← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 272 OF 289

Sashe 272

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

tsaye tare da basu guri ko hakan zai natsar da zukatansu. yana fita Ak ya mik'e tsaye jiki a sanyaye ya k'araso gabanta yana girgiza mata kai alamar ta daina kuka dan har lokacin hawaye bai bar tsiyaya daga ciki kwarnin idanunta ba duk da bataso hakan takasance daita ba. matsota yayi sosai har suna iya jiyo hucin numfashin junansu da yadda bugun zuciyoyinsu ke tsananta bugawa. ahankali yasa hannunwasa duka ya kamo fuskarta yana kallon cikin kwayar idanunta masu matukar kyau da hargitsa masa lisafi sannan yasa harshensa yana d'auke mata hawayen dake tsiyaya batasan sanda wani sabon kuka ya kufce mata ba, ya rungumeta tsam tsam ajikinsa suka fashe da wani irin kuka ya zagaye kugunta da hannun wasa ,ahankali yakira sunan daya saba kiranta dashi. "heart beat... wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki na zallar shaukinsa da muradinsa amman batayi yunkurin amsawa ba. yasan bazata iya amsawa ba kasancewar halin da take ciki, dan haka a kasalance yacigaba da sarrafa labbansa sai dai wannan karon complete name dinta yakira "su'adullahi kiyi hak'uri kiyi hak'uri da abubuwan da suka faru abaya banida laifi ko sanin abubuwa dana dinga aikata miki. " kiyi hak'uri ba laifina bane wasu lokuta da dama wasu abubuwa suna faruwa da mutun iri iri har yazamoto duk inda mutun ya juya zaiji babu dadi ballantana ni da'aka asirce ta hanyar sihiri "tundaga ranar da alkadarin abun ya karye ajikina kullun na kan zauna nayi tunani wai ni aka tagayyarawa rayuwa aka meidani mijin tace amman nasan hakan ma gwadani Allah yayi domin yaga k'arfin imani na. " nagode wa Allah da Allah ya juyar da mugun nufin me shi kansa. yayi shiru hawaye naci gaba da tsiyaya har gadon bayanta take jin d'inga hawaye sa "hawaye...? hawaye Abdul ke zubar akanta? "wannan wace irin rana ce me cike da abubuwa fariciki gareta? "Abdul na kuka akan abubuwan dayayi mata wannan itace rana ta farko data ga hawayen jarumi kuma gwarzon mijinta "am really sorry heart beat i swear to almighty Allah i don't know exactly what's happened to my brain komai ya tsaya min a daidai wannan lokacin bansan me nake aikatawa ba. Amman "Alhamdullahi a kullun ina k'ara godiya ga Allah, da ban sakeki ba acikin wannan halin ,da bansa yadda rayuwata zata muzanta ba.. ina matsanacin sonki su'ad rasaki cikin duniyata daidai ne da rasa komai nawa "please forgive me and forget what happened.. Ta d'ago kansa ahankali suna fuskantar juna cike da muryar kuka tace "ka daina kuka please ta kasa cigaba da magana . Amman a zuciyarta cewa tayi " duniyar da babu kai acikinta abdul tamkar kurkuku ce nima ina sonka mijina har bansa yadda zan ajiye mizanin sonka ba, koda ka sakeni cikin wannan halin sakin baiyi ba ,domin kuwa zan cigaba da kasancewa a matsayin matarka ne, domin a wannan lokaci kai da wanda baya cikin hankalinsa daya kuke dan hukuncin abu d'aya za'a yi muku ballantana baka furta kalmar ba sannan baka rubuta ba. Ajiyar zuciya ta sauke muryarta ta fito ahankali gurin cewa "yanzu ina Zeey take kuma awani hali take? shiru yayi ya kasa cewa da ita komai a halin yanzu data ambaci sunanta ,babu abinda yake jin yafi tsana kuma yake bakanta ransa kamar zanceta ayanzu . Ya kasa hak'ura da abinda tayi masa na kaskancin da wulakanci. Shi bazan ce wata banzar Zeey yayi especting ji daga bakinta ba, yaso yaji tana furta masa yadda tayi kewarsa amman takare da tambayar sa abinda yafi tsana. "kamin magana please tana ina ..? " kayi hak'uri kayafe mata karkace zaka d'auki mataki akanta. "kamin mgn plz... nan ma shiru yayi mata ya kasa cewa komai idan ransa ya baci ko yasoma baci baya iya magana ko kad'an haka kusan minti goma suna haka sannan yasoma mata bayani irin cin amanar da Zeey tayi masa da makomar abinda ta girba yakarasa maganar da "bazan taba yafe mata cutar datamin ba har karshen rayuwata.. "ka yafe mata Abdul, Allah nason bayinsa masu yafiya, sannan duk abinda tayi saboda sonka ne , kaunarka ce silar faruwar haka,dan Allah kayi hakuri ka ya.... tun bata karasa ba yayi k'ok'ari hade bakinsu guri d'aya, tayi saurin kawar da fuskarta tana sauke naunauyen ajiyar zuciya. Ahankali ta juya masa baya tasoma tafiya ta nufi hanyar d'akinta bai tsaya wata wata ba yabiyo bayanta koda yashiga d'akin ya isketa tsaye tana fuskantar mirrow wanda hakan bai katangeta da hango kyakyawar fuskarsa ba. a matukar sanyaye ya k'araso gareta ya manneta da kirjinsa yana sakin numfashi ,yayi shiru yana kallonta ta cikin mirrow kanta ta sunkuyar yace "heart beat a tunanina rabuwar da tashiga tsakaninmu, mun shiga tashin hankalin rayuwa na rabuwa da kusancin da mukayi amman tunda na d'aura idanuna akanki na gane ni kad'ai ke cikin tashin hankali Rashinki kusa dani . "amman babu komai a hakan ma"naji dad'in ganin yadda naganki cikin koshi lafiya. Ahankali ya dinga busa mata iskar bakinsa yana mata wani irin kallo ta cikin mirrow tare da kai hanunsa bayanta yasoma k'ok'ari zuge zip d'in rigarta har yayi k'asa da zip d'in idanunsa na kanta wani irin ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi tana runtse idanunta ahankali ya dinga shafa bayanta da bayan hanunsa zuciyarsa na harbawa ya d'auki wasu mintinoni yana mata tafiyar tsutsa abayanta sannan ya hadeta sosai da kirjinsa had'e da kai hannuwansa Duka daidai damtsen hannunta yana yawo da hannuwansa yana shashshafa mata sansar jikinta......
Chapter 272 · 0% Book details