← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 267 OF 289

Sashe 267

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Taufeek minister Rak da k'anin mahaifinsu Ammi banda Shemah suka bi jirgi . 12 :00 daidai a k'asar Cotonou tayi musu batare da bata lokaci ba escort dinsa suka shiga bubude kofar motocin, suka shiga direbobin suka ja, lokacin da taga motacin sun karya kwanar unguwarsu taji bugun zuciyarta ya tsananta, "ta yaya zata fuskanci iyayenta ? "da wani ido zata dubesu bayan shekaru sama da ashirin datayi batare dasu ba ? har motocin suka ja suka tsaya a k'ofar tafkaken get din gidansu bata da kuzari , jikinta yayi mugun sanyi . ahankali mutanen dake cikin mototocin suka soma firfitowa d'aya bayan d'aya har suka gama fitowa banda ita dake zaune har lokacin abayan motar. Ammi ta sake lek'owa cikin motar "fito mana Salema kisanyawa zuciyarki natsuwa babu wani abinda zai faru sai alkhairi, takarasa maganar tare da kamo hannuta cikin nata, ta fito kafafunta dake rawa. idanunta ta d'ago ahankali ta tsurawa gidansu , tana kallon gidan ,tsarin ginin na nan kamar da can baya sai d'an karin kyale kyalen zamani da gidan yasamu wanda hakan ya nuna mata ahlin gidan suna nan kan samun abun duniya, koma tace arzikin yaci uban na da . me gadin gidan wani mutun ne daban ba wanda tasani ba ahankali take bin bayan Ammi dayake sauran mutane sunyi gaba har sun nemi iso zuwa cikin gidan bayan kamar minti biyu ta d'ago idanunta saka makon jin sautin muryar wanda ya fito bayan shigar me gadi, gama d'agowarta ke da wuya ta sauke idanunta akan k'aramin kaninta autansu Sulaiman ,wanda yanzu ya kara girma ko tace yazama babban mutun kamar a mafarki ya ganta ,mutuwar tsaye yayi agurin yana dubanta kana yashiga nuna ta" yaya salem............. kece ko kuwa idanuna ne ke min gizo? Dady ne ya bashi amsa da "itace me gidan na nan? kai kawai yashiga girgizawa sannan ya juya cikin sauri ya koma cikin gidan yana kiran sunan "mamma mamma mamma !!! "ga Salimarki mamma daga inda take zaune jikinta ya d'auki rawa duk tasan tabbas wata rana wannan ranar zatakasance.. Tashi take son yi daga inda take zaune amman ta kasa yunkurawa har sanda Ammi da Salima suka k'arasa shigowa had'ad'd'en parlour'n gidan tana zaune idanunta sanye da farin medical glass ta tsurawa k'ofar shigowar idanuta tana kallon d'iyarta data zama cikakkiyar mace. kallon kallo ne aka shiga yi tsakanin uwa da 'ya wasu hawaye ne shrrrrrr suka shiga bin kuncin Salima da ta k'asa cigaba da d'aga kafafunta, tsawon rayuwata bata tab'a jin farinciki irin na yau ba. sakamakon d'aura kwayar idanunta datayi akan mahaifiyarta, take anan duk wata ga'ba ta jikinta tashiga aiki fiyye da lokutan baya, yadda ta zuba mata ido tana kallonta tana zubda hawaye haka mamma ta zuba mata ido "mamma ta tsufa sai dai ba can ba wanda tasan tsabar jin dadi ne ya hana tsufanta bayyana. Mahaifiyar Salima tsaye ta zuba ma 'yarta ido tana tasbihi ga Allah daya dubeta da idon rahama ya amsa mata rok'on ta, Ya dawo mata da tilon 'yarta mafi soyuwa a gare ta lfy. zance zuci tashiga yi "Allah nagode ma daka dawo min da Salima cikin duniya ta naganta tun ban mutu ba, Salima k'araso gareni Salima inji dumin jikinki, "hmmmmm tabbas Salima jikina yana bani daman kobajima ko ba dad'e watan wata rana zaki dawo garemu. Duk zantuttukan nan da mahaifiyar Salima keyi a zuciyar ta take yin shi azahiri kuwa zuba ma gud'an jinin nata ido tayi babu ko kiftawa. salema dake tsaye tmkr an dasata ahankali sautin murya Ammi taji ta doki cikin kunnuwanta "ki k'arasa ga mahaifiyarki Salima taji dumin jikinki kiji nata yau ranar farinciki ce gareku gaba d'aya, ki god'ewa Allah da kika sameta araye cikin koshin lafiya. tasoma k'okarin d'aga kafafunta da Suka soma sagewa tana k'ok'ari zuwa ga mahaifiyarta wace zuwa lokacin ta yunkura da kyar ta tsaya bisa kafafunta tare da ware hannuwan ta duka ala'mun tazo gareta tak'arasa da hanzarinta tashige jikinta suka rungume juna. Salima na wani irin kuka me ta'ba zuciya babu abinda yafi iyaye dadi arayuwa barin ma uwa... ..."uwa dabance uwace kawai zata iya sanin radadin da ciwon ya'yanta, uwa jigon rayuwa itace komai itace jin dadin rayuwar ya'yanta babu kamar uwa a duniya . farinciki da bakinciki da zai same mutun uwa bazata tab'a gudunka ba wani irin sanyin dad'i ne ke ratsa zukatansu sosai Salima ke kuka mamma na shafa bayanta dan farin ciki yasa taka sa furta dai dai da kalmar d'aya. cikin muryar kuka Umman Su'ad tasoma magana "mamma ki yafe ni....... kiya femin abinda nayi nasan nayi kuskure abaya wanda bazan sake kwatanta abinda nayi ba tsawon minti goma suna rungume da juna sannan Umman Su'ad ta zare jikinta suka tsurawa juna idanun ahankali ta karya gwiwarta zata tsuguna gaban mahaifiyarta wanda sai lokacin mamma tayi mata magana cewar" "karki zauna a k'asa mana mamana "mamman kibarni haka ina babana yake ina son sake d'aura idanuna akansa ? "mahaifinki na nan salema yana d'ayan b'angare can ya koma da zama tun bayan barinki gida ,"ga Sulaiman can yayi bangarensa na sanan zuwa yanzu yasan da zuwanki takarasa maganar tare da duban inda Ammi ke tsaye tana dubansu" "bawar Allah sannuku da zuwa kiyi hak'uri dan Allah ga gurin ki zauna. kafin kace me tuni dawowar Salema ya isa kunnen yan'uwanta gaddafi da Yasif Ibrahim Sulaiman gaba d'aya sun zagayeta kowanensu na murnar dawowar ta .. can kuwa an yiwa su Dady masauki a b'angaren baki inda mahaifin Salema ya isa d'akin cike da matsanancin mamaki bak'in da akace yayi ahankali yashigo parlour'n bakinsa dauke da sallama "Assalamu Alaikum.... gaba d'ayansu suka amsa masa Taufeek dake zaune ya d'ago idanunsa domin sake kallon fuskar dattijon daya hanashi abinda ya so mallaka tun ganiyar kuruciya ,idanunwansu suka tsarke cikin juna tsawon rayuwarsa bai tab'a shiga tashin hankali da rudu irin na yau ba musamman tozali dayayi da mutumin dayayi sanadin rabashi da tilon d'iyarsa mafi soyuwa acikin ransa.... mutumin da ya aikata masa babban laifi da har ya koma ga mahalinsa bazai tab'a mantawa ba "mutumin da yayiwa diyarsa abu mafi muni da yankan kauna anan take jikin dattijo Alhaji Mahmud ya d'auki rawa shigowar Yusuf ce yasamu madogara , domin dafashi yayi sannan ya iya cigaba da tafiya har zuwa mazauninsa batare da ya iya cewa komai ba. tsawon minti goma da zamansa idanunsa na kan Tauffek yana kare masa kallo "ko da me ya sake zuwa masa? dan har lokacin bai san da zuwa Salima ba dan Sulaiman bai yarda ya sanar masa ba gudun abinda zai je ya dawo. Dady da kanin mahaifin Taufeek ne sukayi karfin halin gaisheshi ya amsa yana girgiza kai sannan Taufeek ya mike daga inda yake zaune yakaraso zuwa ga mahaifin Salema ya durk'usa har k'asa ya gaisheshi babu yabo babu fallasa ya amsa masa sannan "yace ina diyata Salima....? "wannan kalmar tasanyaya zuciyar Taufeek bai d'auka zai iya tambayar sa ita ba dan haka zuciyarsa na harbawa yace "tare muke tana cikin gida. naunayen ajiyar zuciya dattijon ya sauke daga bisani k'anin mahaifin Taufeek yasoma magana akan musababbin abinda ya kawosu da kuma abubuwan da suka faru lokacin da Salima tazo musu da zance ciki. shiru Alhaji Mahmud yayi yana sauraronsu "wato dai dole sai da aka cakud'a masa zuri da diyar gaba da fatiha ?" shi yanxu me zai ce wannan ma cikin kaddararsa ce babu yadda zayi bai isa hana hakan faruwa ba. numfasawa yayi kana yace "nima bayin kaina bane akan dukkanin abinda ya faru alokacin har da sharrin sihiri da aka dinga jifana dashi nan suka shiga jajantawa juna inda daga karshe suka nemi auren Salima gurinsa batare da wani b'ata lokaci ba ya amince da wannan auren a karo na biyu wanda take Dady yabada sadaki aka d'aura auren Salima da Taufeeq murna gurin Taufeek ba'a kama hannu yaro ji yake tamkar an tsundumashi a aljanna ne.. Salima na tare da mahaifiyarta taji wannan abun farinciki ,mahaifinta ya aminta da zabinta a karo na biyu har yasanya hannunsa cikin lamarin aurenta sabanin shekarun baya. Addu'a sosai mahaifin Salima yayi musu tareda zaman lafiya me d'orewa yasama rayuwar aurensu albarka. hayaniyar dataji yana tashi cikin gidan yasan ta mik'ewa daga kwance datake acikin d'akin, tunda tazo gidan wannan shine karo na farko dataji sautin hayaniyar mutane bila adadin irin hk ahankali take takowa har zuwa cikin parlour'n inda idanunta suka sauka akan mutane datafi buk'ata ganinsu acikin rayuwarta mahaifinta da mahaifiyarta. zaune gaban dattijon da tun zuwanta gidan ganinta dashi bai fi sau biyu ba shima a boye sakamakon kin yarda da kakarta tayi su hadu dashi....... mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE
Chapter 267 · 0% Book details