← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 285 OF 289

Sashe 285

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

had'a da baba hauwa me aikin ummanta zata fito "a'a hjy barka da zuwa kece da tsakar rana hk sannu da zuwa ina kika baro mana ya.. ai ganin hawayen dake bin kuncinta yasa baba hauwa saurin yin shiru can kuma taga yinka janye da akwati tayi saurin ja da baya tana adduar Allah yasa dai lfy.. karasawa su'ad tayi ciki batare da tacewa baba hauwa komai ba. ita kuma baba hauwa tayi bayanta da sauri yinka na shigo da akwati parlour'n ita kuma tana shigar dashi d'akin umman su'ad sai datagama shigo dasu sannan ta baro d'akin tana tunanin abinda yasata kuka irin hk. umman su'ad na fitowa daga cikin bayi taga su'ad zaune agefen gadonta tana hawaye, take gabanta yashiga dukan uku uku da hanzari takaraso gareta tana tmbayarta "ke lafiyar waye ya mutu kike kuka hk? wani matsanancin kuka ya sake kwace mata hakan yasa hankalin umma ya sake kololuwar tashi ,jikinta yasoma rawa rawa "wai me faruwa dake ne ki gaya min tun kafin damuwar wannan tashin hankali dake tattare dake ya bugar min da zuciya. "cikin wata irin muryar tace"babu komai "bangane babu komai ko abdul din sakinki yayi ne? cikin kidima umman su'ad tayi mata tbmyr idanunta na kan akwatin kayanta dake jere gefe guda. "da sakina yayi dana jin dadi. sanyayyiyar ajiyar zuciya umman su'ad ta sauke jin ba sakinta yayi ba sannan tace. "kul kar na sake jin kin ambaci wannan kalmar, da Allah ke fushi da duk macen data furtashi ga mijin aurenta, mailaku rahma na tsinewa duk matar data bukaci saki daga mijinta, kada ki kasance daya daga cikin irin wad'an matan. "ni mahaifiyarki ce danayi silar zuwanki duniya nice mutun ta farko da yakamata ki gaya matsalarki but ni din ma bance ki gaya matsalar data shiga tsakaninki da mijinki ba. "su'ad kiyi hkr kowace mace dakika gani hakuri take agidan mijinta, sannan babu macen dazatace bata da matsala ko ta'bon da nmji ,bazan so ki kashe aurenki kizo mu zauna guri daya ba. muryarta cike da matsanancin kuka tace "Allah bazan iya cigaba da zama da mutumin da bai san darajar iyayena ba.. take umma ta fahimci inda zanceta ya dosa "karki ce min akan abinda ya faru last week kikayo yaji.? su'ad ta d'aga kanta ala'mun eh, umma tayi shiru tana dubanta duk da matakin data d'auka ya sanyaya ranta ,amman bata so ya jin datayo ba ,saboda gudun abinda zai faru gaba ,"wannan zuciyarta ta mijinta komai zai iyayi. hawaye suka ciciko idanunta tayi saurin meidasu dan kar su'ad tagani hankalinta ya sake tashi. ganin yadda hankalinta yake a tashe yasa umma kyaleta tacigaba da kukanta har zuciyarta tayi sanyi , rarashinta tayi sosai byn tayi shiru tace. "yanzu ina kika baro yaran? "suna gurinsa " "bari naje na kawo miki abinci amman bai kamata ki baro yaranki ba sunyi kanana dayawa uwa kad'ai ce tasan yadda zata kula da ya'yanta ,da ko karamin ki riko takarasa mgnr tana ficewa daga d'akin . kasa cin abinci da umman takawo mata tayi illa kashe wayarta datayi tasamu guri tayi kwanciyarta a saman gado, sai lokacin tunani barin yaranta datayi yazo mata datasani ta taho da ko karamin d'anta ne. kusan awa biyu da tafiyarta yana nan zaune agurin bai san abinda yakamata yayi ba har yaran sukayi bacci ajikinsa. ahankali ya mike ya kaisu bayan motarsa wanda hkn yasa suka farka daga bacci dan daman bawani dadewa sukeyi a bacci, yana kokarin shiga mota escort dinsa suka taso da sauri , d'aga musu hannu yayi ala'mun suyi zamansu sannan yashiga motar yabar gidan. kai tsaye gidan musty ya nufa tun a mota yakirasa "yace gashi nan zuwa yana isowa kofar gidan yakirashi ,can kmr minti biyu musty ya fito rungume da diyarsa fadela ya mika masa hannu suka gaisa "lafiyar nagan kayi wani sukusuku dai kai? "ina fa lafiya wannan shagwababbiyar yarinyar ce ke nan caja min kwakwalluwa da daru. ya fito daga cikin motar tare da yaransa suka shiga cikin gidan. a parlour baki suka zauna byn yasanarwa eiman da xuwansu, eiman tashigo parlour'n sanye cikin bakar doguwar riga har k'asa hannunta rike da tire tana murmushi ta karaso ta ajiye akan center tabble idanunta na sauka akan yaran tace "kai kai marahabun da manya baki yau ya'yana ne agidan..? sannuku da zuwa ,"zo nan mamana yanaga duk ranki a'bace me yasameki a baki takoma hannun yarinyar tare da zama gefen mijinta tana sake fad'ad'a murmushinta sannan tace "yaya ina wuni ya su'ad take? "tana lfy ya amsa mata atakai ta mike tsaye byn sun gaisa ta amshi emran ta sanya yaran gaba sukayi ciki domin basu guri sun zanta. byan fitar eiman musty ya gyara zama "uhm abokina ina sauraronka me ya had'aka gimbiyar taka ? "ak ya zayyano masa abinda ya faru tun last week zuwa yau din nan shiru musty yayi ya k'asa cewa komai ya tsura masa ido dan lamarin ak yafi karfinsa "gsaky aboki baka kyauta ba "maza tashi muje biko tun abun bai girmama ba. "kabarta kawai friend yanzu haushina take ji ko muje ma ba sauraranmu zatayi ba mubari zuwa wani sati ,zuciyarsa kuwa fad'ar hk yayi ba dan yana jin zai je wani biko ba. nan suka cigaba da tautauna yadda lamarin zai kasance da zai tafi eima tace yabarsu farhan tunda hutu ake ranshi bai so ba amman babu yadda ya iya hk yabarsu ya wuce . koda prof taufeek ya dawo umman su'ad ta sanar dashi abinda ya faru "yace su'ad tayi daidai hk ake son d'a me kishin iyayensa wannan mataki data d'auka zai sa shi mijin yagane iyayenta na da mutunci agurinta ,dan haka bazan takuramata ba, idan taji tana iya cigaba da zama dashi fine, babu ruwana idan kuma bazata iya ba ni me tsaya mata ne ta amshi yanacinta agurinsa . "bai dace kace hk ba kodan darajar aunty. "shi abinda yayi ya dace ? "idan bai duba darajarki na sirikarsa data bashi auren diyarta har da yara guda uku tsakani, yakamata ya duba darajata amatsayana na kanin mahaifiyarsa . "idan shi akayiwa tashi uwar zai ji dadi? umman su'ad ta bud'e bakinta kennan zata sake yin mgn ya d'aura hannunsa akan bakinta "banason na sake jin komai daga bakinki ki xuba idanu kmr yadda nima zanyi "shikena idan ka gama abinci ya kammala "bar zancen abincin nan ki matso kusa dani akwai abu me mahimmanci danazo muki dashi.. ta hararesa" kai haba yallabai wai bakasan ka tsufa ba "wani tsufa ki matso bakisani ba ko adduarmu ta kar'bu muyi d'an kanmu yau kinga shikenan mun huta da... "dan Allah kayi shiru kar wani kunne yajika "haihuwa yanzu gotai gotai dani, ina haihuwa diyata na haihuwa" haba yanzu fa mun Tsufa da wata haihuwa, duk abinda zan haifa nabarwa su'ad," bazan iya da wannan kayan kunyar ba "kece kike ganin kmr mun tsufa da haihuwa. "ina gani fa yar yarinya karama zan bari asamomin na aure abata tayita haihuwa tunda keda shemah har yanxu shiru "wallahi ni nama fijin shemah adduar danake mata kenan kullun ko guda daya ne Allah yabata tasamu abokin shawara.. musty yaji shiru shiru ak bai sake masa zance zuwa gurin su'ad ba, ya same shi zaune acikin office dinsa yana operating system "aboki najika shiru baka sake yi min zance ummul ihsan ba alhalin nasan abin yana damunka.? "wallahi kamar kasani lamarin na mugun ta'ba min zuciya banyi expecting hrt beat zata iya sharewa da lamarina ba, duk ba ma shareni datayi yafi damuna ba kamar yadda iyayenta sukayi burus dani ko zaman daduro nake da diyarsu ai yakamata su nemi ni.. "kai da kake da mata baka nemesu ba ta yaya kake tunani sun nemaka? kawai malam kaajiye girman kai muje yanzu ayi maslaha ka ba kowa na gidansu hakuri a wuce gurin musty yakarasa mgnr yana kwashewa da dry. a cikin mota ma fad'a musty yake masa akan ya canza hali dan wannan halin nasa baiyi ba.. "ka kasa fahimatata ne kawai bakasan yadda nake ji in dawo gida banga yarana ba most especial ihsan yarinyar ta ba'lain shiga raina "hakuri zakayi kamar yadda kowa yake yi, dole ka d'auke zuciyarka akansu, kasancewa jikokin diya mace a zuciyar iyaye suke ballanata wad'an nan jikoki daban suke agurinsu duba ga mahaifiyarsu ita kad'ai ce agurin iyayenta. "sannan ka dinga respecting iyayenta aboki a maganganunka babu respect ciki "yanzu irin abinda kakewa mahaifiyar yarinyar nan, idan nawa ammi zakaji dadi? "ka yi tinani kagani dan Allah daga yau komai ya wuce katayata kyautatawa iyayenta kmr yadda take wa ammi. har suka kusan karaso unguwar fad'a musty ke masa shi kuma yayi shr kmar da gaske d'aukar nasihar yake. cikin kankani lokaci suka iso unguwarsu , agaban makeken get din gidan sukaja birki tare da yin hon me gadi dake zaune yaji karar hon ya mike da sauri ya isa jikin hujin karamin get din gidan yana dubawa wad'an daya Gani ne yasashi fitowa batare da ya bude get ba ,ya isa jikin motar yana me rankwafowa ala'mun girmamawa . musty yayi kasa da glass din motar , yinka ya sake risinawa "sannuku da zuwa. "ykk yinka ya aiki inji cewar musty. "lafiya sir" "yinka bude mana get mushigo " yinka yayi shiru yana tunanin abinda zai fad'a musu har sai da musty ya sake maimaita abinda yace ,sannan yinka ya dawo cikin haiyacinsa yace "dan Allah kuyi hkr small madam tace idan kukazo kar na sake mabarku ku shigo. matukar firgice musty da ak suka kalli juna hankalin ak yayi maseefar tashi da jin hk take jikinsa yasoma tsuma a harzuke "yace kunci kutumar ubanku kai da small madam din wawa kawai ,jibeshi katun banza kawai ya wani 'bare baki yana mgana kmr jaki dan allah malam bude mana get mushigo kafin nafito na tattaka agurin "kasan kuwa ko ni waye dakake isar min da wannan banza sakon "cool down fried ka natsu ka dawo hankalinka "kabari mubi komai ahankali "akan aikinsa yake abinda aka gaya masa shi ya aiwatar "kai yinka jeka kace mata tayi baki ne. . yinka ya juya da sauri yayi cikin gidan, cikin mintina da basu wuce biyar ba, sai gashi ya dawo cikin sauri "wai tace baza ta samu damar fitowa
Chapter 285 · 0% Book details