Sashe 254
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
YA BASIT THE EXTENDER page 80 Ta kowane bangare ammi bata saurara da adduoin dinta da sauke sauken alqurani me girma har ma da sadake sadake tanayi domin yayewa d'anta duhun dayake cikin har ma tana kwadaita masa yin sadaka a duk sanda akaci sa'ar yakirata ta waya . Yayinda Duk sanda zeey taga ak yana sadaka ta dinga tuhumarsa dalili yin sadaka shi kam a kullun amsar dayake bata, bata wuce sadaka ga dukkanin muslimi abu ne me kyau musamman idan Allah ya horewa mutun abinda zai bayar din, wannan abu yana matukar daga mata hankali barin data sanarwa bokanta yace yin haka tamkar yana yaki ne da tasirin sihirin dake jikinsa ne dan tayi kokari towani bangare ta toshe hanyar yin sadaka garesa hakan ce takasance duk wanda yazo gurinsa neman taimako sai tasan yadda tayi ta hana . acikin wannan yanayin ak ya tsinci kansa cikin matashi wadan yasamu cigaba arayuwarsa ta fannin kasuwacinsa na gida Nigeria da sauran kasashen ketare ,a yadda duniya ta zauna ta zanta akan wad'an da suka samu cigaba a harkokin kasuwancinsu da shahara gurin arxi, sun tantance ak shine yakasance mutun na biya acikin masu kudin duniya wannan abu bakaramin faranta ransa dana iyayensa yayi ba . dan haka ma nema labarai suka dinga bibiyarsa dan son hira dashi . Yabawa ait ranar da zasuyi hira dashi inda sauran yan jaridu suka riskeshi can dan daukar rahoto ya fara ne da gabatar da kansa sannan d'an jaridar ya watso masa tmbyr cewa "ranka ya dad'e sir amatsayinka na matashi me Karachi shekaru acikin manya attajiran duniya , yaya ka tsinci kanka lokacin da duniya tasanar da kaine mutun na biyu acikin masu kudin duniya ? Cikin sanyayyiyar Muryarsa me shiga jiki da tsayawa azuciyar duk wanda ya saurara yasoma magana cikin harshen kwararen turanci nsa "alhamdullahi naji dadi sosai da wannan cigaba danasamu arayuwa . d'an jaridar ya sake cewa watso masa wata tmbayar ranka ya dad'e " yaya katsinci kanka acikin wannan matsayin ? Yayi gyaran murya sannan ya yacigaba da cewa"ina godiya ga Allah daya kaddaromin kasancewata daya daga cikin masu rufin asiri na duniya gbdy wanda mahaifina da mahaifiyata sune silar komai gareni dana zama ayau ,bisa jajircewarsu naganin sun d'aura bisa tsari me kyau sai kuma uban gidana sir mahbub wanda shine yakasance na daya acikin masu kudin duniya shima ya taimamin takowani bangare wanda hakan yasa nake jinsa tamkar wani jigo ko uba gareni .. Dan jaridar yace ranka ya dade muna godiya sosai sai dai zamu so musan adadin ma'aikatar da ka mallaka na gida dana sauran kasashen ketare sannan muna son mu san abubuwan da'ake sarrafawa acikinsu ?. Ak ya numfasa sannan yacigaba magana "ina da tarin maaikata wanda tsayawa fad'arsu zai dauki lokaci sosai ,sai dai zan fadi kad'an daga cikisu ,akwai addas company wanda ake sarrafa duk wani nau'i na kayan sakawa daga manya har zuwa na yara kanana ,akwai toyos mother wanda ake sarrafa duk wani nau'i na kayan wasan yara da mother's care haka dai ak ya dinga lisafo company's dinsa daya baya har sanda yayi rabi sannan ya daka tare da cewa d'an jaridar "wani lokacin idan irin haka ya kasance zai gaya masu sauran . d'an jarida ya sake ce wa ranka ya dad'e idan bazaka damu ba zamu so ji ko kana da aure ko akasin? Idan kana da aure matanka nawa sannan yaranka nawa? Ak yayi shiru take kuma zuciyarsa ta hau dokawa da sauri sauri kusan 2 second yayi yana tinanin abinda zaice sannan yasoma magana "ina da aure kuma matana biyu zance haihuwa ne dai har yanxu Allah bai bani ba kutun sai dai ina adduar samuwar haihuwar daga mace tagari .. D'an jaridar yace "Allah azirta ka da samun masu albarka ,"sai dai wani hanzari ba gudu ba, ranka ya dad'e munji rad'e rad'in cewar ka saki matarka ta biyu meye gskyar labari ? Sai daya furzar da iska ta bakinsa bayan kirjinsa daya tsananta faduwa haka kawai ya tsinci kansa da cewar " zan gsky ni ban saki matata ba duk wanda yace na saketa karya ya gaya muku ..yana kaiwa nan gbdy yaji hirar ta gunduresa . D'an jaridar yace "mun gode kwarai da lokacinka daka bamu . ak ya amsa da" nima na gode matuka . labarai hirar ak ya watsu a gari dan haka abokansa suna ta zuwa tayasa murna ciki kuwa har da sakon akil daya aiko masa acikin farar takadar . _inda yake cewa abokina ina alfahari dakai ina matukar tayaka murnar kasancewa daya daga cikin masu arzikin duniya Allah yasanyawa arki albarka daga abokinka wanda ka share babinsa arayuwarka ._ ak yakaranta sokon daga farko har karshe ya kasa gane kowaye wanda ya turo masa kasancewar babu sunan wanda ya rubuto sakon ya nad'e farar takadar ya tura cikin envelop ya ajiye a saman mirrow dinsa wannan matsayin da ak ya taka yasa zeey murna har take jin ta zarta kowace irin mace a duniya. Daren ranar ya tsinci kansa da son zuwa gurin amminsa misalin karfe goma na dare zai fito daga cikin dakinsa ciki shigar kanana kaya ta isa dakinsa da sauri takarasa jikinsa ta rungumeshi ,tace my life yanaga baka cikin haiyacinka? Bai kulata ba yasoma kokarin zareta daga gangar jikinsa takara matsoshi sosai tace "my life magana nake maka ina zakaje da wannan lokacin ? Ya tsura mata mayatattun idanunsa har sai da kayan cikinta yamutsawa kawai ya tsinci kansa dakasa kin amsa tmbyrta ,ya daure yace "yace gurin ammi . "Ammi ta tmbyeshi a rude yaushe rabon ko waya yayi daita bari yaje gurinta . Yace "eh gurinta zani " "Me zakajeyi gurinta da daddaren nan kamata yayi kabari sai gobe kaje tunda har yanzu akwai masu zuwa tayaka murna yacigaba da dubanta yana kokarin matsawa daga gareta amman sai da tasan tsiyasar datayi ta hanashi zuwa ta hanyar tsafinta . Wannan sabon matsayin dayasamu yasa ak yawon tinani sai ya zauna kawai yayi shiru da farkon ta dauka ko tarin gajice tayi masa yawa ,kwasan ta tsinci hirarsa daga ait inda yake cewa yana da aure matansa biyu har zuwa inda yace bai saki matarsa ba jikinta ne ya d'auki rawa daga zaunen datake , sai kuma kawayenta suka soma kiranta suna gaya mata abinda suka ji a tautaunawar mijinta wasu suce ga tashar da suka ji wasu suce jaridar daily trust ga abinda yace . Babu shiri Cikin rawar jiki ta iskeshi a d'akinsa ta sameshi zaune kafarsa daya kan stool dayar kuma a 'kasa yana jijigata ya runtse idanunsa sosai yayi zurfi cikin tinani ta isa garesa da sauri ta dafa kadarsa game da kiran complete name dinsa "abdulkabir?ya bude mayatattun idanunsa ahankali yana dubanta tacigaba da mgn "yaya dai meke damunka ? Gbdy ma ganin yanayinsa yasa ta manta abinda yashigo daita d'akin... Ya d'an gyara zamansa sannan yace "me kika gani ? "kwana biyu ka zama wani shiru shiru gashi ka matsawa kanka da wayon tinani wanda na rasa dalilinsa adaidai wannan lokacin kamata yayi ace kana cikin farinciki da walwala kazamo daya daga cikin masu kudin duniya bawai ka zauna zaman saka kanka cikin damuwa ba , aransa" yace farincikin me zanyi arayuwa byn ina ji araina narasa abu me mahimmanci atare dani. a zahirance kuwa murmushin karfin hali yayi tare da fadin "nason yin haka din Amman sai dai na kasa ni kaina bansa meke damuna ba , bansan abinda nake yawon tunawa ba nasan dai ina ji ajikina nayi Missing wani abu me mahimmanci arayuwata .. "Mene shi wannan abinda kayi Missing arayuwarka alhalin gani atare dakai ? Tayi masa tmbyr muryarta na rawa rawa ,ya daga kafad'unsa duka sannan yace "oho abinda ni kai na nagaza ganowa kenan sai dai na kan zauna na zurfafa tinina ko zan gano ita kuwa zeey zama tayi kusa dashi ta janyosa jikinta tace "haba my life my dear husband karka damu kanka da wannan tinanin ,yawon tinani yana daga cikin sharin shedanun aljanu, kasan wannan d'aukakar daka samu zata iya yiwuwa wasu nabinka da mugun alkabai . shi dai jinta kawai yake haka yasanya jikinta sake yin sanyi sai ta sake akalar hirarta danaji cikin hirarka kace baka saki su'ad ba meye gskyar lamarin? Duk da sanda yaji ta fad'i hkn sai dayaji kirjinsa ya buga amman yasanyawa zuciyarsa kuzarin sannan ya bude bakinsa da kyar yace "Eh na fadi haka manufa anan kinsa yadda yanjarida suke yanxu ina gayamasu gsky su ammi zasuji tunda Shirin kai tsaye ake d'auka . "Ok yanzu naji batu amman duk wanda ya sake tambyarka karka sake boyewa dan boyewar bashida amfani yayi mata shiru yaki cewa koma tacigaba "yaushe ne bikin eiman ne? "Dan ya dace ace zuwa yanzu munsoma shirye2 kaga dai kai ne babba yaya ..ya kalleta kawai yana jin haushinta tundaga kasan xuciyarsa shi kansa wani lokaci zai zauna yana tinanin yadda akayi ya aureta . "yauwa my life ya zance kudin dakace zaka bani yakamata ace kabanisu tun yanzu ga shirin bikin eiman ga kawayena suke zuwa min taya murna kuma ya.. atsawace ya dakatar daita dan Allah ki barni hk kaina yanasoma ciwo plz get out zeey ina bukatar hutu yakarasa mgnr yana nuna mata hanya fita da hannunsa .hankalinta ya sake tashi matuka jikinta yasoma rawa rawa taso cigaba da magana amman sai taga rashin faidar hakan ta mike da sauri ta nufi dakinta tashiga tunani daga karshe zuciyarta tace yamata ta kaiwa bokanta xiyara . Wajen sati biyu kenan bata samunta a waya kotakirata bata samu tace zata gidanta ta dubata tagani ko lafiya shiru babu alamunta ko jin duriyarta ,yau dai da hidimomi suka mata sauki tace yazama dole taje gidanta nan da nan tashiga motarta ta fice tun daga kan farkon shagonta wanda take aikin nurse dinta ciki tasan akwai matsalar dake faruwa da kawarta domin kuwa koina kazan kazan har wani wari wari yake tashi daga cikinsa da sauri takarasa shigewa cikin shagon sosai "wai ina kike ne kawata meke faruwa dake ne ? Ganin bata parlour'n kai tsaye tayi uwar d'aka inda nan take aikin cirewa mutune ciki abortion, can bisa d'an karamin gadon da marasa lfy ke kwanciya ta isketa kwance da sauri takaraso gareta tace