← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 289

Sashe 77

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam addua'ussalahul mu'amin* *Allah messenger s a w said supplication is a believer's weapon* *besty comments for this novel*. *mrs adam* *maimuna matar,abdullahi* *zahra yakub* *subby* *mmn twins* *i really appreciate for the comment's* page 29 saurin mikewa AK yayi tsaye zuciyarsa na bugawa da matsanancin karfi,yana duban inda dady ke zaune yana sake cigaba da maimaita mgnrsa atsanake, matsawar abdulkabir mijin aurenki ne ina me tabbarta miki da zaki aureshi da izinin Allah. da yarda allah zane miki da zarar mahaifiyarsa ta dawo kasar . yanayin bugun zuciyarsa bai saisaita ba.. hk yanayin tsoratar da yayi da furuncin dady sai ya baka mamaki. bakinsa na rawa yasoma mgn cike da in.. inna ,ha..ba haba dady ....dan Allah dan annabi karka min hk dady. karkayi kokarin hadani da wannan watsartsiyar yarinyar amatsayin matar aurena.. yarinyar da bakasan ko wacece ba balle asalinta. dady kowani uba nagari burinansa arayuwa bai wuce yasammama ya'yansa uwa ta Gari ba.... idan na aure wannan gantalalliyar yarinyar nacewa ya'yana me...? mezance dasu dady....? kwata kwata bata cancanci zama uwa ko zaman aure ba. , tafi cancanta da watsatsu maza yan'uwanta ko yan zaman wajoko wlh shine abinda yafi dacewa daita . ya sake raunata muryarsa sosai kmr zai zubda hawaye hb dady'nah .. ka kalleni ka kalleta kasan babu ta inda muka dace da wannan prostitute din me bin..... ya isa dady ya sake katse masa hanzari a tsawace ta hanyar dakatar dashi, babu shiri yayi shr sbd yadda ya hango tsagwaron bacin rai shimfide akan fuskar dady'nsa . "karka sake kuskuren furta wannan kalmar gareta banson sake jinta daga bakinka, kaddara tana kan kowa km babu wanda ya wuceta. furzar da iska yayi daga bakinsa yana lumshe mayatattun idanunsa kusan minti goma ya dauka runtse da idanunsa sannan ya budesu ahankali ya meida kallonsa zuwa inda take tsaye tsuru tsuru tana kallonsa , tsoro da matsanancin firgici yaga ya bayyana akan fuskar su'ad yayinda zuciyarta tashiga bugawa da karfi numfashinta yasoma barazanar daukewa tayi saurin dafe kirjinta da hannunwanta duka, duk da wannan fargaban da zuciyarta ke ciki hkn bai hanata tattaro jarumata tasanyawa jikinta ba tare da zuba masa fararen idanunta tana kallon cikin kwayar idanunsa dake cike da matsanancin tashin hankali iri iri . tana jin ,wani irin bakin ciki me tattare da tsagwaron bacin rai na ratsa kowani sashi na gangar jikinta . wasu zafafan hawaye ne masu dumi da ciwo suka soma gangarowa bisa kuncinta. jitake duk duniya babu bil'adam da aka tabayiwa wulakanci da tozarci irin wanda abdulkabir yayi mata ayanzu .. meyye laifinta ....? bafa ita tasanyawa kanta soyayyarsa ba. Allah ne ya jarabeta da matsanancin kaunarsa. wanda a iya rayuwarta bata taba tsammanin zata tsinci kanta cikin wannan halin tashin hankali ba.. yau ita ke bin namji allah da annabi ya sota amman yake wulakantata hade da tozarci iri iri . gabadaya acikin tozarcinsa dayake mata kalmar karuwanci dayake hadata dashi yafi komai tsaya mata arai da bakanta mata rayuwa. ganin tana tsaye tana kallonsa bata da niyyar tafiya gashi dady yaki cewa ta tafi . yasashi harzuka yashiga nuna mata kofar fita da dan yatsan hannunsa tsayuwar uwar me kikewa mutane anan yayi mgnr cikin daga murya ki tafi man ko gidan ubanki ne nan ..? kawai ina zaman zamana kina son jazamin bala'i da wahalarki. ban da ita zuciyarki tsinanniyar zuciya ce tarasa wanda zataso sai ni abdulkabir... yakarasa mgnr yana furzar da iska da nuna kirjinsa gabadaya yafita cikin hankalinsa da natsuwarsa idanunsa sun gama rufewa burinsa kawai tabar gurin banda sambatu babu abinda yake yana zaginta da tozartata. " duk wani tsoron dady dayake ji abaya ayau ya kau acikin idanunsa da zuciyarsa . sam baya jin zai iya abinda dady yake son aikata wa . dady kace mata ta wuce wlh idan bata bar gidan nan yanzu ba zan mata lahani zan mata dukan mutuwa zan kasheta da hannuna na kashe kaina kowa ya huta haba narasa wace zan aura sai wannan karu...... ..saurin datse harshensa yayi yana cizan lips dinsa da iyakacin karfinsa sbd gargadin dady garesa. matsowa tayi ahankali kusa dashi tana girgiza masa kai ciki kaduwa . jikinta na rawa ta sake matsoshi sosai har suna iya jiyo numafashin juna..... yaja baya da sauri yana tsaida ita da hannunshi karki sake ki karaso gareni ..naji bazan yi kuskuren aikata hkn ba amman dan girman allah ka daina furta min wannan kalmar kada zuciyata ta buga Allah yasani ni ban kasance cikin wayan nan matan da kake lisafowa ba ....yiwa mutane shr stupid kawai Allah yasa zuciyarki ta fashe ki mutu na huta da jarabarki ......haba wannan wani irin naci ne sbd Allah nace ban sonki ban sonki ba sai ki rabudani ba tunda ba'a soyayya dole ayi mutun ba zuciya ... dady dake zaune yayi shiru yana kallonsu cike da matsanancin mamaki da tausayi abu tmkr a film. ahankali dady yakira sunanta da yarinya dan har lokacin bai san cikakken sunanta ba. su'ad tajiyo ahankali idanunta cike da ruwan hawaye ta daurasu akan fuskar dady. sai da dady yayi gyran murya tukun yasoma mgn atsanake cike da natsuwa. " kiyi hkr kiyi tafiyarki Insha Allahu zan san abinyi da yarda Allah .. karasowa tayi jikinta na rawa ta dukursa gaban dady har kasa tana masa godiya tana zubda hawaye me taba zuciya na gode na gode dady Allah yabiya maka dukkanin bukatunka na alkhairi yadda kake kokarin tallafawa maraicina Allah ya duba naka bayan.... a fusace ak yakaraso gareta zai damki wuyanta dady yayi saurin dakatar dashi da hannunsa yana yi masa warning kashiga hankalinka abdulkabir ka fita cikin idona na rufe sannan tun raina bai baci ba. ka dawo cikin natsuwarka ... wlh dady matsawar kana bukatar natsuwata sai wannan jakar yarinyar tabar gidan shine kwanciyar hankalina but as far as ina ganinta anan wlh bani ba wata natsuwa balle kwanciyar hankali dan kwata kwata bana kaunar na bude idanuna na ganta. bason daura idanuna akanta. to naji ka zauna zata wuce yanzu wani irin kuka su'ad take na fitar hankali me taba zuciyar ma'aboci sauraro. sosai zuciyar dady tayi rauni amman shi ak ko akwalar rigarsa sai ma Allah Allah yake tabar gurin ya huta . jikinta a matukar sanyaye ta mike tsaye hawaye na sake wanke mata fuska ta tsura masa ido tana kare masa kallo sannan ta juya ahankali tasoma daga kafafunta tasoma tafiya cike da sanyi jiki kirjinta na wani irin bugu kmr ana buga mata guduma ta isa bakin kofa kmr ta juyo ta sake kallonsa sai km ta fasa ta daura hannunta akan handle din kofar ta murda ta bude kofar ahankali tare da turawa ta fice daga part din. fitarta ke da wuya AK ya sauke naunauyen ajiyar zuciya tmkr wanda yayi gudun tsare, batare da ya sake yunkurin cewa komai ba ya koma ya zauna akan kujera zuciyarsa na wani irin harbawa da sauri sauri dady ya tsura masa ido kawai yana girgiza kai sannan ya yakira sunansa abdulkabir...da kyar ya iya bude bakinsa ya amsa da na'am dady . abdulkabir banason abinda kakewa yarinyar nan ,yana taba min zuciya wlh ita ma mutun ce kmr kai. akwai tarin mutane dayawa mara iyaka acikin wannan garin da km unguwar datake rayuwa ammam ta zabi takasance tare da kai. meyasa bazaka amsa tayinta ba? abinda nake so dakai da zarar anyi bikinka da zainab kayi kokari ka auri yarinya nan kodan yanto rayuwarta. "lamarin yarinyar akwai tausayi ciki,nasan bata cikin natsuwarta amman shi son datake maka abin a duba ne . ni kaina hk kawai tun sanda kabani labarin yarinyar na tsinci kaina da son ka aureta wanda bansa dalilin jin hk ba. a kallon farko danayi mata dazu naji tashiga raina . hakazalika tausayinta ke dawainiyya dani. bance zan tursasa maka akan lamarin yarinyar ba amman kayiwa Allah kayi tunani akan yarinyar nan ... tunda dady yasoma mgn ya runtse mayatattun idanunsa yana sauraronsa har sanda ya dasa aya baice komai ba ya numfasa tare da bude idanunsa wanda suka soma canzawa zuwa ja ya saukesu akan dady dake zaune yana kallonsa muryarsa a kasalance yasoma motsa labbansa dady ba bujirewa mgnrka nake kokarin yi ba . amman kayiwa Allah da manzonsa dady kabar zance yarinyar nan . wannan yarinyar da kake gani ba abar tausayin bace wlh azim bata da tarbiya balle kamun kai , duk wani abinda kasan nmj na sha na dangin maye babu wanda bata sha .. gang ne daita na musamman masu tadda tarzoma acikin gari. nasan bakasan da wannan halin nata ba dady ,dabaza ka taba cewa na aureta ba. ni dai dady dan girman Allah kayi hakuri kayi hkr da zance yarinyar nan dan bazan iya aureta ba, ya karasa fadar mgnr muryarsa na rawa kmr zaiyi kuka.. dady yayi murmushi irin nasu na manya sbd hango wasu abubuwa da yayi tattare da tilon "dan" nasa. kana yace yarinyar tana matukar kaunarka abdulkabir sannan bakasan abinda Allah yake nufi da hkn ba . bakasan me gobe zata haifar ba atsakaninka da yarinyar . a yadda yarinyar take mutuwar sonka zata maka biyayya zaka juyata yadda ranka ke so, sai yadda kayi daita matsawar baka aureta ba km kai kanka bazaka zauna lfy ba, bazata barka ka huta ba . farinciki dakake nema arayuwar auranka bazaka taba samunshi ba... aurenta kawai shine mafuta agareka damu gbdy ,nima ubane yadda bazan so ganin nawa ahlin cikin halin damuwar da yarinyar take ciki ba. hk zalika bazanso ganinta cikin tashin hankali ba, amman kayi nazari da tunani da kyau kafin dawowar amminka a thing this week zasu dawo abinda ka yanke ka sanar min ,dady nakarasa fadar hk ya Mike tsam yasoma kokarin barin part din.. yayinda AK dake zaune agurin kmr an dasashi yashiga damuwa mara misaltuwa , babu wani abun da zanyanke akai dady byn taje gaba ta nemi nata mijin yayi mgnr cikin zuciyarsa. tafe take bisa kafafunta tana zance zaci tmkr wata tababbiya sabon kamu, yayinda zuciyarta take cike fal... da matsanancin tsoro da fargaba rashin amincewar ak akan batun aurenta . zuciyarta ce tashiga bata karfin gwiwar bisa ga maganganun mahaifinsa gareta dattijon arziki da sanin
Chapter 77 · 0% Book details