Sashe 75
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam athur shaturul iman* *best family forever and ever i really appreciate all your washi and the love you showed on me ,i truly feel happy to have such amazing family in my life Love you so much* *hajarutul (mee'ad )da halimatu sadiya (e'man) Allah yaraya min ku cikin tafarkin sunnah ,Allah yasanyawa rayuwarku albarka* page 28 a kalla ya kusan minti talatin jingine da jikin kofar ,dafe da saitin zuciyarsa, yana fidda numfashi sama sama. runtse mayatattun idanunsa ya sake yi sosai tare da kiran sunan Allah, ya salam .. .. karo na kusan goma kenan daya ja tsaki cike da matsanancin takaicinta . bai san me ya kawota gidansu ba... yanzu idan dady'nsa ya fito ya ganta agurin yace masa me ,akan yarinyar da tuni yace masa yakawo masa ita amman yaki ? ahankali ya bude mayatattun idanunsa wayanda suka gama rikidewa sukayi jawur dasu sbd abinda yake jin yana masa yawo cikin rayuwarsa a game da lamarin yarinyar . a fill yace, wannan wace irin maseefa da jaraba ke shirin kusantoni da rayuwata ? ita bata barni na huta nayi rayuwarta yadda nasaba ba. sannan ita bata bar kanta ta huta ba.. cikin wannan tunanin da yake wasu zafafan hawaye masu zafi da ciwo yaji suna sauko masa akan kyakkyawa fuskarsa.. cikin sauri yasanya hannusa ya sharesu tare da jan numfashi da kyar ya fitar ,lokacin ne yaji tsanyi ni'ima da wadataccen iska yana kursuwa ta kofofin window's din part dinsa da karfi . cikin hanzari yasoma takowa ya isa ga window's yasoma kokarin kullewa kasancewar yadda iskan yake saukowa da karfi. dan har feshin iskan yasoma shigowa. tsaye yayi cike da sabon mamaki yana kallonta . tsaye take agurin tana kallon sararin samaniya yayinda ruwan sama oready yasoma saukowa da karfi ,yana sauka ajikinta. ,kusan minti goma ya dauka tsaye agurin yana kallon yadda ruwan sama ke sauka a sansar ajikinta batare da tayi yunkurin tsarewa ruwan ba. ,take kirjinsa yayi wani irin matsanacin bugu .. sosai ya zuba mata mayatattun idanunsa yana cigaba da dubanta tare da jin wani irin sauyi na daban agabadaya ilahirin sansar jikinsa. takoina ajikinta jike yake sharkaf da ruwa tun daga samanta har zuwa kasanta tsiyaya take. wani irin sanyi ne Me tattare da tausayinta yasoma ratsa ilahiri jikinsa. karo na farko kenan daya ji wani abu makamanci hk atare dashi a game daita. ,kmr ance ta juyo.. idanunsu suka tsarke cikin juna. a matukar firgice take kallonsa tare da narka da fuska ala'mun ya tausaya mata . wani irin nagartaccen kwarjini taji ya sake yi mata me gauraye da tsagwaron sonshi. yadda bai dauke idanunsa akanta ba. hk itama bata fasa kallonsa ba, har sanda tasanya tafin hannuwanta duka bisa fuskarta tana goge ruwan dake kokarin rufe mata idanu ,domin hanata kallon cikin idanunsa. ,cike da mutuwar jiki ya saki labulen ya zuge glass din window, ya koma jikin kofar ya jingina yana jin yadda bugun zuciyarsa ke sake karuwa . takun su'ad ta sake yi, ta dawo jikin kofar ta jingina bayanta tare da sake fashewa da wani irin kuka me cin rai da ban tausayi .. tana furta wayyohhly Allah Ni su'ad laifin me na aikata ma Allah da yasa nazo duniyar nan...? ya Allahu laifin me nayi da rayuwata tadawo hk? meye makusata da aibuna wanda yasa abdulkabir yakasa amsar soyayyata..? Kowa yana sona a wannan duniyar, amman kai dana sha matsananciyar wahala akanka shekara da shekaru kana guduna.... babu wanda yake kina sai kai abdulkabir.. bakasona ....... bakason na rabeka ko rabar duk inda Kake ballantana na rage radadin da nake jin a zuciyata. pls ...pls ...abdulkabir karka min hk NI masoyiyarka ce kamar yadda na sha gaya maka. ,wayyohhly Allah ya Allah ka dauki rayuwata na huta da wanan bak'ar ukubar akan na ga aurenka da wata .. Allah ka kasheni kafin zuwan lokacin aurenka, na gwamaci mutuwata da wannan rayuwar... ahankali tasoma yin kasa kasa da jikinta tana risgar kuka har ta tsugunna tare da daura fuskarta akan gwiwowinta tana cigaba da kuka me cin rai da taba zuciyar ma'aboci sauraro. iskan ruwan na sake dukanta inda take tsugune . zuciyar AK ce tayi wani irin bugawa da karfin gaske sakamakon jiyo sautin muryarta cikin kuka ,har tagama sambatunta yana jingine yana jinta , wani irin sanyi ne ya dinga ratsa gangar jikinta. take tasoma rawar sanyi da karkarwa har hakoranta na kirma. ruwa ne aka tsugashi ba wasa ba . domin kuwa duk wanda ya kwana ya tashi a garin Lagos yasan yadda ake tsuga ruwa barin ma farkon damuna. km duk tsawon wannan lokaci tana nan a tsugunne ajikin kofar part dinsa tana cigaba da kukanta ahankali wanda ya hadasawa kanta sarawa da karfi. gashi AK kwata kwata bashi da niyyar bude mata kofar balle tasamu mafaka domin tsira da lfyrta ... hkn yasa tasoma dago kyakkyawa fuskarta dake zubar da ruwan hawaye ..tun kafin takarasa kai ga dagowa gbdy take jin wani irin azababben kamshin turaren wanda yasaba tsaya mata arai .. km take ji ajikinta kmr tasan shi . ,tana karasa dago fararen idanunta da suka sauya daga fari zuwa ja ta saukesu akan fuskar wani dattijo dake tsaye can nesa kadan daita, yana dubanta . hannunta tasa ta dan murza idanunta domin sake tabbarwa kanta mutumin dake tsaye agabanta ba abdulkabir dinta bane kama ce kawai, da dan bancanci tsakaninsu, shi wannan fuskarsa ta dan manyata sabanin ta abdulkabir dinta dake cike da tsantsar annuri da zati tattare da nagartacce kyau da kurciya. kusan Mintuna talatin ta dauka tana kallonsa , kafin daga karshe ta zabura ta mike tsaye a firgice tana zare idanuwa cike da matsanancin tsoro.. bangaren dady kuwa tsaye yake cike da sarkakiya da mamaki ganin mace a kofar part din ak. duk yadda yasan dan nasa na mu'amula da mata baiyi tunani zai iya kawo mace har cikin gidan dayake zaune ba, wani irin kallo yake bin yarinyar dashi zuciyarsa na kitsima masa wacece ita da kallon sani dayakewa fuskarta? her face is familiar to him . sosai ya tsura mata idanu ahankali yashiga tunani Inda yasan fuskar ,gabansa ne yashiga dukan uku tabbas duk inda fuskar take yasanta sani km farin sani sai dai,ta ina hkn zata kasance, fuskar wayanda yake gani a fuskar yarinyar dake tsaye agabansa yanzu bata da halaka da fuskar dayasani, kama ce kawai ba wata halaka ko dangantaka ce ba. ahankali yacigaba da kallonta, kafin daga bisani ya numfasa tare da cewa . yarinya daga ina hk ko wani kike nema..? tunda dady yasoma mgn su'ad ta sunkuyar da kanta kasa gabanta na faduwa sbd kwarjinin da dattijon yayi mata, bakinta da jikinta rawa suke gurin cewa uhm ..uhm ina wuni sunana su'ad daman nazo wajen abdulkabir ne.. nazo gurin abdulkabir dady ya maimaita mgnrta cike da mamaki, take km zuciyarsa tasoma bashi haske akanta. duk da bata gaya masa bayanin komai akanta ba ya gane yarinyar dake da halaka da tilon dansa ce tausayin yarinyar ne ya rufe shi ,ya dinga wani iri acikin ransa. wannan wani irin so ne hk takewa abdulkabir dinsa ..? yanzu duk ruwan nan akanta yakare kome.? to yanzu ina shi abdulkabir din yake. daya barta anan ruwa yayi mata duka? ajere yayiwa kansa tmbyr acikin zuciyarsa. wani irin sanyi yaji yana ratsashi ta koina, ko babu komai wannan abun alfahari ne ace mace tana maka irin wannan tsaftacencen soyayya ta gsky . wanda duk wani uba na gari zai so ace dansa yasamu mace irin wannan me tsananin sonshi . ita kanta soyayyar mace wani jigo ne da taimako a bangaren auratayya,rayuwar aure. sannan tunda yake a rayuwarsa bai taba ji ko gani irin wannan soyayyar ba . cikin sanyi jiki su'ad tashiga ware bakin mayafinta domin suturta jikinta , tana kokarin barin gurin dan gane kowaye agabanta. dady yayi hanzarin dakatar daita da hannunsa yana takawo ahankali zuwa bakin kofar part din ak tare da yin noucking . "ak wanda ke tsaye jikin kofar yayi shiru kirjinsa na bugawa da karfi, yaki motsawa balle yayi yunkurin bude kofar yayinda zuciyarsa tashiga shawagi tare da harbawa, jin bugun kofar yayi yawa ne yasa zuciyarsa dugunzuma tare bude bakinsa cike datakaici yace dan ubanki tsayuwar uwar wa kike da bazaki bar gidan nan ba .. ko gidan ubanki ne ? wlh idan kika sake na fito na sameki agurin zan miki dukan mutuwa na balbalki na aikawa ubanki da kasusuwanki stupid girl kawai ...wace bata san ciwon kanta ba . yana karasa mgnr bai tsaya jin ko me zat'ace ba ya baro jikin kofar ya nufi cikin bedroom dinsa a tunaninsa ko su'ad ce ke yin nouking . yana shiga ya fada kan gadonsa yana fidda numfashi ahankali ahankali ko mitin biyu baiyi da kwanciya ba kira yashigo wayarsa, sai da gabansa ya fadi dan jin wayarsa ta dauki karar sauti ,yasa hannunsa ya lalubo wayar ya manna akunneshi batare daya duba screen din wayar ba. shiru yayi yaki cewa komai, yana jira daga dayan bangaren, kazo ka bude min kofa....gani akofar part dinka. ai jin muryar dady yasa ak yin wata irin zabura ya Mike zaune yana kallon kofar bedroom dinsa zuciyarsa nacigaba da harbawa oh my God Allah kasa dady bai ga wannan shegiyar yarinyar nan ba? cikin sauri ya duro daga kan gadon yasoma kokarin sanya kaya ajikinsa. short niker yasa tare daura riga tsanyi me hulla abayanta bai tsaya zuge zip din gaban rigar ba ya fito ransa a matukar bace. ya bude kofar idanunsa suka sauka akan fuskar mahaifinsa tsaye, yana kallonsa , matsawa baya kadan yayi domin bawa dady hanya tare da zabgawa su'ad wata uwar harara wace tasa hantar cikinta kadawa, da sauri tayi Kasa da kanta tare da kamo yatsun hannunwata tana wasa dasu.. kokarin kulle kofar AK yake yaji sautin muryar dady cikin kunneshi yana bashi umarni ,kabar yarinyar nan tashigo.barin kofar yayi a bude ,ya juya cikin fushi batare da ya sake kallonta ba, zuciyarsa kmr zata buga, yana kokarin komawa cikin bedroom dinsa. dady yakirasa sunansa abdulkabir dawo nan sannan kacewa yarinyar nan tashigo ciki yanxu tun ranka bai fi hk baci ba. dole tasa ya