← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 289

Sashe 57

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* ~DEDICATED TO~ HAUWA A USMAN JIDDARH *qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam tahadau tahabbu* *Allah's messenger (s. a. w) Said exchange gifts, it enhances affection* Page 23 Tashi daya hankalin ak ya sake birkicewa akan matsanancin son ganin zeey, natsuwarsa yasoma barin gangar jikinsa ,tare da rashin sanin madafar abinda ke damunsa . "yarasa meke masa dadi arayuwarsa . meke damun tunaninsa da kwalkwaluwarsa akanta. " gabadaya kasar spain tagama fice masa arai ga duk yadda yake mugun kaunar kasar da son zama cikinta kasancewar kasar haihuwarsa ce. "ta koina ya gilma cikin kasar , zafi kasar yake ji a gabadaya ilahirin jikinsa gashi sauran kwanaki ne yarage masa yasoma zana jarabawarsa na zangon karshe wanda daga shine zai karfi certificate na Digre dinsa na biyu. "wani irin zafi da radadin zaman garin yakeji tare da jin matsanancin haushin duk wani wanda ke tare dashi ,sosai ya tashi hankalinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye , magana daya biyu zakaji yace shi kasar ta fita ranshi ,barinta zaiyi gbdy ya huta ya koma gurin zainab dinsa . Yasan zai samu dukkan wata natsuwa da kwanciyar hankali dayake bukata fiyye da komai agunta . onye najin hk ,take hankalinta yayi bala'in tashi sbd zuwa yanzu tasan tsinanniyar yarinyar da ke rusa mata asirinta akansa ce ke zafafa wani shirin ,, and she knows duk asirinta ne ke yamutsa masa tunani da lisafi . Wunin yau tana zaune akan kujera one site ita kadai ta zabga uban tagumi tana tunanin mafutar hanyar da zatabi gurin rutsa zafaffen asirin zainab akanshi. yashigo gidan a matukar firgice ya wuceta zaune zuwa bedroom dinsa.batare dayace mata komai ... A firgice ta mike staye Jikinta na rawa tabi bayansa da sauri tana kiran sunansa... Yayi mata banza bai ko nuna yajiyota ba ballantana ya kai ga tsayawa. ,yasanya kansa kawai yayi cikin dakin ,yana shiga yasoma hargitsa koina a dakin yana duba takardunsa na fita daga kasar spain .... kusa dashi tazo ta tsaya sosai kmr zata shige masa cikin jikinsa . bai ji komai a gangar jikinsa ba sbd ahalin yanzu ba itace agabansa ba . Zeey dinsa kawai yake kwadayi da muradin son daura kwayar idanunshi akanta. Damuwarsa yadda zai fita ya bar kasar kawai yake, yanzu dayake hargitsa dakin. Muryarta a matukar raunane kmr zatayi kuka tace honey what are you looking for ..? Ya sake yi mata banza batare da ya amsa mata ba ,bata damu ba still sbd idan da sabo tarigada tasaba da yanayin halayensa wata rana farinciki wata rana baknciki . ,yacigaba da dube dubensa amman yawam ba takardu babu alamunsu. kawai yaji wasu hawaye masu zafi da radadi sun shiga tsiyayo masa bisa kuncinsa tsabar takaici da zafin dayake Jin zuciyrsa nayi .. nashiga uku abinda onyen ta iya furtawa kenan cikin yarenta na iyamuranci tare da daura hannuwanta bisa kanta tana jin jijjiyoyyin jikinta na tsinkewa. , hankalinta a tashe tace me zangani yau, ak hawaye kake ....? akan wani dalili zaka dinga zubda hawayenka abanza, ta matso sosai kusa dashi ta riko tafin hannushi cikin nata tana murzawa cike da matsanancin faduwar gaba takira complet name dinsa cikin rawar murya abdul...kabeer meke damunka hk wanda yasa kake hasarar hawayenka akanshi....?sannan km meye shi abinda kake nema ?tayi masa tmbyr ajere tana kallon cikin kwayar idanunshi da suka gama rikedewa zuwa launin ja. ya runtse mayatattun idanunshi gam yana jin zafin tafuffukan hannunta ajikinsa . "kokarin zame hannushi yake cikin nata batare daya bata amsar tmbyrta ba, tayi saurin riko yatsunsa guda uku da yayi saura cikin nata pls karkamin hk honey .. kagayamin shi abinda kake nema bakasani ba ko nasan inda yake takarasa mgnr hawaye na wanke mata fuska ,naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi tare da bude mayatattun idanunahi ya sauke cikin nata idon ... take zuciyarta ta bugu da sauri sakamakon ganin yadda yanayinsa ya sauya cikin kankanin lokaci. muryarsa na rawa yace vizata tabarin kasar nan nake nema ..yayi mgnr in a low voice .. kasar nan zakabari honey tayi mgnr cike da farinciki ? kasancewar ita kanta a matse take data bar kasar ,taje ga nata bokan. amman batasan yadda zatayi ba. dan bata son barinsa shi kadai . tafison kafarta kafarsa zuwa nigeria . hankali ya girgiza mata kansa ala'mun eh .ok yanzu ka kwantar da hnklinka ka tuna inda ka'ajiye takardun. " wallahi na kasa tunawa ya fadi mgnr muryasa cike da rudani .. ok kwantar da hankalinka mu duba atare . Ahankali suka cigaba da duba koina a dakin . duk takardar datagani sai ta nuna masa amman yace baita bace. hk wunin ranar yashige a neman takardun viza sukare Batare da sun gani ba.. Daren ranar ma kusan tsaye suke suna abu guda. Ya firgice ya haukace duk yabi ya rame sai idanuwa kawai yake zarewa kmr wani zautace zuciyarsa jinta yake tmkr ana buga masa kuduma . " zariya yashigayi acikin dakin yana zuba sambatu wayyohhh allah yanzu bazanje naga Zainab dina ba ......zainab nake son gani .....wayyohhh zuciyata zata bagu ya dafe daidai saitin Zuciyarsa da duka hannuwansa ... onye sai binsa take tana kokarin kamoshi yana kwacewa . Take tashiga rarrashinsa tana gayamasa word masu sanyi da sanyaya zuciya yayinda take jin kmr zata bugu kirjinta yayi mata nauyi agabanta ak ke haukan son wata wannan ya nuna mata bokan ita yarinyar yafi nata bokan iya aiki da tasiri ,kai karya ne inji wani side na zuciyarta nima dan bana nigeria ne .zuciyarta ta dan samu natsuwa kadan sbd sanin sunan yarinyar ahalin yanzu tashin farko zata saka bokanta ya haukata mata ita tabi duniya ..ko km ya kashe mata ita gbdy .. ammi wace ke tsaka da baccinta ta farka a firgice daga mummunar mafarkinta datayi da danta . Zaune take atsakiyar gadonta tana kallon celling dakinta da fankar dake jujjuyawa ahankali. addu'oi tashiga karantowa abayyane sannan tashiga tariyo mafarkinta daki daki wai abdulkabeer dinta ke faman falfala gudu acikin wani kungurmin daji wanda babu gida gabanshi babu gida bayansa . "yayinda wasu mutane masu siffar aljanu ke binsa da wuta a hannunsu suna watsa masa ta koina a sansar jikinsa ,shi km yana ihu da kururuwar neman dauki . gumin daya rufeta tashiga gogewa da hannuunta tana cigaba da karanto duk addu'ar datazo bakinta. mikewa tayi cikin sanyi jiki ta sauko daga kan gadonta takarasa inda wayarta ke jone a charge tasa hannu ta zare wayar tashiga neman layinsa misss cal kusan sama da goma tayi masa kafin daga bisani tasamu ya dauka . muryarsa a sarke yace hello amminah... ,ajiyar zuciya ta sauke da karfi tana me dafe daidai saitin zuciyarta dataji ya cure guri 1tare da runtse idanunta sai hawaye sharrrrr .....daga kwarnin idanunta da sauri tace abdulkabeer dina....... na'am amminah ya amsa mata muryarsa a matukar sanyaye . ,lafiya naji muryarki wani iri kmr ma kuka kike ? Tayi saurin goge hawayen dake tsiyayowa daga idanunta tare da saita muryarta ,kana tace babu komai yarona ba kuka nakeyi ba fatan kana cikin koshin lfy? ..lafiyar nan dai kam da sauki ammina sbd ji nake tmkr nazama tsuntsu na dawo nigeria. "Tiririn zafi Nakeji asansar jikina gabadaya kasar spain ta gundureni ahalin danake ciki ..wasu sabbin hawaye ne suka shiga gudana a saman kuncinta kenan mafarkinta ya tabbata gasky ne? Kenan wani mummunar abu ke shirin faruwa da gudan jininta........ Bakada lfy ne da jikinka ke tiririn zafi ..? Lafiyata lau hk kawai nakekin wannan yanayin atsakankanin wannan lokacin .. Ta sake goge wasu hawayn har da shesheka kana tace inna lillahi wa inna ilaihi raji'un , dan girman allah abdul ka dinga bin komai ahankali tare da addu'oi idan wani mummunar abu yasameka bansan yadda zanyi da rayuwata ba. ,abdulkabeer baka addu'a ka taimaki rayuwar amminka ka dinga kusanta kanka zuwa ga allah. duk yadda nake matukar sonka da son lafiyarka allah yafini sonka km shi zai kare min kai aduk inda kake amman sai idan kana da kusanci dashi . yanzu me kake yi a halin yanzu ? takarasa mgnr tare da tmbyrsa .lips dinsa dake datse da hakoransa ya saki yana furzar da iska me dumi ta bakinsa sannan muryarsa na craking yace ina neman takardun vizata ne,dawowa zanyi ko ayanzu idan nagani . ammi ina son na dawo banajin dadin zuciyata dama rayuwata gabadaya ..amma kagaya min nest week zaku soma exams ? eh na hakura da karatun zuciyata da gangar jikina amatukar matse suke da son dawowa nigeria a halin yanzu. " ammi ta natsu tare da yin shiru tana sauraron zantuttukansa ta lura kwata kwata baya cikin natsuwarsa da hankalinsa . ka natsu abdul kaje yanzu kayi alwala kayi nafilfili ka kaiwa allah kukanka koma menene am very sure allah zai kawo maka sauki ,nima bakomawa bacci zanyi ba . Sannan kabar zance tahowarka har nan da sati biyu daidai kagama exams dinka. ni kaina nafi sonka kusa dani amman bazan so wahalarka ta tafi abanza ba .. ok kawai ya iyacewa badan yaji zai iya abinda tace masa Din ba. na ya zauna har ya rubuta wani exams . allah yayi maka albarka allah ya kareminkai aduk inda zaka sanya kafafunka ya karemin kai daga sharrin mugayen mutane Da aljanu yakara maka lafiya kai da sauran al'umar annabi muslimai.amen ammina yayi mgnr yana jin sauki da sanyi cikin ranshi. love you so much my d love you more my sweet mom . ammi ta katse kiran daidai lokacin da onye tashige cikin jikinsa ta rungumeshi tsam tana son dagula masa lisafi you have such and lovely care mother and you were to give it up to her she love you so much ...ak ya katseta ta hanyar rabata da tsantsar jikinsa dan yadda yake jin zuciyarsa baya kaunar kusancinsa daita .yashige bayi ya dauro alwala kmr yadda amminsa ta umarcesa ... Main Parlour ya fito ya tadda ikamar sallah yashiga jero nafiloli wanda shi kansa ba yace ga iya adadin raka'oin da yayi ba. daga karshe yayi wutiri yana jin natsuwar zuciyarsa na karuwa ,kirjinsa yarage nauyi ...... Ahankali yake jan carbi yana lazimi . Kadan2 bacci yasoma kawo masa ziyara yayi yan addu'oinsa ya mike da kyar yakoma yayi kwanciyarsa akan daguwar kujera dake parlour'n . washegari
Chapter 57 · 0% Book details