Sashe 199
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wando sai farar riga me dagon hannu daga cikinta ,ta daura after dress asamanta hannuta daure da agogon fata baki, tai Rolling kanta da mayafin after dress , flat bby shoe ne red sanye da kafafunta tayi wani irin azababben kyau," gsky ban da tafiya zaiyi daita da bazai bari ta fito hk ba, killace abarsa zaiyi kawai km ban da ammi dake gurin cewa zaiyi takoma ta sauya wasu kayan amman yasan yana yin wani abu karsheta ya rusa plain dinsa akanta, dan hk ya mike tsaye yana sake yiwa ammi sallama yayi gaba abinsa. eiman tasanya kai ta fice tare da cewa "ammi sai mun dawo su'ad ma har takai bakin kofa tana wa ammi sallama ta dawo baya kadan gabanta na faduwa tana jin kmr karta tafi rakiyar "ya'akayi mamana ko akwai matsala ne? girgiza kai kawai tayi tasoma tafiya kmr kazar da kwai ya fashewa aciki "idan bazaki rakiyar ba kiyi zamanki man. kmr tace to km ta kasa mgn . can waje kuwa AK ne ke zubawa eiman maseefa ina tabar su'ad . "wallahi yaya ban san me ta tsaya yi ba amman bari na dubuta ta juya cikin sauri. can sai gasu sun fito tare hannunta rike cikin na eiman tana tafiya ahankali kmr batason taka kasa, naunaiyen ajiyar zuciya ya sauke yashiga byn mota ya zauna har bakin motar eiman ta kaita ta bude mata kofar motar tashiga ta rufe ta karasa tashiga dayar motar . daga ita sai shi acikin motan sai direba dake mazauninsa hk kawai ta tsinci kanta cikin yawon jin faduwar gaba idanunta suka cicciko da hawaye ta dinga jan numfashi da kyar tana fitarwa hankali yayi matukar tashi hk kawai taji tana zubda hawaye sanda suke gifta unguwarsu ummanta ce aranta kmr tace a tsaya tashiga amman tasan mgnrtata bazatai wani amfani ba ga mutumin take mahaukacin so.. kawar da kanta tai gefen titi tana kallon motoci dake wucewa tana cigaba da kuka.. "sautin kukanki na dagula min lissafi ,yayinda kwalkwaluwata ke cikin over thinking ,"ki tsagaita kukan nan zuwa gaba ko zai miki amfani kunnuwanta suka jiyo mata sautin muryarsa yana mata mgn cikin sanyi kmr ta juyo garesa ta sake kallon yanayinsa sbd yadda muryarsa ta fito din kmr yana cikin damuwa amman sai ta fasa tacigaba da kallon gefen titi. ya motsa labbansa zai sake cewa wani abu sai km ya fasa ya ciro wayarsa data dauki karan sauti me dadi yanayin yadda yake amsa mgnr tasan musty ne wayar suka cigaba da yi har suka iso airport wanda dole tasa ya takaika mgnrsa ya katse kiran. yana gaba suna biye dashi a baya ita da eiman airport din cike yake makil da tarin jama'a wadan yawancinsu duk matafiya ne zuwa kasashen duniya ahankali ta lura yana rage saurinsa zuwa tafiya ahakalin har takaraso garesa. ala'mun yayi mata tayi gaba byn ya dakatar da eiman wanda ita bata lura da hkn ba gaban tayi kmr yadda ya umarce sbd idanun mutane da ke kansu tasan halinsa ganin mutane bazai hanashi shuka mata rashin mutuncinsa ba sai dai idan bata kuskure masa ba. ahankali sukacigaba da tafiya duk takun datai idanunsa na biye daita jikinta kebata idanu na kai kawo akanta hkn yasanya jikinta daukar rawa gabanta yashiga faduwa da sauri sauri kafafunta suka soma rawa rawa batare da ta ankare ba kafafunta suka harde tana yunkurin kaiwa kasa cikin zafin nama ya tarota ta fada kirjinsa rungumeta yayi tsam ajikinsa batare da wani shaka ba sannan ya rada mata sannu cikin kunneta "ki bi ahankali cikin siririyar muryarta ta amsa da to ahankali ya dago idanunsa yaga yadda idanunwa mutane sukai caaaa akansu ciki kuwa har da wani abokin kasuwancinsa kamal wanda gbdy idanunsa da natsuwarsa nakan su'ad . wani irin tuttukin bakinci ne me tattare da kishin matarsa ya caki tsokar dake makale da kirjinsa kawar da kansa yayi ahankali ya tsuguna har kasa yana duba kafafunta sai daya tabbatar da bataji rauni komai ba ya sake cewa "ki natsu plz naga duk kin rude bawani gurin zan tafi dake ba . kmr ta tbyeshi eiman kasancewar yanzu dayake tsugunne a gabanta ta juya bata ganta ba, amman tayi sh. mikewa tsaye yayi tare da cewa " muje ko ta dai kasa hkr sai da tmbyesh. "abdul wai ina eiman? tayi mgnr muryarta a sanyaye. mayatattun idanunsa ya watsa mata su cikin wani irin salo na shaukinta kana yace na aiketa yanzu zata dawo tayi mamaki kwarai sbd ita bataji sanda ya aike din ba. kwata kwata hk kawai takasa yarda dashi zuciyarta takasa samun natsuwa "ok bari najira anan ya watsa mata harara wanda yasa ta gigice tana shan jinin jikinta yayinda still idanu mutane ke kansa tun datake arayuwar har zuwa lokacin datayi zaman tantiranci bata taba zuwa airport ba wannan shine karonta na farko data sanya kafafunta cikin aiport tasan km hkn yana da nasaba da rudewarta . ahankali taji ya rike hannuta cikin nasa yana massaging ahankali ahankali yana cigaba da tafiya tare da daita. koda suka karaso reception baifi sauran minti goma jirginsu ya tashi ba ,kallonsa take cikin wani yanayi , shi km yana duba agogon diamond dake daure da tsintsiyar hannunsa can akasoma sanarwa matafiya su shiga jirgi abunda yabawa su'ad mamaki bai wuce hannuta dataji AK ya sake damka cikin nasa ba yasoma tafiya daita agigice take binsa da wani irin kallo ahankali aka gama duba kayansa kadai dan ita ba da komai sai yar jakar rataye data makala itama babu komai ciki sai wayar hannu da yan tarkacenta kai tsaye harabar inda jirgin yake suka nufa "ki natsu ki daina zazzare idanu hk kar mutane su dauka satoki nayi gabansa yasata yana biye daita abaya har cikin jrgin kai tsaye kujerun da'aka tanada na VIP suka nufa yasanya ta gurin window shima ya zauna gefenta ya hade fuska dan ya lura da yanayinta tana iya yin abinda zai saka mutane su gane ba'a son ranta take zaune ba . cikin mintuna da basu wuce 30 ba jirginsu yasoma shawagi aiko su'ad ta kamkame jikinta dan ji tayi kmr ana ya mutsa mata kayan cikinta ne. satar kallon yayi kadan ya kawar da kansa sai lokacin yayi tunani may be wannan shine Karonta na farko data shiga jirgi ba ta saki jikinta ba sai da jirgi yai balance a sararin samaniya . Wani zama ne sukayi cikin jirgi,tunda suka shiga babu wanda yayi wani mgn sai da tafin hannunta na cikin nasa yana massaging ahankali ahankali . wannan abokin kasuwancinsa ne yayi masa magana wanda tun shigiwarsu aiport din ya lura da yadda yake binsu da kallo, su'ad ta dubi fuskarsa taga ya maseefar tsare gira kmr wanda aka aikowa da mutuwa ,kasancewar yasan halin mutumin mugun mayen mata ne, idanunsa basa ganin mace ya kyale mugu mugun dan harka ne na bugawa ajarida sbd tsabar jarabar neman matansa yasa duka matansa suka kasa zama dashi ,ga dai kudi kmr ya kasheshi amman dukiyarsa na neman mata ne. km wannan mutumin yasan halin AK ciki da bay hk shima ak kar tasan kar ne tsakaninsu sai duk neman matan ak bai kai kalma ba, kamal karshe ne km hatsabibi ne gurin harka da mata dan ya zarta ak . duk macen da kamal yaji yana sha'awarta ko matar aure ce sai yasan yadda yabi ya nemeta. ko yanzu dayake zaune daga dayan bangaren idanunsa na kan su'ad yana satar kallonta a ranshi ya furta Allah yayi halitta anan tunda yake bai taba cin karo da macen dayaji farat daya tashiga ransa ba kmrta zance zuci kawai yake yana kokarin sake ka llonta idanunsa yayi clashing dana AK. da idanunta yayi masa gargadi sannan ya kare matarsa sosai ta yadda babu yadda za'ayi yaganta duk nacinsa. har wannan lokacin a dan tsorace su'ad take dan jikinta bai bar rawa ba ganin hk yasakashi yasanya tafin hannunshi cikin nata yana sake matsowa kusa daita sosai yana mata magana kasa kasa,duk wanda gansu zai gane suna cikin shaukin soyayyar juna . ahankali yake mata mgn cikin kwantar da murya "Banson ki sakawa zuciyarki damuwa ina matukar son kasancewa tare da domin in dawo da soyayyata cikin zuciyarki shiyasa nasatoki tunda mamanki takibani hadin kai, dan hk kibini a hankali" yanzu kina cikin doka da orde ne. kirjinta ya dinga budewa maganganunsa na masu masauki na musamman yayinda zazzafar soyayyarsa ke sake kawo ma zuciyarta ziraya yana fixgar tsokar dake makale akirjinta . wani irin sauyin yanayin take ji ajikinta sbd taushin laulausar tafin hannunshi da ke ratsata yana circulating every part of her ,yayinda shima ya tsinci kanshi cikin yanayi datake ciki sai dai shi ba lallai ne a fuskanci hk ba . ahankali taji ya sauke boyayyar ajiyar zuciya lokacin dayake jin yadda dumi tafin hannunta ke ratsashi yana bin kowacce jijiya dake zagaye da jikinsa. ganin yadda ta runtse idanunta ala'mun sakon dayake aika mata ta tafin hannunsa yasoma tasiri ajikinta yasa cikin sanyi muryarsa yace "Kwantar da kanki a saman kafadata idan kina jin bacci ne . idanunta ta bude ta waigo gareshi tana dubansa sai taga shi din ma ita yake kallo ta kawar da fuskarta, shi km yasoma daddana wayarsa. ,a hankali ta dora kan nata saman kafadarsa kmr yadda yabata umarni ,dumin jikinsu ya soma gauraya atsakaninsu yana kaiwa kowanensu farmaki taja wani irin numfashi da kyar wanda ya shako mata daddande kamshin turaren jikinsa,kana ta sauke numfashinta a hankali tana lumshe fararen idanunta ahankali kamshinsu dake gauraye da juna yashiga bada wani sihirtaccen kamshin na daban sosai take jin dadi kamshin turarensa dake bugar mata hanci. numfashi take ja sama sama kmr me cutar asma tana fesarwa ahankali shima numfashinta da kamshin turarenta ke kaiwa zuciyarsa farmaki wanda yake neman caza tunanisa, kokarin control din kansa yayi dan ji yake kmr ya kwantar daita ajikinsa ya daura bakinsa kan nata ko zai dan samu natsuwar zuciya . Jin bai sake yunkurin ce mata komai ba . yasanya itama taki bude idanunta ko daga kanta ,tayi lamo akafadarsa tana shakar daddadan kamshinsa,a hakan batasan sanda bacci yayi nasarar daukarta ba . ya gyara zamansa ya tsura mata idanunsa yana kallonta . ahankali yake jin yadda zuciyarta ke bugawa a nutse,wanda hakan ya tabbatar