← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 265 OF 289

Sashe 265

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* Dedicated To Hauwa A Usman Jiddar YA MUDHILL THE GIVER OF DISGRACE page 83 .........."duk da likitoci na iyakar kokarinsu akanka amman Habib yagaza hak'uri, gani yake kamar basu baka kulawa data dace , sati biyu tsakani ya shirya mana tafiya da kai zuwa wani hospital 'kwa'kwalwa dake k'asar india . ranar monday mukabar koria zuwa india inda kasoma karbar treatment daga k'wararrun likitici 'kwakwalwa, cikin wata uku ka warke garas. "Sai dai lokacin da kasamu lafiya sai ka dawo tamkar me 'kwakwalwa yara komai sai anyi maka gaba d'aya kulawarka ta dawo hannuna alokacin, haka Habib zai tasaka gaba yayita kuka ya dinga furta kalmar Alhamdullahi wato kowani bawa danasa kaddarar, gashi shi d'auke da cutar dake daf da kai shi kabari, kai kuma ga taka kaddarar ta juwewar 'kwakwalwa,ina son na dinga kiran ka da suna amman narasa da wani suna zan kiraka. dan haka na" cewa Habib mu samu sunan dazamu dinga kiranka dashi, dan shine farkon abinda zai saka ka dawowa aikata halayyan irinta cikakkun mutane. da fari Habib yaso mu dinga kiranka da sunansa acewarsa shi ba mazauni duniya bane, "watan wata rana zai tafi ya barni da kai, sunansa zai dinga d'ibe min kewarsa, nan take na tubure na nuna masa sam ban yarda ba wannan tsari ba ,ya canza maka wani suna babu abinda zai rabamu ciwo ai ba mutuwa bane sai ni nazo na mutu nabarshi a duniya ,shine da kansa ya zaba maka sunan Mahbub, a wani daren jumma'a muna zaune da habib byn na bashi ganinsa ya ya kira sunana" Shemah ...na d'ago ina dubansa alokacin kai idanunka na kanmu "ki rike Mahbub amana da gaskiya ina jinsa ajikina sosai ina jinsa tamkar wani jigo ne gareki ko ina raye da bayan raina ,idan mutun yayi wani alkhairi kansa yayiwa hakazalika akasin hk, sai kayi alkhairi ka manta agaba ka tsinci ribarsa, "ki dinga kallonsa amatsayin mutun me mahimmanci ga rayuwarki, irin irin zantuttuka Habib kenan gareni wad'an da suke maseefar kashe min jiki da narka min da zuciya har yasani zubda hawaye tausayinmu . "Aka sallamomu daga hospital muka dawo koria cike da tsantsar murna kasancewar kashiga ranmu sosai bayan kyakkyawar surar da Allah ya halicceka dashi, kai din wani hazikin mutun ne me kwarjini da kuzari hade da nutsuwar zuciya, alokacin na d'auki soyayyar duniya na d'aura maka tare da rike amanar da yayana yabani na kulawa da kai gaba d'aya na nemi son da na kewa Husein na rasa adalilin kasancewata tare da kai. "Anan koria ma lokaci zuwa lokaci kana zuwa ganin likita dan lokacin bama bacci sai kayita juye juye kana rike kanka kana ihu ,sannu ahankali ka dawo normal tamkar baka ta'ba samun matsala a kwakwalwar ka ba, in da muka cigaba da rayuwarmu har kasoma bin Habib office daga k'arshe ya d'auraka akan matsayinsa alokacin komai tare mukeyi duk inda kake muna tare wata irin shakuwa ce me k'arfi tashiga tsakaninmu wanda hakan yayi wa Habib mugun dadi dan jinka yake tamkar d'an'uwansa na jini karamcika da fara'arka da rik'on amanarka yasa Habib yi min sha'awar aurenka lokacin daya zo min da zance naso k'in amincewa lamarin, amman soyayyar danake maka taki barina kin amincewa . lokacin da mukayi aure Habib ya tattara duk wata kadarata ya damka maka ,har ma da wasu kadarori daga cikin nasa, ya d'aukaka acikin kasashen duniya duk wani abu da za'a yi da matsayinsa kai ke gudanar dashi duk wasu takardunsa dana wa ya canza suna zuwa sunanka. " alokacin da mukayi shekara d'aya da aure likita ya sake tabbatar mana Habib bazai wuce shekaru d'aya a duniya ba zai mutu hakan ya sake d'aga min hankali"nace idan rayuwarsa a hannunsa yake sai ya kasheshi " haka kace shekara daya data wuce bazai wuce shekara daya ba, yazo har ya dara hkn yanzu ma kazo da magana mutuwa duk maganarka bata wuce zance mutuwa, "kasani ma ko zaka rigashi mutuwa na dinga zakin doctor duk da lokacin gbdy a firgice nake daganin yanayinsa gaba d'aya komai masa ya sauya hatta tufafin sawarsa sun dawo farare bashi da abin yi sai neman istigifari da salatin annabi . "a lokacin da kai mukeyin komai gurin tattalin lafiyarsa koma nace kazama jigon komai domin duk abinda yaka mata nayi mishi ka maye gurbina, "gaba d'aya muka tattara al'amarinmu zuwa ga ubangaji wanda ba'a hanashi shine mai bayar da lafiya ga wanda yaso. "Allah bai rabani da d'an'wana ba har sai da muka rayu dashi na tsawon shekaru biyar sab'anin yadda likitoci suka sha gaya min. "mutuwar Habib ta girgiza zukatan mu ni da kai da sauran masoyanmu wanda gaba d'aya kusan rasa gane kaina kayi domin nima a sanadiyar haka na kamu da ciwon zuciya. "da taimakon Allah da taimakon ka naci g aba da rayuwa a duniya abu d'aya ke kwantar min da hankali a duk sanda na tuna Habib ya koma ga Allah yana me karatun alqurni me girma ana zarar ranshi amman sunan Allah yake ambato wannan abu shiyafi komai yi min dad'i arayuwata, har nasawa zuciyata danganar rashinsa atare dani. jinka tare dani ke d'ibe min kewar d'an'uwana danarasa sakamakon kulawar dakake bani, mutuwar Habib ta sake saka shakuwa mai k'arfi a tsakaninmu muka sake yarda da junanmu da zuciyoyimu cewar muna son juna da amana kuma zamu rayu k'ark'ashin inuwa d'aya muddin rai. " bayan wani lokaci kaima kayi suna ta kowani b'angare cikin k'asashen duniya ka gahurta har ma kaso kafin lokacin da Habib ke raye, "muyi zama na amana da soyayya a tsakanin mu wanda idan akace min wata rana zamu rabu zan k'aryata hakan sai dai duk wannan tsawon shekarun muna tare batare da wata matsala ba in ma har muna da matsalar arayuwar mu alokacin to bata wuce matsalar rashin haihuwa ba ...... "munyi zariyar asibiti munyi na gargajiya shiru dan haka muka sake rungumar junamu muka d'auki komai muka mikawa Allah. wanda ba'a sa shi kuma ba'a hanashi shine me bayarwa da hanawa ga wanda yaso d'an likitoci sun tabbatar muna da kowannen mu lafiyarsa lau, lokaci ne Allah bai kawo ba, shemah ta sauke naunauyen ajiyar zuciya lokacin datazo k'arshen labarin tare da tsura masa ido tana kuka me ta'ba zuciyan me sauraro,sannan tace "wannan shine tarihin rayuwata da kuma silar haduwarmu da kai. "kayi hak'uri koda baka sona kacigaba da rayuwa dani takarasa maganar tana me had'e hannunwan ta duka .. Ammi ta rungumeta ajikinta tana rarrashinta "kukan ya isa haka Shemah In sha Allahu ina me tabbatar miki zaki tabbata mallakinsa cikin inuwarsa har yanzu mijinki ne Taufeek da igiyar aurensa akanki. " Nasani Aunty ina jin tsoron karya ce bazai cigaba da zama dani ba "sannan meye matsayin wannan matar dayake ikirarin zai sake zuwa gurin mahaifinta akaro na biyu neman aurenta..... ? " ya tab'a aurenta ne suka rabu har yake tambayar ta cikin daya barta dashi..? "ni dai koma menene tsakaninsu Aunty ki taimaka yacigaba da rayuwa dani, Ammi tace "karkiji komai zai rayu tare daku "ita wannan da kika gani tsaye sunanta Salima itace asalin muradin ransa ,a duniya idan akwai abinda Taufeek yafi kauna da so bai wuce wannan bawar Allah dake tsaye a gabanki ba. soyayyarsu ta wuce na tsaya misalta miki, nan Ammi tashiga bawa shemah labarin Salema tundaga farko haduwarsu da Taufeeq har karshe da haihuwar d'iya macen datayi masa da yadda d'an cikinta ya aureta abu d'aya ne bata sanar mata ba shine batan su'ad shima dan kar kara masa dumuwa ne. wani irin kuka Shemah ta fashe dashi me tsuma zuciya "lallai ta cancanta yasota fiyye da komai a arayuwarsa "amman dan Allah ni dai sumin alfarmar cigaba da rayuwa dasu, na kasance a cikin inuwarsu, bazan shiga rayuwarsu ba burina nakasance tare da Taufeek araye, saboda bani da kowa a yanzu daya ragemin sai shi....... kuka take sosai har tabawa Salema tausayi ta isa gareta ta rungumeta suka rungume juna suna kuka. "ki bar kuka shemah zaki rayu da Taufeeq oredy ma taufeek naki ne" daman ni tuni na cire rai da rayuwa dashi ,zuciyata ta dade da hak'ura dashi kucigaba da rayuwarku kawaki kamar yadda kukayi a can baya nabar miki shi muddin rai.... shema ta rungumeta sosai "nagode nagode har bansa da wace kalma zan gode miki ba amman ki aureshi mu zauna tare.. shi kuwa Taufeek jin abinda Salima ta fad'a yasa komai ya tsaya masa tunani kala kala zuwar masa yake acikin zuciya har yaji gefen kansa yayi mugun sarawa "me salima take nufi da kalmar tabarwa shemah shi? abinda ma bazai ta'ba yiwuwa ba kenan yana raye tana raye yayi rayuwa dawata ba ita ba yayi mgnr cikin ranshi. daga can wani b'angare na zuciyarsa ke tambayarsa " anya ma kuwa zaka iya cigaba da rayuwa da shemah? "idan nace zan yacigaba da rayuwa da ita bazai iya yin adalci atsakaninta da Salima ba,domin kuwa Salimarsa dabance da sauran mata, bazai tab'a iya raba soyayyarta da wata ba ballantana a yanzu daya ji furuncinta me gauraye da tsagwaron kishi daga bakin Salima "wai ta barma Shema shi, kallo d'aya yayi mata yagane maganar ba daga zuciyar ta takeba iya baki ne kawai . tsawon lokacin ya d'auka tsaye yana kallonsu har sanda Doctor Rak yak'araso garesa ya dafa kafad'arsa yasoma masa magana cikin rad'a "ka zauna kasan baka gama wastsakewa ba tukun "kabi komai ahankali ta hakan ne kawai zamu samu sauk'in alamarin.. "Rak... Taufeeq yakira sunansa ahankali kamar yadda yasaba a tun farko wanda shine mutumin daya rad'a masa sunan tun a ganinyar kurciya. "kasa a sallameni ina buk'atar barin hospital d'in nan ayanzu gida nake buk'ata domin ina bukatar natsuwar zuciyar tunkaran mahaifin Salema ... ."an gama inji cewar minister lafiya wanda ya kamo hannunsa ya zaunar dashi akan gefen gado shi kuwa taufeeq da idanu kawai yake bin Salima dashi hankalinsa a matukar tashe gani yake tamkar ba Salimar sabace , me sonshi kalamanta sun tsaya masa arai matuka ya matsu ba'a zo an sallamesu ba .. misalin k'arfe takwas na daren ranar aka sallamo Prof Taufeek daga gadon asibiti, kai tsaye gidan Ammi sukayo dashi, akayi masa masauki a part d'in dake kallon na Ammi zaune yake abakin gadon ya nad'e hannu wansa
Chapter 265 · 0% Book details