Sashe 234
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH YA WAHAB THE GIVER OF ALL THING page 75 .......batare da 'bata lokacin ba aka d'auki su'ad zuwa asibintin dr saif ,koda suka iso daita gbdy batasan inda kanta yake ba Spcial room ya bari aka kwantar daita sannan ya daura mata drip dan har lokacin bacci take bata farfado ba . kusa daita yakarasa tare da janyo kujera ya zauna ya rungume hannuwansa duka akirji ya zuba mata ido sosai tamkar ranar ya fara ganinta bacci take hankali kwance sai dai kallo daya zaka mata kasan bata cikin natsuwarta, haka ya tasa gaba ya dinga kallonta ya kasa barinta yaje yayi abinda shine makasudin kawota. kallonta yacigaba dayi saboda su'ad wata irin halitta ce agurinsa da bai ta'ba ganin irinta ba. ba dan kyawunta ba daman skin dinta dole ya kasancewar hk kodan yanayin gidan data fito . sabon gwaje gwaje yayi mata ya sake d'iban jininta wannan karon bashi yayi ba dan kar abun ya dinga maza gizo, hatta scaning sai daya sa aka mata. tsakanin awa daya komai yayi ready a saman mekeken table dinsa. gabansa ammi ce zaune gefenta kuma eiman ce tsaye umman su'ad kuwa tana waje dan gujewa kunnuwanta abinda zai d'aga mata hankali. ahankali doctor saif ya dago fuskarsa tare da zare farin glass din dake manne da idanunsa byn yagama duba sakamakonta ya ajiye agefe tare da xuba tagumi da hannunsa daya ya tsurawa ammi ido na tsawon minti goma wanda zuwa lokacin gbdy hankalin ammi yagama tashi. Tsawon lokaci ya d'auka yana duban ammi itama shi take kallo atsorace, yarasa meke damun zuciyarsa akan yarinyar jikinsa yayi mugu mugun sanyi a inda yake zaune gumi ne ke karyo masa takoina ajikinsa shifa yana sonta koda dama cikin jikinta gbdy zai iya aurenta koda kuwa cikin jikinta zai kasancen shrge ne . wani irin kirma jikinsa keyi ,a marairaice yasoma magana cikin sanyin murya "ammi meye matsayin su'ad agurinki ? bakinta na rawa tace "diyata ce halak malak sbd d'anuwana da muke uwa daya uba daya ne mahaifinta "meke damunta doctor idan akwai wani abu dan Allah kasanar min hankalinmu gabadaya a tashe yake. ya lura su'ad din tamkar rayuwarta ce dama ahlin gidan gbdy . ya numfasa sannan yace "ki kwantar da hankalinki ammi bawani abu bane sakamakonta ne ya tabbatar mana da tana dauke da ciki har na tsawon wata uku da yan kwanaki yakarasa mgnr yana jin gabansa na tsananta faduwa ya tsaya yaga reaction dinsu amman sai yaga sabanin hk .. ..... "alhamdullahi alhamdullahi !! abinda ammi ke fada kenan tana fafad'a murmushinta tana sake maimaita alhamdullahi, itama eiman farinciki take tare da rungumo ammi suka 'kwakume juna suna murna wanda hakan yasa numfashin dr saif kokarin barin gangar jikinsa ahanakali kuma kirjinsa yasoma bugawa eiman ta Kalli ammi tana murmushin jin dadi "ammi yaya zai yi d'an kansa bari naje nayiwa dady albashir ta nufi kofar fita da sauri. gyra zamansa yayi tare cewa "yanaga Duk kuna murna ko daman tana da aure ne? ammi tashiga daga masa kai sannan tace"tana da aure su'ad matar d'ana ce dana haifa. a zabure yace "kikace me ? "matar d'ana ce dana haifa " "to ina shi mijin nata yake da duk wannan doguwar jinyar datayi bangansa ba ko sun rabu ne? ya fadi hk yana adduar Allah yasa sun rabu ne a zuciyarsa. "a'a suna tare ya tafi wani aiki ne zuwa koria amman zuwa nest week muke sa ran dawowarsa ta fada masa haka ne dan rufa sirrin gidan d'anta . sam bai yarda da zance ammi ba amman Bai san me zai sake cewa daita ba ,dan hk yayi shr tare da komawa ya jingina bayansa da jikin kujera dayake zaune ,ya runtse idanunsa yana jujjuyawa shi kad'ai yasan halin daya tsinci kanshi lokacin da ammi tace masa matar aure ce. ahankali ammi takira sunansa "d'ana saifullahi meye damuwarka naga kashiga damuwa da jin su'ad na da aure ? Bude idanunsa yayi ya saukesu akan fuskar ammi sai dataji tsoro sbd ganin yadda idanunsa suka dawo tmkr garwashin wuta muryarsa a raunane yace "bazan boye miki ba ammi sbd ina jinki tmkr uwa agarene ,"ammi na kamu da mutuwar son su'ad acikin kankanin lokaci wanda bansa dalilin dayasa Allah ya d'aura min soyayyarta haka ba ,amman babu komai zan bawa xuciyata hakuri yakarasa maganar yana goge idanunsa da yatsu biyu. jikin ammi yayi mugun sanyi sbd yabata tausayi muryata a sanyaye tace "almarin Allah kenan sannan kayi tinani dakace zaka sanyawa zuciyarka hakuri ,ina maka fatan Allah yabaka mace wace tafita zama alkhari agareka "ameen nagode sosai . ammi tacigaba da mgn "ala hakikanin gsky da kace su'ad sun rabu da mijinta wallahi zan iya tsaya maka ka aureta ba dan komai ba sai dan kaima kana da nagartar daza'a baka aure duk da bansan tushenka ba. ,"da kuma ba'ayiwa eiman miji ba dana tsaya anbaka ita dr saif yayi murmushin karfin hali wanda yafi kuka ciwo kana yace "na gode kwarai da kaunarki gareni allah yabar girma . Ammi ta amsa da "Ameen Allah yayi muku albarka yasa kayita samun nasara asha'anin aikin ka, sannan ta yunkura ta mike cike da tausaya masa gefe daya kuma tana cike da murna samun jikan dazatayi ta bar office din. ta barshi zaune tamkar wanda ya mutu alhalin yana raye , fitarsu ke wuya ya zabura ya mike yashiga buga table din gabansa yana zagaye office yana jin kamar ya d'aura hannunsa duk a bisa kai ya rusa ihu ne, yanzu shi yaya zaiyi da tarin soyayyarta? Hakuri. Zuciyarsa tabashi amsa da haka . bashi yasamu natsuwar zuciya ba har sai daya dangana da gida addua yayi tayi a game da lamarin soyayyarsa da su'ad, ya dawo asibiti guraren 4 lokacin har ta tashi ammi ta taimakamata tayi wanka tana kwanciya yashigo ya jima tsaye jikin kofar dakin yana kallonta gbdy hankalinsa kacukan ya daurasa ne akanta bai taganin halitar data tafi da zuciyarsa da hankalinsa kmr ta ba, har yagama tsayuwarsa bata juyo ba duk da taji ajikinta shine yashigo dakin. Kwananta daya a hospital aka sallamota suka dawo gida ,kmr kar labarin cikin ya bayyana shikenan laulayi ya tashi zangazanga komai taci sai ta amayar dashi ga xubar da miyo gbdy lokaci daya ta sake ramewa ,dan haka kusan duk bayan kwana biyu sai tasha drip. lokacin da musty yasamu labari cikin su'ad yayi murna sosai yace "kar agayawa ak shine zai masa albishi sbd yasan yadda ya matsu su'ad bata haifa masa bby ba, amman abun mamaki sanda yake gaya masa ko gezo baiyi ba ballantana ya nuna murnarsa akan samun katuwar daya yi. ,anan musty ya dasa ayar tmby akan lamarin ak tabbas akwai abinda ke faruwa da amininsa . Ana ta xuwa gida duba lafiyar suad amman banda uban cikin ,hidama sosai musty yake daita da cikin jikinta dan wani lokacin idan su'ad tace zataci abu shi ammi take kira haka zai bar ayyukansa yaje da kansa ya siyo ya kawo . tunda mijinta ya juya mata baya duk dare sai tayi kuka rashinsa musamman idan tazo gurin kwanciya gara ma da rana idan tana tare da su ammi da suke d'ebe mata kewa, hakan ke sa taji damuwarta ta kau amman muddin zata kasance ita daya dole tinaninsa yazo ya addabi rayuwata kusan yanzu tafi damuwa dashi akan da, batasani ba kodan tana dauke da cikinsa ne ganin tinansa na neman taba lafiyarta yasa ta mike taje tayi alwala tasoma kaiwa allah kukanta . ****** ak zaune yake bisa rocg a babban parlour'nsa kasancewar week end ne babu aiki kafarsa daya a Mike dayar kuma a lankwashe ya dora system kan cinyarsa yana operating suna hira da musty inda yace "aboki yakamata kaje ka duba lafiyar matarka ko babu komai taci darajar cikin jikinta, ka duba har tagama kwanciya a hospital baka leka kaga yanayin jikinta ba yanzu kuma ga laulayin ciki yasakata gaba still bakazo ka duba lafiyarta ba ,"da me kake son taji da wulakancinka ko da halin datake ciki ? kazo ka tare guri daya.. "ya tare guri daya ina ruwanka munafukin Allah ta'ala ...on expecting suka jiyo sautin muryar zeey bisa kansu "ok ashe fa kaima kana cikin yan bakinciki da basu son gani na dawo gidana to ta Allah ba taku, zama kuma daram agidan Abdulkabir adam sai dai ku mutu makiyya kawai .. "my zeey dan Allah atsawace "tace kamin shiru nasaka bakinka ko nace kayi magana ? take yayi shiru ya sunkuyar da kansa yacigaba da aikinsa. "kai km malam katashi ka wuce ,zance zuwa wani dubuya bazashi ba idan har sai yazo dubiya zata warke sai dai ta mutu dan, idan kuma turo akayi kaje kace injini nace bazai zo ba, oya oya malam tashi ka kama gabanka " gargade na nakashe karka sake zuwa gidanmu dan bama bukatar ganinka . musty dake zaune ya dawo tamkar mutun mutumi a agurin yana kallon ak yana kallon zeey dake tsaye tana jijiga sannan ya meida hankalinsa kan ak yana son yaji me zaice amman sai yaga yayi musu burus . "my life ak ya dago d'a sauri yana kallonta "kace masa ya tashi ya wuce yanzu. Muryasa na rawa yace"musty oya zoka wuce dan allah kada kadata min hankali ina zaman zamana da matata lafiya zaka hadamu . da Allah karka sake zuwa gidana kmr yadda tace duk abinda yataso ma hadu a office, zance yarinyar nan kuma karka sake min shi saboda na tsananeta bana so ganinta arayuwata har waje ak ya kai musty yana jadda masa kar ya sake zuwa gidansa. Gudu kawai musty yake akan titi hankalinsa a tashe daga gidan ak kai tsaye gidan ammi ya wuce nan yashiga korawo ammi duk abinda ya faru "ammi ina ganin fa yarinyar nan bata bar ak haka ba akwai lauje cikin nadi duk yadda sukayi da abdul sai daya kwashe ya gayawa ammi ita kuwa su'ad tun da musty yashigo taji yasoma mgn akan ak ta mike da kyar ta la'be cikin labule tana sauraronsu . "ammi tace nayi tinanin haka rashin kwakwarar hujja yasa kaji nayi shiru sbd sanin halinsa na wulakanci , kasan kuma asiri yana tadda hali ,halinsa dana sani shiyasa