Sashe 116
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ina kallonsa ina kuka me taba zuciya so nake naga ta ina zai bi sai naga ya kama karfen bancoy yana kokarin sauka ahankali ahankali kafarsa daya tana jikin bangon gidan dake zagaye da wayar wutar lantarki sannan yakama wata igiya ta bayan harabar gidanmu ya tafi kasa zuuuuuuu har ya kai kasa ina kallonsa ya sauka yana kakkabe hannunwasa tare da daga min hannu. wasu zafafan hawaye ne suka gangaro min sbd ganin yadda yake saida ranshi, akaina. na tabbatar da securities gidanmu sun ganshi a daidai wannan lokacin zasu iya harbeshi . da gudu na juya na koma dakina na sanya hijab nabiyo bynsa so nake nagamasa kar ya sake wannan kasadar amman ina karasa saukowa na nemeshi sama ko kasa narasa . nakarasa bakin get gurin securities muryata na rawa na kira sunansa john ko ka budewa boyfriend dina get? yace yes madam baki san da zuwansa bane? nace nasani ok yanxu ya fita sbd ke na bude masa amman alhj yahana . nace nagode sosai john batare da wata alamun tsoro ko fargaba ba nasoma kokarin bude karamin get din zan nufi waje. john ya dakatar dani yana bani hkr small madam alhj yace kar musake mu barki ki sake fita.... tsayawa nayi kawai ina kallonsa tare da daura hannuna bisa kai ina jin tmkr na kurma ihu hk ina ji ina gani nakoma cikin gida nakarasa dakina ina kuka nashiga nayi wanka tsarki . ranar bansamu isashen bacci ba tunanin magangun taufeek ne kawai ke yawo cikin kwalkwaluwata . yayinda zuciyata take bani karfin gwiwar binsa kasarsa wani bangare na zuciyata na nuna min illar aikata hk, duk runtse kar na sake nabisa na bar iyayena. a hk har bacci barawo yayi nasarar daukata cike da mafarkinsa barkatai. mgnr matsalata da prof taufeek ta bazu acikin dangina har hjy harira tasamu labari nan fa hnklinta ya tashi ta sake bazama cikin gari gurin bokaye da malaman tsubu akan batun aurena da yakub . byn taje gurin wani malamin tsubbunta yayi mata duba ya tabbatar mata da duk kina da son auran yakub sai anyisa domin akwai alkhari acikin aurena dashi har ma da rabo a tsakani amman duk da hk zai mata aiki me zafi akan mahaifina da sauran dangi ta yadda kowa zai sake yin na'am da lamarin . daren ranar data dawo ne daga gurin Boka jannat takawo mata ziyarar dare ta isketa tana waya da kawarta amadadin ta katse kiran sai cewa tayi ta zauna tana zuwa. wajen gidan taje ta wajen bayi tana cigaba da waya da aminyarta inda suka cigaba da tautauwa akan amarin hatsabibancinsu nan ne hjy saratu taji komai da duk yadda take hada tugu ta hanyar bin bokaye . hjy saratu batayi sanya ba tayi tattaki tun daga zugu xuwa cikin Cotonou tasamu mahaifiyata da zance abinda tajiwa kunneta sannan tabbatar wa mamma cewar atashi tsaye da addua domin tana ganin ko ciwon hjy babba tana da sanya hannu ciki . lokacin da mamma tasanarwa mahaifina kin yarda yayi da mgnr ya fututtuke ya hanata karasa mgnr wai hjy harira bata bin bokaye da malamai akansu. da mahaifiyata ta matsa masa da zance sai ma cewa yayi karta dameshi dan hjy harira bazata taba aikata hkn ba. dan hk karta sake zuwan masa da irin irin wayan nan zantuttuka marasa ma'ana da kan gado akwai wanda ya isa yayi bawa abinda Allah bai masa ba? mamma ta girgiza kai ala'mun a'a to karki sake tada zance idan ba hk ba zan saba miki. ita dai tabar zance a cikin zuciyarta amman tun daga ranar mahaifiyata ta tashi tsaye da Addua sosai akan hjy babba da mahaifina. shi kuwa taufeek gbdy kasar Cotonou ta fita masa arai zaune kawai yake cikin kasar baya jin dadin zama cikin tare da neman mafitar yadda zaiyi . zai cigaba da zama cikinta ne alhalin bamu tare ko zai bar kasar ne ya koma kasarsa yaje yaciga da rayuwarsa da matarsa da dansa zuciyarsa tabashi shawarar ya bar kasar kawai matsawar bai samu aurena ba. a wani zuwa ne da aminyata ramlat tayi byn munsha hirar mu daita wanda rabi hirar duk ta matsalata ce da taufeek da zata wuce ta bar min wayarta ta zare layin tunda ni tawa wayar tuni an karbe. dan hk ta nan muke mgn da taufeek dina sai mu kwana muna waya dashi batare da mun gaji da juna ba . tare da musayar kalaman soyayya . ni kaina ina jinjinawa yadda taufeek ke maitar sona da kaunata ban yi tsammanin yadda ya mallaki sirrin jikina zai iya cigaba da sona ba. amman kullun cikin nuna min kulawa da soyayya yake duk da babana yace bazai bashi ni ba amman yakasa rabuwa dani to acikin hirarmu yake sanar min da matsawar bai samu aurena zai bar kasar . ni km nake karfafa masa gwiwar zamu mallaki juna matsayin mata da miji. dan hk kullun muna makale a waya dashi ko what's app, tare da yin video cal amman yana yawon min complain kasar Cotonou ta isheshi sannan yayi dayasanin zuwansa salemat idan nasan zan hadu dake na kamu da matsanancin kaunarki mahaifinki ya hanani aurenki da koda billions of dollars bazan xo kasar nan ba. sai nace ya daina fadar hk sannan ya daina fidda rai da zamuyi aure irin irin wadan nan magangun dayake yawon fada min . wani lokacin nasa masa kuka sai km ya koma rarrashina wannan communicatio din da muke samu dashi yasa hankalina yasoma dawowa gangar jikina na fara samun natsuwa har iyayena suke ganin kmr na hakura ne da zance taufeek ne ba su san muna makale da juna ba. byn wata uku wanda yayi daidai da watana shida kenan a tsare agida batare da na leka koda kofar gidanmu bane ... taufeek ya sanar dani zai zo gidanmu akaro na karshe ya sake rokon babana sbd shi jibi zai bar kasar km bazai sake dawowa cikinta ba. jikina yayi sanyi amman naji dadin zuwan dayace zai yi gurin babana . ranar kwana nayi ina kaiwa Allah kukana. gbdy sai naji wata natsuwa acikin zuciyata amman yanayina ya sauya banda faduwa gaba babu abinda gabana ke yi.. washegari da yammacin ya iso gidanmu ina kwance akan gadona sanye cikin riga hamless fara sol da wando pencil jeans . na tufke gashina atsakiyar kaina naji wayata na babireting na mike zaune sbd nasan kowaye ya kirani . ina dauka nace ka karaso ne? yace gashi acikin compaund din gidanmu ki leko naga beaty face dinki tukun ko zan nasamu natsuwar fukantar babanki. na fito daga dakina na nufi babban parlour gidanmu inda bancoly dake facing din duk wanda yashigo harabar gida. na tsaya ina kare masa kallo daga samansa har kasa sanye yake cikin wasu haddaun kaya masu maseefar kyau da tsada wando baki da riga fara sol sai yar saman rigar me badadden gaba shima baki me dagon hannu iya gwiwa . kafafunsa sanye cikin cover shoe baki wanda ke daukar ido tsabar kyallin hkn yasa kyaunsa sake fitowa fili sai wani farin glass dayasa ya manne idanunsa dashi tsadadden murmushinsa ya sakar min nima murmushi nayi masa tare da daga masa hannuwana duka na hade babban dan yatsana da me bi masa, ala'mun yyi kyau. ya sake yin murmushi ina kallonsa yakira daya daga cikin securities yace ya masa iso gurin babana.. mu km muka cigaba da kallon juna, byn kmr minti goma sai ga john ya dawo yace masa ya biyoshi abaya suka shiga har parlour da babana yake zaune john ya kawoshi ya juya .nima tun sanda yabiyo byn john na koma ciki. " kai tsaye part din babana nayi nasam guri nesa kadan dasu na rabe batare da babana ya gani ba. da sallamar ya isa cikin parlour inda babana ke zaune yana shan coffee ya dago yana ganinsa ya hade rai sosai dan bai tsamaci shine yazo nemansa ba. daurewa yayi ya amsa masa sallamar aciki shima dan sanin mahimmanci sallamar ne tare da cewa lfy? prof taufeek yace itace takawo hk yabashi amsa atakaice dan zuwa lokacin taufeek yasoma jin haushi ko tsanar mahaifina ne ni dai bansani ba dan ko hira muke na sako zancesa yanxu ne zai nuna baiso tare da kawar da hirar take ni km zan nuna masa bacin raina. yakarasa ahankali inda mahaifina yake ya durkusa har kasa a gabansa yace barka da warhk baba ya gida ? cikin hade rai babana yace meya sake kawoka gidana..? wani irin fargaba da tsoro ne suka min diran mikiya suka caki tsokar dake makale da kirjina wanda yasa kadan ya rage fitsari bai kufce min ba take km jikina yasoma rawa rawa . "kayi hakuri bisa sake zuwa gidanka danayi na sake dawo ne bisa kudirina na son auren salemat agurinka ,bazan gaji da rokonka ba baba sbd ina matukar son diyar cikinka ...so km irin wanda da wuya asamu a irinsa a duniyarmu ......... dakata babana ya tsaida shi da hannunsa take ni km gabana yashiga duka uku uku na dinga nasoma kokuwa da numfashina nashiga karato duk adduar danasani domin samun nasara . amman fa kallo daya zaka min ka tausayamin gani arakube amman wani irin kirrma jikina keyi na tashin hankali sautin muryar baba naji ta karade parlour 'n ina ganin kmr ka manta abinda nasar maka akan diyata ...? amman bari na sake maimaita maka dan hk ka bude kunnuwanka da kyau ka saurareni salema "ya"ta nayi mata miji so kana iya tafiya kabani guri .. shiru ya ratsa parlour na wani lokaci can taufeek ya dago idanunsa yana kallon mahaifina cike bacin rai mara iyaka sannan yasoma mikewa tsaye bai gama mikewa ba. na bayyana gabansu ina kuka wiwi wanda kukana ya janyowa hankalin mutane gidanmu suka firfito gabadayansu har da yayyena da suka kawowa mamma xiyara da matansu. na hade duka hannuwana guri daya ina juyasu tmkr yadda yara kanana kanyi idan 'sum shiga tashin hankali nasoma mgn cikin muryar kuka wayyohhly babana karki min hk kayi hkr dan girman allah kabarni na aure taufeek ..ina sonshi bazan iya rayuwa babu shi ba karka Hanani aurenshi shine farincikina na isa gurin mahaifiyata mamma dake tsaye zugun tana kallona cike da tsusayi kisaka baki mamma kar