← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 289

Sashe 186

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH YA RAH-MAN THE COMPSSINATE page 63 jin tayi shr taki cewa komai hkn yasa ya ja motar aguje yana cizan lip's dinsa na kasa ahankali ahankali, tare da murza sitiyarin mota , ta kasa daurewa ta dago ahankali tana kallonsa zuciyarta na matsanancin bugawa, zatayi mgn yace "karki ce min komai dan bazan iya barinki kwana wani guri ba, gara muna waje daya koda bazaki min amfani komai ba zansu ki kasance a inda nake . dauke fuskarta tayi daga gareshi ta maida gefen titi taki yunkurin sake ce masa komai sai da zuciyarta cike take taf da kuncin me tattare da takaicinsa, "gidan ubanta inda mahaifiyarta ke rayuwa ciki ,yake kira da wani guri .... "wasu lokuta al'amursa na matukar bata mamaki da daure kai, tarasa wani irin mutun ne shi me son kanshi dayawa , akoina sai ya gwada kunjinsa akanta , wanda tasan sharadinsa da ikonsa ba iya kanta kadai ya tsaya ba, ko har da sauran matan dake kai masa hari yakewa iko da nuna shi wani ne . yadda ta juyar da kanta gefen titi tai kmr batasan da zamansa ba, hk shima yayi mata banza yacigaba da tukinsa har suka iso harabar gidan'su ammi babu wanda yacewa danuwansa kala. yana gama parking ta yunkura zata fito a matukar sanyaye tare da sanyo kafafunta waje byn ta bude kofar mota . shima ahankali ya karasa fitowa yayiwa motar key bai fi sauran taku biyu tashiga part din ammi ba ya cimmanta kasancewar bata da saurin tafiya yasa hannuwansa duka ya janyota zuwa jikinsa ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya bakinsa daidai saitin kunennta wanda hkn ya haddasa mata jin wani iri a gbdy ilahiri gangar jikinta muryarsa a kasalance yace "fushi kikeyi dani ko? "tai shr ...." " kiyi hkr ba nufina na kuntata miki ba amman ki duba yadda zan tsinci kaina idan barki a wani guri ba inda nKe ba... "naji ni ba fushi nayi ba sakeni nashiga ciki. "nagode nakira wayarki? ta gyada masa kai ok muje ya sakar mata jiki tare da janyo hannuta cikin nasa suka jera tare har cikin parlour 'n ammi bakinsa dauke da sallama . ammi dake kallon tashar arewa 24 ta waigo ahankali tana amsa sallamarsa, ganinsa tare da su'ad yasa ta kasa karasa amsa sallamar da yayi. ya waske yana shafa sumar kansa da dayan hannunsa, tare da kashe mata idonsa daya ,ya zaunar da su'ad gefenta yasamu guri gefen ammi ya zauna "ammi sannu da gida inji cewar su'ad yauwa mamana ya jikin naki? "naji sauki . "ammi nah karki wani damu daman ciwon nawa ne km na magance matsalar sai dai atari gaba ko hrt beat ,su'ad tayi masa banza tare da zabga masa harara tana me dauke kanta .... " kai kai!! abdul bansan wani irin halita bane kai, yanzu zuwa kayi ta taho daita? " sai dai kiyi hkr tunda gata agabanki ni dai alfarma daya kar a sake barinta fita koina, idan ma fitar taza dole a gaya min kawai dan gsky banason dogon yawo, yayi mgnr yana mikewa tsaye tare da kokarin son barin parlour. "ammi ta juyo tana kallon su'ad wace ta dawo kalar tausayi dan gbdy ta sukurkuce "kiyi hkr mamana hk halinsa yake kece zakiyi kokarin canzashi. "babu komai ammi ni yanzu abinda yafi damuna shine bamuyi sallama da ummana ba.. "ok bari na kirata miki " koda ammi takira umman su'ad tana gaya mata abinda ya faru, cews tayi babu komai Allah ya tashemu lfy. "ina su'ad din? ammi tayi saurin mika mata wayar tare da yi mata ala'mun tai mgn " muryarta na dan rawa tasoma mgn "ummana kiyi h... umma tayi saurin katseta ta hanyar cewa "karki damu diyata ya jikin naki yanzu ? "naji sauki " suka dan dauki tsawon minti goma suna hira yayinda su'ad ke narkewa tana zuba shagwaba sannan sukayi sallama . karfe 10:00 dot Yagama duka wani abu da ya zame masa kaida yayi shirinsa na bacci ya lalubo wayarsa yashiga neman layinta lokacin suna tsaka da hira ita da eiman kiransa yashigo . tana dubawa taga shi ne aranta tace aifa nashiga uku da dan naci tsiya . eiman tabita da kallo batare da tace komai ba sai daya kira yafi sau goma sannan ta dauka muryarta a sanyaye "hello.. "malama wannan wani irin sabon salon iskanci ne ina kira kina kallo kiki dauka? muryarta a dake "tace ina cikin mutane ne . "su waye wadan nan mutane, da mahimmanci su ya zarta nawa ? "zan kiraka idan na kimtsa kawai yaji kit ta katse kiran ...eiman tabita da kallo mamaki dan zuwa wannan lokacin ta fahimci me kiran . "gsky bazamu yarda wannan ajin fa yana son yayi over dayawa karfa aje neman gira arasa ido .. "ai wannan yayan naki ne sai da hk wallahi ya cika son kai da zafin zuciya,"aji km yanzu nasoma jan zarena shima dayake nmj yayi fiyye da nawa sai nice zan kasa amsawar kaina y'anci , dan hk yanzu time dina ne nima a barni na wataya "sai dai yyi hkr takarasa mgnr tana murmushi itama eiman kwashe da driya tai tana bata hannu suka tafa. ak dake kwance yabi wayarsa da kallo cike da matsanancin mamaki ya sake gwada kiran layinta still taki dauka ya dafe goshinsa da hannusa yana jin wani irin tuttukin bakinciki "hk zamuyi da yarinyar nan? ya mike tsaye. "ni zata jama aji? Ya fadi hk yana sake kira layin yaji wayar a kashe. bangarenta kuwa hirarsu suka cigaba dayi daga karshe sukayi kwanciyar su ,da kyar su'ad ta samu barci ya sace ta byn juye juyen data dingayi tana takure jikinta guri daya . washegari da Zullumin haduwarta dashi ta tashi . salon soyayyar AK da tsarin yanayin takurawarsa da nuna ikonsa yana matukar bata tsoro gaskiya. Shi kuwa tunda ya tashi yake faman zarya apart din ammi, ammi na lura dashi tayi kamar bata san yanayi ba ko breakfast yaki zama yayi gashi sai faman kiransa ake daga office da ala'mun kiran is very important amman yaki tafiya. Ransa yayi mugu mugun baci matuka, ya zauna tare da dafe goshinsa yayi shiru yana tunani .. sai wajen 11 saura ta shigo parlour yana ganin ta ,ya sauke naunauyen ajiyar zuciya batare da yace mata komai ba sai tsura mata mayatattu idanunsa dayayi kawai yana kallonta duk ransa a matukar harzuke yake amman duk da hk yaji dadin ganinta . sai dai idan ka kalli yanayin yadda ya nuna afuskarsa kaza dauka baiji dadin ganinta ba. ahankali ya mike tsaye ya bar parlour 'n. " Ta gaida da ammi tana sunkuyar da kai dan bakaramin kunya taji ba lokacin da ak ya kafeta da mayun idanunsa yana kallonta kmr zai cinyeta, hk kawai ta tsinci kanta da kasa zama a parlour ta wuce kitchen ammi Ta bita ta ido tana 'yar dariya Wannan zafaffar soyayya ta abdul ai sai ya tashi gari. can kmr minti goma Ya sake shigowa yana daure fuskarsa me nuna ala'mun yana fushi. "ammi na wuce sai na dawo..... ammi ta kalleshi a kaikace "breakfast din fa ko zaka aiko ne? "no abarshi kawai na koshi yayi mgnr yana tafiya ,ammi tabi bynsa da kallo tana mamakin halinsa ,yacika zafin rai tsiya da son ikon mallaka ita duk bataga wani abun fushi anan ba . Koda ta gama hada abinda take son ci tayi dakin eiman. Da daddare taci kwaliyarta cikin dinkin riga da siket na atamfar super exclusive me zanen fulawa kalar ja da ruwan dorawa ,dinki yayi matukar amsar surar jikinta barin ma siket din wanda ya zauna das a kungunta ya fidda ainihi Hip's dinta, ta fashe ilahirin jikinta da daddaden kamshi turarenta, tazo parlour ta hakince tana zaman jira shigowarsa amma taji shiru gbby ta kasa samun sukuni dan hk ta mike ta fito waje ta nufi gurin motacin gidan duk suna jere a ma'ajinsu tafi kusan awa daya agurin tarasa gane da wace motar ya fita balle tasan ko yashigo gidan. tacigaba da tsayuwa agurin amma shr bashi ba alamunsa . Duk km sai ta shiga damuwa takasa tsukuni ta dawo daki dan kar ammi ta farga tana cikin damuwa ta kwanta lamo akan gado tana jin kmr taje part dinsu ta dubosa ko ya dawo gidan. Washe gari tunda sanyi safiya yabar gidan, nan hankalinta ya sake kololuwar tashi ta kasa tsaye ta kasa zaune cikin hk ammi ta rutsata adaki ta soma dan janta da labari har ta dan saki jikinta. abu fa kmr wasa ak ya lashi sati uku yana fitar sassafe km baya dawo gidan sai cikin dare ta sake shiga damuwa kmr wancen lokacin, wanda ita kanta ammi ta lura da hkn har ta kai ga tmbyrta " Ni kuwa mamana kwanakin nan duk bana jin dadin yadda nake ganinki ko bakijin dadin jikinki ne? "babu komai fa ammi lfyta lau ta fada tana yar murmushi wanda ya bayyana wushiyarta amman kallo daya zaka mata kasan murshin iya baki ne bai kai zuciya ba. "ni kuwa sai nake gane kamar kina tare da damuwa ko wani gurin na miki ciwo . "wallahi ammi babu komai "idan ba haka bane to ki saki jikin kibkoma kamar farko . " toh, tana sake fadada murmushinta. ammi ta danyi shiru tana nazarinta , sannan ta murmushi irin nasu na manya kana tace "mamana na daukeki tamkar 'yar da na haifa acikina, in takaice miki ko ya'yan dana haifa bana jinsu kmr yadda nake jinki kasancewar su din suna da komai na rayuwar duniya basu rasa soyayyar uba.. "ke kuwa tun kina cikin ciki mahaifinki ya rasu ya barki, a kullun na tuna dan uwana da abubuwan da suka faru abaya na kan zubda hawaye ,ahalin yanzu ke kadai ke maye min gurbin uwa uba dan'uwa har ma da dangi gbdy. dan haka ina rokon ki saki jikin ki kada kibari damuwar matsalolin abdul ya taba min farincikinki da lfyrki, wanda shine kwanciyar hankalina kinji. su'ad "Ta ce toh ammi nima ina sonki sosai a halin yanzu banajin cewa ni din maraniya km mara galihun, " ke kadai da kika rage min yar uwar mahaifina araye yafin komai yi min dadi a duniya
Chapter 186 · 0% Book details