← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 289

Sashe 4

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fadi hk . AK yaja ya tsaya cak batare da juyowa ba sbd yasan dashi take . ahankali takaso xuwa gurin dayake tsaye tasha gabansa ta riko hannayensa duka cikin nata tana kada masa idanuta tace da gaske zaka dawo gareni wani lokaci? yace me zai hana? OK inda kadawo sunana onye kada kashiga dakin wata..... sbd ina da matsanancin Ki...... katseta yayi ta hanyar ce mata bakece zaki tsara min yadda zanyi ba ni ne zanyi abinda yadace ya fadi hk yana kokarin bude kofar dakin. tayi hanzarta bude masa tayi masa rakiya. Tana tsaye har sai dataga tashin motarsu.ta dawo zuciyarta cike da tunanin AK sannsn tana jin ajinin jikinta bazata iya rabuwa da shi ba. ko ta wani hali sai tabari ya ratsa cikin jikinta suyi mu'amula dashi ta lashi zumar dake tattare dashi.da wannan tunanin tashige dakinta tana tattera kudin da AK yabata, ta saba Jakarta tare da kullo kofarta tayi waje tana rangwada tkmr wata bugagiya. akil suka fara saukewa . Sannan suka dauki hanyar gidan. Karfe goma sha biyu daidai. aka danna hon da wani irin matsancin karfi Wanda ya kusan frigita alhalin gidan dan lokacin tuni iman da zeey sun Dade da yin bacci. alhj Adam da hjy baraka ne zaune zaman jiran shigowar AK wanda tun byn fitarsa suke kiran layinsa Amman baya shiga. azabure suka mike tare da dady sakamakon jin wannan razananniyar hon din ake faman yi . suka zuge labulayen parlour 'n windows suna son sanin abinda ke faruwa . wanda shi get man din gida oready tuni ya isa ga hujin get din gidan. ganin motar dake tsaye akofar gidan yasaka shi hanzarta soma zuge get din gidan jikinsa na rawa rawa . ai yanagama zuge get din a guje motar AK ta sanyo kai cikin compound gidan. abokannensa guda biyu suka fito aguje suna kokarin kamoshi su fito dashi wannan abun dake faruwa .. yasa ammi da dady fitowa da sauri km agigice suna kokarin zuwa inda motar AK take parke da mugun sauri suke daga kafafunsu kowanensu na addua cikin ransa Allah yasa bawani mugun abu ne ya faru da tilon dan nasu daidai conal da zata kai mutun ainihin compound 'n din gida suka ci karo da musty da Malik tallabe da Ak wanda yake samkame kunfa na fitowa ta bakinsa idanunsa gabadaya Sun kakkafe . yayinda koina ajikinsa ke kirrma ai ammi naganin hk batasan sanda takarasa da wani irin matsayacin gudu takarasa zuwa inda suke tana kiran sunan danta abdul...kabir .... Abdul...Abdul... shima dady yakaraso yayi yana kiran sunansa . da furta Kalmar Inna lillahi inna wa inna ilaihi rajiun sbd yadda yaji zuciyarsa ta amsa tasoma bugawa da sauri ya bakinsa dayasoma rawa yana tmbyrsu. meyasa meshi? Me kuka Yi masa hk? Gabadaya ya rude ya dinga maimaita tmbyr daya ganin yadda kumfa ke fita daga bakin AK ne yasa shi tsayawa cak yana dubansa domin ganowa da yayi ciwonsa NE yatashi. ammi ce dake durkushe rungume dashi ajikinta Tana kuka tana cewa Meyasa ..meyasa.. ciwon nan baya tashi sai sanda muka zo Nigeria....? Wai meke shirin faruwa da yarona ne...? Wani irin masefaffen ciwo ne wannan me shirin tarwatsa min rayuwar Dana? Dayaki ci yaki cinyewa yana son ganin baya na da rayuwar dana.. ..... Kuka take sosai tana sambatu. gabadaya tsoro da frigici suka taru suka shiga Zariya da musty da Malik daKe tsaye. suka rasa me zasu ce da ammi da dady . banda kirma da rawar baki, babu abinda suke Sun rasa me zasu ce sai da kyar musty ya iya karfin halin cewa wlh Ammi Yana driving ne kawai muka GA ya mimike jikinsa na rawa bakinsa na fidda wannan kunfar shikennan muga ya sankame gurin daya, shine mukayo gida dashi . ammi wace gabadaya jikinta ya dauki rawa hk shima dady dake tsaye yana kallon yaronsa cikin mawuyacin hali ,cike da tsananin tsoro ganin yadda ,idanunsa suka firfito cikin matsanancin ciwo. tausayi da kaunar dansa suka taru suka raunata zuciyarsa. Ya dinga ina ma zai iya daya cire masa wannan mugun ciwon ya daurawa kansa domin yaronsa yasamu yayi rayuwa me inganci wasu siraran hawaye suka samu nasarar zubo masa. yayi saurin gogewa , jikinsa a sanyaye yakarso ya rike hannun AK yace ku kama mana shi mushiga ciki dashi. Take su musty Suka kama AK dake samkame still kunfa na aikin fitowa daga bakinsa suka nufi cikin gida dashi akan kujera three star suka kwantar dashi ammi ta nufi dakinta da wani irin mugu mugun sauri shima dady dakinsa ya nufa shima domin dauko maganin gurinsa wanda kaninsa ya kawo masa dazu dayazo . atare suka sake fitowa shi da ammi kowanensu narige rige karasowa gurin AK dake kwance yana shure shure still kumfa na fitowa daga bakinsa . Suka shiga shafa masa magani takoina ajikinsa suna cire masa rigar dake sanye ajikinsa. tundaga kansa har zuwa kafafunsa kana rawar jikin ya dan daina sai kumfar dake fita ta bakinsa.. musty da Malik suka ce su zasu wuce gida sbd dare yayi. dady dake tsaye daidai kan AK. yace OK mun gode sosai ku gaida gida . suka fice suna cewa zasu zo gobe Inshaallahu. suga yadda jikinsa yayi.. Kuka kawai ammi take tana adduar samun lafiyar danta.. AK bai dawo haiyacinsa ba. sai gurin ukun dare wanda kafin lokacin ammi taci kuka har ta gaji ta godewa Allah. dady ne ma ME kokarin rarrashinta. Koda AK ya farfado yaganshi cikin wani hali da bazai iya tuna when last daya kasancewa ciki wannan yanayin ba. ahankali ya mike zaune hade da yin salati yana kallon amminsa da dady'nsa .bakinsa mgn yake son Yi amman ya Kasa bude baki yace komai ,idanu kawai ya tsurawa ammi da dady'nsa sbd yadda yaga alamun rashin kwanciyar hankali atattare da iyayen nasa, kmr koda yaushe idan ya tsinci kanshi cikin wannan yanayin me wuyar fassaltuwa . runtse idanunshi yayi wanda gabadaya bai san sanda yayi hakan ba. ammi ta mike zumbur daga inda take zata karaso gareshi . dady ya dakatar daita ta hanyar taga mata hannu aiko ta tsaya cak tana dubansa shi da Ak. zuciyarta tmkr zata buga tsabar rudanin datake ciki . wasu zafafan hawayen tausayin tilon Dan nata ne sukashiga zubo mata tasa hannuta tana gogewa wasu na sake biyo kuncinta. yayiwa dady yayiwa AK umarnin ya mike tsaye daga inda yake. Ahankali ya mike tsaye da kyar jikinsa babu kwari. Ammi tayi saurin rikoshi zuwa jikinta ta nufi dakinsa . shi km dady ya dauko wata robar me cike da ruwan magani ya yayyafa akan kujerar da AK ya tashi. Ammin kuwa tana shiga dakin AK . bathroom ta nufa dashi tana ganin yashiga takoma parlour'n wanda zuwa lokacin tuni dady yaga abimda yake har gurin yasoma bushewa. zama tayi jikinta a matukar sanyaye tare da zabga uban tagumi . dady yakaraso gurin datake zaune ya zauna akan kujerar dake facing dinta tare da riko hannuta duka cikin nashi yace Ki daina damuwa kiyi hakuri da wannan ciwon daga Allah ne. babu yadda bawa zai Yi da kaddarsa, km har yau muna iyakacin bakin kokarin akai .. nasani dady'n Abdul Amman ni rasa dalilin dayasa ciwonsa baya tashi sai munzo Nigeria. nima abinda ke damuna kennan ammi .dayake shima hk yake ce mata kmr yadda ya'yanta ke kiranta dashi . Shiru sukayi tare kowane da abinda zuciyarsa ke saka masa akan ciwon AK. Byn kmr minti shabiyar ammi da dady suka nufi dakin Ak wanda tuni har yayi wanka ya fito ya saka wasu kayan yana zaune gefen gado jikinsa a matukar sanyaye yana tunani . suka karaso gareshi suna Yi masa sannu da kyar ya iya bude bakiNsa ya amsa. Magani ammi ta mika masa cikin cup tace yayi bismillah yasha . ya karba yana duban iyayen nasa cike da matsanancin tausayinsu sbd yadda suke mugun sonshi da son duk wani abinda yake so . sannan da kin Duk wani abinda baya so byn yasha maganin ammi tace suje yaci abinci muryasa cike da rauni ciwo yace ammi banajin cin komai yanzu. cikina akoshe yake ya kwanta yana me runtse idanunsa kusan minti goma suka mike shima dan sunga alamun yasoma samun bacci ne. Daren rana daga ammi har dady babu wanda yasamu damar iya runtsawa. gabadaya tunaninsu ya ta'allaka ne akan yadda tilon dansu zai warke , yarabu da wannan mugun ciwon me digresing din mutun cikin mutane sannan yake fama dashi sama da shekara goma sha iya magani sun nema akai wannan ciwion Amman har yanzu basu dace da magani ba . ko sanda suke Spain an sha aiko musu da magani km duk sunayi masa amfani dashi yadda aka ce. Washegari AK ya Mike sumul dashi tmkr bashi ba . jikinsa sanye da riga long-sleeve fara Sol da Wando ,ya Dan nade hannun rigar Wanda ya bayyana tsadadden agogon Rolex din dake daure a tsintsiyar hannushi sai kamshi turaren ameeral oud yake, zubawa takoina ajikinsa . gashin kan nan shi yana kwanshe luf luf sbd mugun gyara dayake samu akai akai wani irin sihirtaccen kyau yayi tmkr ba asalin dan Nigeria ba . gabansa system ne yake aikin sarrafawa Ta hanyar turawa abokansa dake Spain sakonni . harkokin gabansa kawai yake hankali kwance tmkr ba wanda yayi wata lalura bA jiya. yayinda daga ammi har dady suke binsa da wani irin mayataccen kallon Duk ta yadda ya motsa daman km hk ce take kasancewa dasu, a duk sanda irin hk ta faru dashi ,sai suyita kafa kafa dashi ko fita basa barinsa yayi, ammi ta mike jikinta a raunane tashiga kitchen sbd lokacin girkin rana yayi domin batason mavaikatan gidan yimata duk abinda ya danganci kitchen dinta. byn ita da diyarta iman ko zeey Inda tazo , sai dai dan abinda baza rasa ba kmr abinci masu gadi. AK ya dago sexy eyes dinsa yana duban dady'nsa daya koma can daf da kofar fita ya zauna yana karanta magazine din dailytrust kana a shagwabe yashiga kiran sunan ammi.. Yes my son me kake da bukata ta amsa masa tana daga kitchen. sake shagwabe fuskarsa yayi tmkr wani karamin yaro yace ammi coffee...ok Dan albarka ganinan zuwa bani 5 minti. bai ce komai ba ya meida idanunshi kan system dinsa yacigaba
Chapter 4 · 0% Book details