka yada zango a parlour babana kasancewar akwai mutane zugu da sukaxo biki basu rigada sun koma ba. muna shiga babana ya finci koni ya maka da kujera yana huci kafin na mike naji yace kin cuceni salema kin gurbata min xuriya.kin min tabon da har in mutu bazan taba mantawa dashi ba ke kadai da allah yabani mace amman kin zamemin masifa ni dawood diyata ke dauke da cik... jire ne ko kuwa buguwar zuciya ne tasameni daga tsaye sbd ji nayi kaina tare da gangar jikina suna juyawa gabadaya idanuwana sun rufe bani ganin komai da lalube nasamu na isa jikin bango na jigina jikina ina kallon iyayena da yan'uwana a matukar tsorace ahankali na sulale nayi zaman yan bori wato na mimike kafafuna na waresu tmkr yadda kananun yara kanyi. can kmr daga sama naji ana furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun sai kawai naji nima nakama kalma nashiga furtata ina maimaitawa bude idanuna nayi ahankali tmkr na masu bacci naga mahaifina tsaye yana sake furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shida mahaifiyata rike da sakamakon likita a hannunsa yana sake duba farar takarda .. ni kaina kalmar nacigaba da furtawa daga inda nake sbd halin tashin hankali danake ciki . take naji numfashina na kokarin daukewa adaidai lokacin danake jin sautin muryar babana ciki kuka cikin agidan.... ni dawood cikin shege acikin gidana har na tsawon wata uku..? yakarasa mgnr tare da yowa kaina gadan gadan yana huci ubawan yayi miki ciki shege? yayi min tmbyr yana daukeni da wani gigitaccen mari ... mamma takaraso garesa cikin yanayi na rudani da tashin hankali ta rike hannunsa kabari abi komai ahankali musan wanda yayi mata cikin. ya fixge hannunsa yana nunata da yatsansa ala'mun ta kiyeyesa. ni km na dan yi murmushin da bansa sanda yafito ya bayyana akan fuskata ba sbd na tabbatar matsawar ciki gareni babu tantama na taufeek ne, cikin karfin hali naji mgnr ta fito daga cikin bakina nace baba matsawar likita ya tabbatar da ciki gareni to cikin taufeek ne ..gbdy daga mamma har baba atare suka zaro idanu waje.. kenan da gaske ciki ne dake? inji cewar yayyye wadan suka hada baki gurin furta hk . batare da wani tsoro ko fargaba ba na daga musu kaina ala'mun eh nan fa babana yashiga dukana takoina tare da allah wadai dani dukana yake yana dukan cikina da iyakacin karfinsa. " su yaya yusif suka rikesa suna kuka suna bashi hk.. yana cikin dukana mamma ta zube kasa suka barshi yacigaba da dukana sukayi kan mamma suka shiga jijigata gaddafi ne ya nufi fridge ya dauko ruwa aka shafa mata ta farfado tana sauke numfashin tare da cewa ya kasheta ko..? ni kuwa har lokacin banana bai bar dukana ba sai da yayi min jina jina tare da canza min halita sannan yaje har dakina ya dauko akwatin kayana ya dinga watsa min a harabar gidanmu zo ki bar min gidana.. wallah bazan barki ki haifamin "dan "shege acikin gidana ba . "mamma wace tagama farfadowa ta mike tsaye tana kirrma karka min hk dawood karka kora min yarinya duniya karkayi sanadiyar rugujewar rayuwarta. ki min shr ai duk da hadin bakinki yarinya tasoma lallacewa wallahi kinji na ratsen miki saleema baza sake kara second 1 acikin gidana ba sai tabarshi . ke km idan kikayi kuskuren sake cewa komai abakacin aurenki wani irin firgitaccen ihu nasaka tare da daura hannuwansa duka bisa kaina wayyohlly Allah nakaraso inda mamma take tsaye kmr andasata tana xubda hawaye. nace dan girman allah mamma karkice komai kiyi hkr kiyi shr banason tawa matsalar ta shafeki yanxu zan bar gidan kmr yadda baba yace kimin addua acikin zuciyarki ke uwace nasan duk inda nake adduarki zatayi tasiri gareni.. kimin addua mamma ina bukatar adduaki ko zanga daidai arayuwata ina cikin mgn mahaifina yakaraso a zuciye yasoma jana da akwatin kayana daga yau ni ba ubanki bane.... " bana bukatar sake ganin fuskarki arayuwata kije duk inda zaki a fadin duniya nan amman ina tabbatar miki duk abinda kikayi sai aminki ninkinsa yana kokarin ingizani waje yayyena sukayi sautin isa gabansa suna bashi hakuri atsawace yace wallahi kuka sake mgn zan tsine muku take kowanensu yaja baya suna kuka turani waje yayi tare da kullo get din gidan sannan ya juyo yana fuskatar mamma da yan'uwana duk wanda ya nemi inda salema take ko taimaka mata arayuwa ban yafe ba... ..sannan ya juya yana layi ya nufi dakinsa. ina daga waje ina jin sautin kukan mahaifiyata da yan'uwana.. amman bani da damar shiga cikin gidan natsaya ina kallon gidan da'aka haifeni nataso acikinsa cikin farinciki amman yau gashi zanbarshi ba dan ina so ba. na dauki jakata ina kuka nasoma kokarin daga kafafuna abu na farko dayasoma zuwa cikin zuciyata ina zanga taufeek ...tafiya nayi sosai acikin wannan dare kusan ta awa daya kafin naxo ainihin inda zan samu mota sbd daga uguwarmu zuwa tashar mota akwai nisa sosai . da kyar nakaraso tashar tapa juga juga abinka da ba'a saba tafiyar wahala ba. koda naxo tasha babu mota me zuwa Nigeria duk motocin sun gama tashi . "idan ma akwai motar da wani kudi zan shiga motar ..? dan hk ahankali nasamu wani dan dakali na zauna ina kuka tare da kalle kalle yan tsirarun mutane dake kai kawo a bakin titin ina nan zaune sai ga wasu custom su biyu kowanensu sanye da uniform sun karaso jikin wata mota crv suna zantawa da ala'mun dayan dake rike da farar leda ne yarako abokinsa ko dan'wa. acikin tautaunawarsu ne naji shi dayan yace Nigeria zashi ina jin hk nayi saurin mikewa jikina na rawa amman na kasa isa inda suke har dayan ya juya yayi tafiyarsa shi kuwa dayan ya juyo zai bude murfin motarsa muka hada ido dashi. ya bar abinda zaiyi yakaraso gareni tare da cewa yan mmata ina zuwa ne? da sauri nace Nigeria, Nigeria ya sake maimaita sannan yace ok nima can na nufa ko zan iya rage miki hanya? nayi saurin cewa eh ok muje ya bude min gaban mota nashiga na zauna shima yazagaya yashiga ya zauna ya tayar muka bar gurin. tafiyar awa 3 ce takawomu *yanoba* hk nagani a rubuce sannan ya juyo ya tmbyeni wani unguwa zani gamu a nigeria nan fa nasoma duru duru da idanu nace ai bansa unguwar dazani ba ka taimakeni da gurin bacci har zuwa gobe da safe . yayi shr yana kallona duk da yanayina bai nuna masa ko ni yar hannu bace .. ok badamuwa zan taimakamiki dan hk kai tsaye gidansa ya kaini inda ya saukeni adakinsa. yace naje nayi wanka nace a'a sbd ban damu da nayi wanka ba dan bashine agabana ba. ina zaune yagama duk abinda zaiyi yace sake cewa naje nayi wanka