← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 289

Sashe 34

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *qala rasulillahi sallallahu alaihi wasallam:* *laa yahillu lilmusli an yahjura a khahu fauka salaat* *Allah's messenger (s. a. w) said it's not permissible for a Muslim's to forsake his Muslim brother beyond three days* Page 14 Yayi murmushin mugunta tare da sake damke h annuta sosai cikin nashi yana murzawa ahankali muryarsa a kasalance yace ai ita wace nike son ba sai na rike hannuta ba itace zata rike nawa, sbd tsabar tana son kmr yadda nike sonta. ki zauna kawai muci abinci wlh bana jin dadin yadda Duk kika canza min akan nace wata nike so ba ke ba ... Zeey ta yatsina fuskarta kmr zatayi kuka ,muryarta raunace tace ka kyaleni nayi tafiya . "bazan kyaleki ba sai kin zauna muci abinci Dan nasan duk kwanakin nan bakya wani cin abinci Kalli yadda Duk kika rame Dan Allah.. A fusace tace to nace na koshi bazan ci ba ko dole ne .. AK ya gyara zamansa yana tsareta da mayatattun idanunshi ai ko yarinya karyarki Tasha karya wlh sai kin zo mun ci . IN ba hk ba na dauke Ki na daura Ki kan ciyoyina na dura miki Ta karfin tsiya. Ta rausayar da idaunta tana tabe baki zuciyarta na wani fizga tkmr zata fasa kirjinta ganin yanayin kallon datake masa yasa shi cewa ko kina ganin bazan iya bane kike wani kallona kmr wata wawiya. tai tsuru tsuru da idanu domin tasan halinsa Zai iya komai yace.. Ita km tasan yanayinta Dan hk tace ka kyaleni zanci. Yadda yanayin sautin muryarta ya fito yayi matseefar bashi dry Dan hk ya kyaleta tawani sauke ajiyar zuciya da karfi. Ak yacigaba da cin abinsa batare da ya sake kulata ba . ko ce mata wani Abu ita Kuwa Zeey dago kanta tayi tana satar kallon AK Wanda ya maida hankalinsa gurin cin abincinsa ya gama ta kwashe kayan abinci Ta nufi kitchen dasu data dawo maimakon Ta zauna a parlour sai ta nufi hanyar dakinsu. Muryarsa a kausashe yace ke Ina km zaki? Ta tsaya tana kallonsa Ki zo ki zauna muyi hira bacci nike ji ya zabga mata katuwar harara ban yarda ba kawai kizo Ki min hirarrakin da kika saba min wayanda suke sakani nishadi.. Da gaske bacci nike ji da safe idan Allah ya kaimu zan maka ya sake watsa mata wani hararar ke dai kice zakiyi Min wayo ne. tayi murmushin jin dadi ganin har yanzu yana bata kulawar data dace bai canza mata ba. dakinsu Ta nufa tare da maida murfin kofar ta rufe Kai tsaye bayi tashige ta jingina bynta da jikin kofar Ta sanya hannuta duka ta dafe daidai saitin kirjinta sakamokan bugawa da yayi da karfi yayinda taji zuciyarta tana harbawa da sauri sauri tabbas bata taba tsammanin son da takewa AK ya kai hk ba. Gabadaya ji take data rasashi gara tarasa rayuwarta domin Kuwa hkn zai fiyye mata kwanciyar hankali da sauki Akan taga AK yana rayuwa da wata baita ba bata Ankara ba sai dai taji saukar hawaye daga idanunta ahankali ta silale agurin . durkushe bisa gwiwowinta tana cigaba da kuka jitake tmkr ta daura hannu bisa kanta ta rusa ihu kozata samu me kawo mata dauki akan halin tashin hankslin datake ciki da jin saukin tafarfasar da zuciyarta takeyi mata .. wayyohhly Allah ka taimakeni kada narasa abdulkabir.. abdulkabir ya zamto wani jigo ne na rayuwata me matukar mahinmanci ina matsanancin sonshi banason rasa shi meyye aibuna da baza soni ba? Da kyar tasamu ta fito Ta rarrafa zuwa inda sabuwar shimfidar take ta kwanta lamo game da lumshe idanunwanta duka hawaye suka cigaba da silalawo akan fuskarta zuciyarta km tacigaba da harbawa hade da tafarfasa sakamakon matsanancin son AK dake cin zuciyarta.. Kwana biyu tsakani AK bai nufi inda onye take ba sai yammacin yau zaune yasameta cikin dakin tana karanta jaridar dailytrust tana ganinsa tayi xumbur Ta mike tare da ajiye magazine din dake hannuta ta nufoshi tana yauki ta rumgumeshi tsam tsam ajikinta tmkr wace zaa kwacewa shi Tana shakar dadadden kamshin turarensa me zautar da tunainta. Ya lakuce mata hanci da alamun yau kina cikin nishadi? Ya fadi hk yana kokarin cireta daga jikinsa suka zauna kan katifarta ta lumshe idanunta tana matsowa jikinsa cak ya dauketa ya daura bisa cinyoyinsa fada min meye sirrin wannan farinciki da nishadin da nike hangowa acikin kwayar idanunki domin na lura kina cikin nishadi onye tayi murmushin tace jin dadin ganinka on expecting ganinka kadai kan mantar dani komai, Ganinka nasa na dingajin kasala a ilahiri sansar jikina ganinka nasa nakasance cikin matsansncin farinciki AK son da nake maka bakina ba zai iya furta maka shi ba ..takarasa mgnr tana sanya idanunta cikin nashi tare da narkar dasu wanda hkn yasamu nasarar kashe Masa jiki AK ya lumshe mayatattun Idanunshi yana cizan lip's dinsa sannan yace nasani.. Nasan kina sona sosai fiyye da tunaninki tun ranar farko da muka soma haduwa nasan Kin fada tarkon sona . Sai dai am sorry to say ni dai kina matsanancin birgeni Amman maganar so.. Yayi shr yakasa furtawa Ta tacigaba da kallonsa ka karasa Man baka sona ko abdulkabir..? A tarihin rayuwata banta jin wata ya Mace Ta birgeni ba kmr yadda kike birgeni. kin shiga rayuwata dayawa sai dai shi wannan son ne bazan taba miki karyar ina miki shi ba... Basani ba ko gaba ba.. ta rungumeshi ajikinta ni dai what I know I love you so much and I can't do without you honey dan Allah Kasoni ko yaya ne, daga nan suka shiga holewarsu da suka saba... har misalin karfe shabiyu na rana Zeey tana kwance a daki Kirjinta ne yake Yi mata ciwo Amman sbd gudun tashin hankalin ammi taki fada GAnin bata da niyar tashi ne yasa iman ta nufi inda take kwance domin taga halin datake ciki aiko tana taba jikinta taji rau atafin hannuta da Sauri Ta janye hannuta ta nufi dakin ammi tasanar mata atare suka dawo ammi ce gaba iman tana bayanta ammi na tura kofar dakin ta hango Zeey kwance a kasa sai mayar da numfashin take sama sama tmkr me cutar Asma ammi tayi saurin karasawa inda take kwance a rikice ta janyota jikinta game da cewa subuhanallah Zeey me zan gani hk kwanciya akasa ?Allah ammi nima hk kawai naga ta dauki salon kwanciyar kasa ai ko sanyi Tayis ya isa ya saka cuta takamata inji cewar iman, meke miki ciwo Zainab, Zeey ta Kalli ammi ta nuna mata saitin zuciyarta subuhanallah to meyasa baki fada ba zaki zauna da ciwo hk ,ke iman jeki kicewa yayanki yazo yanzu yakaita hospital, iman Ta juya da sauri ta fice ta nufi part din AK wanda ke kwance suna waya da onye iman tayi nocking yace yes who is that it's me yaya ammi ce Ta aikoni ya Mike da kyar ya nufo kofar ya bude tare da kashe wayar iman tace wai ammi tace kazo ka kai aunty Zeey hospital bata da lfy meke damunta? Tace unhmm ina GA Dai kmr Ciwon kirji ne.. AK yace OK gani nan zuwa iman takoma dakinsu inda ammi ke rungume da Zeey har lokacin tasanar mata sakon AK ta taimaka suka shiryata ammi ta kamota ita da iman suka fito farfajiyar gidan hkn yayi daidai da fitowarsa daga bangarensa yanayin yadda ya ganta yasanshi karasowa gun da sauri yace ammi hk jikin nata yayi tsanani sosai? Ammi tace hk nima nagani narasa meke damunta duk kwanakin nan hk take.. Da Sauri ya tashin mota suka wuce hospital Kai tsaye emergency aka nufa da Zeey sbd yadda jikin nata ya kara tsanani cikin kankanin lokaci doctors suka taru akanta domin kokarin ceto ranta daga barin gangar jikinta ammi takira mahaifiyarta sanda tazo hankalinta yayi matukar tashi hk ma AK Shima hankalinsa ya tashi da ciwon zeey. Cikin ikon Allah ba dauki wani lokaci ba doctor ya fito daga dakin da aka kwanantar da Zeey dr yakira ammi da AK sbd sune suka kawota yace yana son ganinsu a office dinsa. Ammi da AK zaune gaban doctor byn Dr yayi yan rubuce rubuce akan file din Zeey ya cire medical glass din dake manne da idanunsa ya dubi ammi yace kece mahaifiyarta..? Eh nice ya maida dubansa kan AK kai km kaine yayanta ko? Ak ya jinjina Kai batare daya amsa ba. Gud doctor ya sake duban ammi yace Hjy yarinki tana cikin damuwa me tsanani domin akwai abinda ke damunta wanda Ta saka shi cikin zuciyarta dalilin hk ma Ciwon xuciya ke daf da kamata ga jininta ya hau sosai ammi nagama sauraron bayanin likita Ta dafe kirji tace inna lillahi WA inna ilaihi rajiun Zainab da ciwon zuciya ga hawan jini wannan kankanuwar yarinyar da manya ciwoka hk? Ita kuwa Wace irin damuwa ce take Tare daita da har ta janyo mata wannan muguwar matsalar? Doctor yacigaba da koro bayaninsa Dan hk ya kamata kuyi bincike ku gano menene matsalar domin a samu a magance mata ita domin gudun kara faruwar wani abu km a daina bata rai domin da zarar an bata mata rai hankalinta zai iya tashi sakamakon hkn km Ciwota zai iya tashi.. Ammin tace Inshaallahuu zamuyi iyakacin bakin kokarinmu Dr ya rubuta irin magungunan da masu lalura irin nata ke Amfani dashi. Mahaifiyar Zeey da ammi da iman zaune jigun jigun suna kallon Zeey dake kwance an daura mata drip sai bacii take sakamakon allurar bacci daaka mata. AK yashigo dakin ya gaida mutane dakin tare da tmbyr me jiki da saukin muslinci suka hada baki har yanzu dai bata farka ba. ya nemi kujera ya zauna sai byn da aka idar da sallar magriba Zeey ta farka mahaifiyarta dake kokarin sallame sallah takaraso gareta Dan ammi sun wuce tun dazu tai mata sannu ta amsa ahankali ta nunawa mahaifiyarta tana son tashin zaune Dan hk Ta taimakamata ta tashin Ta jinginar mata pillow. Mahaiyarta ta tmbyeta ko zata iya shan tea Zeey ta girgiza kai alamun aa sbd me bazaki sha ba? Sbd bana jin dadin bakina. Daman ai babu yadda za ayi kiji dadin bakinki sai dai ki daure mahaifiyarta taje Ta hado mata tea da kanta ta rinka bata tana sha.
Chapter 34 · 0% Book details