← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 289

Sashe 119

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya mike jikinsa a sanyaye yabaro zugu. .... .koda ya dawo daga zugu bai yi gigin sanarwa mahaifiyata komai ba dan yasan idan yasanar mata yadda sukayi da hjy harira rigama kawai za'a yi agidan . sai dai ya tmbyeta ko na bude dakina tace masa a'a.... washegarin ranar ta biyu da faruwar abun na gwada kiran layin taufeek cikin sa'a number'sa tashiga yana dauka na sakar masa kuka yayi shiri N wani lokaci sannan yace isa! ya isa!! my louloooo dan Allah salema kibar kukan nan hk . kukanki bashine mafita ba idan kina irin wannan kukan ya kike son ni nayi da tarin damuwata.. ? nafiki shiga damuwa kasancewar soyayyata tafi taki karfi . kuka nake sosai har da shesheka nace taufeek ina cikin bakincikin rashinka dole nayi kuka wanda nasan har karshen rayuwata da kukan rashinka zanyi . kiyi hkr nima ina cikin bakinciki kwarai da gaske akan cewa bazaki zamo matata ba. nasan km zan kasance cikinsa har abadan duniya, kenan har aranar da rayuwata zata zamo the end salemat ina sonki ..ina sonki so na tsakani da Allah amman gashi ina ji ina gani babu yadda zanyi na mallakeki yakarasa mgnr yana jan numfashi kana yayi shr amman ina ki san wani abu bazan taba son wata diya mace kmr yadda nake matsanancin kaunarki ba. da mahaifinki zai yarda yabani auranki da zan zame masa tmkr bawa garesa . ko matsayin me gadin gidansa yabani zan amsa matsawar zai bani aurenki .. kece farincikina....zan bar kasar da tarin tunaninki da kewarki.. kece muradina samun mace irinki a wannan lokacin yana da matukar wuya kece sarauniyar zuciyata. hk ya dinga gaya min word' world masu dadi da taba zuciya ni km ina kuka tmkr raina zai fita har daga karshe ya kashe wayarsa tare da yi min sallama . ****** tsawon sati daya kenan da faruwar tashin hankali dana tsinci kaina ciki gari zai waye dare yayi ina cikin dakina kwance kusan kwanaki 4 kenan da suka wuce wanda lisafina taufeek ya dade da barin kasar sbd duk kwanakin cikin kiransa nake number'sa batashiga. yayinda kwanciya ya zamemin abinda nafi so da bugata alokacin ,idan na kwanta har bana son tashi ko kwakwarar motsi nayi zuciyata manne take da tunani taufeek tare da tuna momment din da mukayi spend tare da shi. hk zan dinga jin hannunsa na yawo ajikina duk inda na motsa. kiran sallah ne kawai ke tadani dan ta abinci ma na manta rabona daya shiga cikina . rabona da abinci tun wanda naci ana gobe taufeek zai zo gidanmu . dan randa zai zo ma kasa cin komai nayi sbd fargabar abinda zai faru. hjy harira ganin yadda mahaifina yasameta da zance fasa aurena da yakub yasa ta sake tashin hankalinta . "ta km bazama gurin bokayenta da malaman tsubu sannan ta bawa yakub din umarnin yasoma zuwa gurina zance byn sake jaddamasa kudinrata akan aurena datake son yi tunda tun farko tasanar Masa kasancewar shima makiri ne irinta bai nuna mata kin abin ba sai murna dayayi .wanda shi daman ya dade da kamuwa da matsanancin kaunata. ranar farko dayazo gidanmu gurina bai samu ganina ba, sbd ina dakina a kulle mamma ta tareshi cike da karramawa da mutuntawa sai dai fuskarta babu yabo babu fallasa. ya tmbye ni mamma bata boye masa komai ba tace yayi hkr bazai samu damar ganina ba sbd kwanana bakwai kenan adaki a kwance na kulle kaina na hana kowa ya ganni . yayi shr yana sauraronta can km tace tana xuwa bari ta gwada tagani ko zan bude. byn kmr minti 5 sai gata ta dawo tace yayi hkr naki budewa . wani bakin ciki ne ya kama kahon zuciyarsa ya tokareshi tagumin bakinciki yayi sbd yaxo da maitar son ganina dan ko abinci da mamma takawo masa ma bai ci ba ya bar gidan ransa abace. akwana na goma ne iyayena suka sa aka balla musu kofar dakina wanda zuwa lokacin na galaibaya iya galabaita na fita haiyacina numfashi ma da kyar nake iya janyowa . ai Suna ganin halin danake ciki kuka suka saka ina kallonsu da idanuna dake lumshe . "duk kawaici irin na mamma sai data kalli tsabar idanun babana tana kuka tace idan kabari wani abu yasamu yarinyata bazan yarda ba.. dawood ...zan cire zumunci da auren dake tsakanina da kai nayi kararka xuwa court dan bazan zauna ina kallo ka nemi kashe min yarinya ba sbd farinciki wasu ... ban taba ganin bacin ran mamma ba sai s ranar ta inda take shiga ba ta nan take fita ba .gama mgnrta ke da wuya ta juyo kaina tana tabani cikin muka take kiran sunana sai gani tayi jikina ya sake na sume... hankalita ya tashi ta juyo ahargitse ta cakumi wuyar rigar babana tana ihun tana kukan ya kashe mata ni . da kyar wata yayar babana datazo duba jikin hjy babba tashiga tsakaninsu . aka kira likita yazo gida ya bani taimakon gaugauwa tare da daura min drip . a dan tsakankanin wannan lokacin mahaifiyarta da yan'uwana basa nesa dani kullun cikin rarrashina suke da bani baki . "abinci ne agabana mamma tana rarrashina naci amman naki sai dan ruwan shayi dana soma sha . tun daga ranar da mamma tace min yakub yazo gurina bai sake takowa gidanmu ba. ni km kuwa nayi kudirin koda ya dawo bazan bari yaganin ba. yayinda hjy harir ta sake banko wani sabon tasiri me zafi ajikin mahaifina dan hk wata rana mamma na zaune a parlour ya dawo gida a hargitse yake sanar mata da za'akawo kayan aurena tace yanzu bazaka bar zance auren nan ba? Kai tsaye yace mata eh idan an daura auren na mutu. kwasam ina parlour akwance naji sautin muryar mutane nashigo cikin babban parlour gidanmu wanda duk wancin yan'uwanmu ne dan na dauki muryoyinsu wai sunzo kawo kayan aurena da yakub . ina kallon lokacin da mamma take musu alama da suyi shr amman ina nagama sauraronsu na mike tsaye ina layi kawai sai gani sukayi na zube kasa na sume . hankali kowa ya tashi akayi hospital dani wanda likitoci sukayi tsaye akaina domin dawo dani haiyacina amman numfashina yaki dawowa sai da aka manna min isar oxygen domin taimakawa numfashina yayinda mamma da ssuran dagin ke gefena cikin fita haiyacinsu da shiga tashin hankali lokacin dana dawo haiyacina aka canza min daki. satina biyu a hospital aka sallameni muka dawo gida wanda har lokacin bangama dawowa daidai ba. kwance nake adakina cikin matsanancin tashin hankali tun danake atsawon rayuwa ban taba fuskatar irin tashin hankali danake ba alokacin . idanuna sukayi luhu luhu suka zurma daman ga uwar rama dana sakeyi dan gbdy na zabge na dawo wata irin dani sai kashi nayi kuka har nagaji. itama mamma tayi kuka har ciwon idanu sukayi nasarar kama idanunta tana zaune tana kallona tmkr matacciya . surutai take ahankali zuwa lokacin tace batasan me taufeek yayiwa tilon diyarta kwaya dal a duniya ba wanda yasa ta shiga wannan halin . ina sauraronta har tagama sambatunta amman hankalina bai gareta bare nace mata wani abu . har zuwa sanda yayyena suka shigo dakin jikinta har rawa yake gurin ce masu anya kuwa yaron nan da salema ke mutuwar so bawani abu yayi mata ba? soyayyar datake masa yasoma bani tsoro. yaya yusif ne yayi karfin halin cewa babu abinda yayi mata kawai dai tata kalar soyayyace tazo mata da zafi. ahankali naji mamma tace ban yarda wannan soyayyar ta wuce ace babu abinda yayi mata takarasa mgnrta tare matsowa sosai inda nake kwance tmkr matacciya ta kamo hanuna cikin nata tare da kiran sunana mamana ki sanar min ko taufeek yabaki wani abu ne alokacin da kuke soyayya musan yadda zamu bullowa lamarin? nayi shr naki cewa komai. tacigaba ko km kunsha jinin juna ne kedashi ki gaya min ni mahaifiyarki ce ko kowa yakiki ni ina tare dake ki gaya min inda akayi aikin muje akarya ki dawo haiyacinki . na ma shr duk da bakina nason tanka mata amman na kasa bude labbana da suke a bushe. ahankali nasoma samun sauki kadan sbd kulawar danake samu daga mamma . dan gbdy kauracewa mahaifina tayi. " ta dawo dakina tare muke bacci daita tana kula da yanayin , wani lokacin idan taga nashiga damuwa sai tasanyani ajikinta wai naji tumin jikinta ko zan dawo daidai. alokaci su'ad idan akace miki nice wannan matashiyar salemar me cikar halitta da kyau zakice karya ne sbd muguwar ramar danayi kirjina har wasu mugayen katsutsuwa ne suka bayyana step by step.. kallo daya zaka min kasan ina cikin alhini da tashin hankali. ciwona bai hana mahaifina soma shirye shiryen bikina da yakub ba dan har ankawo komai daza'a bukata agurin biki . hatta kayan daki ya kammala anje anyi jere anyi komai wanda kusan duk dagin mahaifina ne ke tsaye akan komai dan mamma na tare dani taki yarda tashiga cikin sha'anin bikin. yadda bani son auren da yakub hk itama take nunawa dangin mahaifina bata so har rigama yaso shiga tsakaninta da mahaifiyar yakub. sai da manya suka shiga tsakani. yayinda ni km hankalina ya sake tashi nashiga tashin hankali mara misaltuwa fiyye da lokutan by na kara ramewa sai dai nayi wani irin fari na dashe kmr wace bata da jini jiki sannan sai alokacin nake sake tabbarwar kaina da gaske dai narasa taufeek har abada. take ciwon sonshi ya motsa min ya dawo min sabo fil . barin lokacin da magangagunsa suka dinga dawo min daki daki kibini mutafi kasata muyi aurenmu acan zan zame miki komai zan soki zan baki kulawar data dace bazan taba cin amanarki ina kawowa nan jikina yasoma rawa rawa kafin kace me wani zazzzafan zazzabi yayi nasarar rufeni na dunkule kaina adaki na lullube cikin bargo duk hayaniyar da'ake acikin gidan ina ji wanda hkn ke karawa zazzabin jikina tsamari ranar dai sai da muka dangana hospital naga likita. byn mun dawo daga hospital nashiga tunanin mafuta nakarasa inda jakata dana saka diary da taufeek yabani ya dauko har na juyo da niyyar fito da diray nakaranta abinda yake ciki . najiyo takun shigowar mamma dan hk na nade jakar da sauri ta turata cikin wata yar karamar akwatina
Chapter 119 · 0% Book details