← Book details Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 268 OF 289

Sashe 268

Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~NA~ *AYSHA A BAGUDO* Dedicated To Hauwa A Usman Jiddar YA SAMI'U THE ALL HEARING page 84 ........gaba d'aynsu da mamaki suke binta da kallo banda Taufeeq da Alhaji Mahmud da basu san ko wacece tsaye a gabansu ba, illa tsabar kamar da dattijon yaga tayi masa da sirikinsa dake zaune agabansa. cike da buguwar zuciya Ammi tace "daman kina nan mamana muke ta nemanki? " babu inda bamu nemeki ba mamana ....takarasa maganar hawayen farincikin ganinta ya ciciko a kwarnin idanunta, "bata san irin son datake mata ba... "a da can baya ta d'auka maraicin rashin mahaifiyanta ne ya haddasawa zuciyarta kamuwa da matsanancin soyayyarta ,sai yanxu fahimci soyayyyar yarinyar daban, na mahaifinta daban ammi ta saka gefen hijab dinta ta goge hawayen daya soma biyo kuncinta. Su'ad ta narke fuska tamkar zatayi kuka itama dan tasan tabbas ammi zata shiga wani hali adalilin rashinta, tana kokarin isa inda ammi take, mamma tace "zo nan Su'adullahi karki yi kuka yau ranar farin ciki ce garemu gbdy ahankali tacigaba da takowa zuwa inda mamma take ta zauna tsakiyarsu ita da ammi tana jin wani irin sanyi dad'i ta kasa cigaba da kallon fuskar Ammi datayi mata zuru tana kallonta cike da matsanancin mamaki . shi kuwa Taufik tunda yaji furunci Ammi yasan itace d'iyar da yabar cikinta kuma ko ba'a gaya masa ba yasan jininsa ce, diyar salimarsa tunda suna fizgar kama daita. shi k'ansa Alhaji Mahmud kallon Su'ad yake tare da kallon Mamma, ganin Alhaji Mahmud na neman k'arin bayani akan Su'ad yasa Mamma taci gaba da magana tare da rik'o hannu su'ad cikin nata. " na boye maka ita ne saka makon wani dalili nawa, amman tunda k'arshen komai ya bayyana dole na bayyana maka, ita koda kuwa bata bayyana kanta ba. "wata daya daya gabata ina zaune Saifullahi yazo min da ita wai a tapa yaganta tana neman gidan nan, inda daga karshe yace min daman yasanta tun a Nigeria shine likinta dake kula da lafiyarta, lokacin data sanar min cewa ita d'in d'iyar salima ce, nashiga wani yanayi me cike da rudu da tashin hankali daga baya damuwar ta juye zuwa tsantsar farin cikin sanin halinka da nuna rashin kulawa da damuwarka a tun barin salima gidan nan, yasa nayi tunanin boyeta har zuwa wani lokaci. "na kaita masaukin danafi buk'atar ta zauna mun dad'e muna tantaunawa akan mahaifiyarta inda take sanar min da duk abinda ta yafaru da ita bayan barinta gida har zuwa auren d'an yayar mahaifinta datayi da mutuwar aurenta.... mamma takarasa maganr tare da yin shiru tana kallonsu daya bayan daya Ammi ta kasa boye farin cikinta ta matso su'ad sosai ta rungumeta tsam ajikinta tana godiya ga Allah gabadaya takasa boye tsantsar farin cikinta "mun yi kewarki mamana mun shiga tashin hankali rashinki ashe kina nan tare da kakarki kin manta damu ko kina nan kina jin dadinkiko ? "Allah sarki shiyasa Ummanki tace in kwantar da hankalina jikinta nabata kina hannun na gari "ashe gsky ta fad'a Allah mun gode maka daka kawo mana k'arshen wahalarmu ,kalli nan ta nuna mata inda prof Taufeeq ke zaune wannan shine mahaifinki wanda yayi silar zuwanki duniya "Taufeeq ga d'iyar cikinka. idanunta ta meida kansa tana kare masa kallo Sir mahbub " kenan hasashenta zai zama gskiya? "Sir mahbub shine mahaifinta , tasha kawar da zuciyar datake karyata hakan gareta ta yaya hkn zata kasance ? a she kasan cewarsa na nan zuwa ,wani irin kukan farinciki ne ya kufce mata wanda bata san sanda ta mike tsaye da kyar hade da dafe kasan mararta ta isa gabansa ta durkushe har kasa bisa gwiwowinta tana kuka ahankali ya d'aura hannunsa bisa kanta yana jin wani irin sanyi da farin cikin mara misaltuwa na kai kawo a gbdy ilahiri gangar jikinsa. "yau ga diyar da salimarsa ta haifa masa, diyar daya bari aciki ya tafi kasar spain, itace ta girma haka har tayi aure .. cikin muryar kuka su'ad tace" zan kiraka da baba ka amsa min ya mahaifina" tsawon rayuwata nayi kwad'ayin wada zan kira da haka narasa sai yau "babana ina sonka bazan ta'ba kinka ba duk da kayi sanadin zuwana duniya bata hanyar dabata dace ba ....... " nima ina tsananin sonki diyata tun kina ciki nake mutuwar sonki da kwad'ayin ganin zuwanki duniya, Allah be kaddaro faruwan hkn ba har sai munyi wasu shekaru kafin muga juna, ta riko hannwansa duka cikin nata tana kallon fuskarsa tabbas shine dai mahaifinta da mahaifiyarta ta nuna mata hotonsa kuma shine dai me gidan Abdulkabir, furta sunan ak da zuciyarta tayi yasa ta runtsa idanunta dan bata son kawowa zuciyarta shi . mutumin data so kamar rai da ajali amman ya barta akan macen daya ya sha gaya mata baya sonta a can baya.. tacigaba da kallon mahaifinta tana jin tsantsar soyayyarsa na ratsata tana son ubanta bata da kamarsa ,duk da kasancewarta yar gaba da fatiha amman dole za'a kirasa da sunan mahaifinta, wannan farincikin kad'ai ya isa takarasa rayuwar datayi saura cikin jin dade. " sun dade tana kuka shima prof kukan yake har salima "to yane zasuyi da kaddarar da gifta musu kowani bawa da silar zuwansa duniya sannan babu wanda ya isa ya gujewa kaddararsa. a tsanake ta mike ta karasa ga kakanta wanda yayi shiru yana kallonsu cike da matsanancin tausayawa "kayi hakuri ka yafewa iyayena abinda suka aikata maka arayuwarsu ,samuwata a duniya ,kadarrasu ce babu tsimi babu dabara dole sai hkn ta faru "amman dan Allah kayi hakuri kabarsu su auri junansu a karo na biyu ina bukatar sucigaba da rayuwa a inuwa d'aya koda ban kasance cikakkiyar d'iya ba ina buk'atarsu atare ina son ganinsu cikin inuwa d'aya ka ..taimakeni dan Allah kabarsu su auri juna.... takarasa fad'ar hk tana me had'e hannunwanta duka tana rokonsa tana kuka ... atsanake Alhaji mahmud ya kai hannunsa yakamota ta zauna gefensa yana murmushi irin nasu na manya cike da jin dadi kana yace "raguwar mata kawai dube yadda kike kuka dagani lusarin miji kike aure ,wannan kukan hk kamar zaki had'iyi zuciya cikin muryar kuka tace "please granpa ka ceci rayuwa iyayena suna bukatar junansu ... murmushi yayi dan yaga ala'mun bata fahimci komai daya faru ba yasa yasoma magana cikin wasa da dry "ai tuni wannan maganar ta dad'e da wucewa acikin zuciyata" ni kaina cike da muradin sake d'aura idanuna akan iyayenki dake kanki nakeyi a kullun ," kaddara kuma mutun bai isa ya kankarewa kansa faruwata ba, zance auren iyayenki kuma tuni iyayenki sun mallaki junansu matsayin ma'aurata . ta juyo da wani irin sauri zuciyarta na wani irin harbawa tana kallonsu atare suka gyad'a mata kai ala'mun hk ne "Alhamdullahi ta furta a k'asan ranta "Allah na gode maka daka nuna min wannan rana "a she wannan ranar zata zomin nan kusa ban sani ba ? ta isa ta rugume iyayenta daya bayan daya tana murna Ammi tasa aka kira minsters da Dady dasuke parlour'n bak'i suzo suga ikon Allah, ai kuwa sun sha mamaki ganin su'ad nan dai akayi ta farinciki da murnar faruwar hk daga karshe ammi ta nasarwa su'ad Ak bai saketa ba da aurensa akanta jikinta na rawa tace "Ammi ya sakeni fa alokacin har tambayarsa Zeey tayi yace duka sakin yayi min idan ma duhun daya tsinci kansa ciki ne yasashi manta ai akwai shida tabbacin sakina dayayi barinaje na kawo miki ta mik'e cikin sauri ammi tabi bayanta da kallon cikin jikinta yafito sai dai bakowa zai tabbatar da cike gareta ba, kasamcewar cikin zumbulelen hijab take bata fi minti goma ba ta sake fitowa rike da farar takarda bata bude ba ta mik'awa Ammi. Ammi ta numfasa kana tasoma bude farar takarda ta duba tana sakin murmushi tare da mikawa Dady shima dubawa yayi sannan ya mik'awa minster haka suka dinga pacing din takarda atsakaninsu har Prof Taufeek sai daya gani sannan Ammi ta janyo hannuta "zo ki zauna diyata da ala'mun tunda aka baki takadar fargaba bai barki kin budeta ba? "amshi ki duba ki gani mijinki bai sake ki ba har yanzu igiyoyin aurensa na kanki jikinta na kirma ta amsa abinda tagani ya kusan zautar da tunaninta "to me hkn yake nufi Abdul bai saketa ba ....? farinciki yakamata tayi ko akasin hk? tayiwa kanta tmbyr cike da matsanancin tsoro da tashin hankali wannan wace irin rana ce gareta me cike da tarin fariciki? sosai ta tsurawa takadar idanu babu komai rubuce illa farar takarda empty , parlour'n ya d'auki shiru zuwa wani lokaci kafin daga baya Alhaji mahmud yayi musu nasiha me ratsa jiki daya danganci rayuwa aure sannan yasanyawa rayuwar auren salima albarka tare da fatan zaman lafiya me dourewa a tsakaninta da mijinta .. bayan karramawa da mutunta ka da akayi musu ta fanin abinci na ban girma har da zaga dagin sukayi na kusa ,sannan suka d'auki hanyar komawa gida cike da matsanancin farinciki da zumar wani sati Prof taufeek zai dawo ya d'auke salima tun cikin jirgi ambasodor yace "kar agayawa Ak abarshi tukun har zuwa wani lokaci .. Daren ranar da Salima ta kwana gidan su sam ahalinta babu wanda ya runtsa yadda suka ga rana haka suka ga dare suna hiran yaushe gamo. da suka isa gida ma Dady ya sake jawa Ammi kunne sosai akan karta kuskura ta sanarwa AK inda su'ad take har sai ya kara shiga hankalinsa . ****** ranar kusan kwanan farinciki Prof taufeek yayi duk kulawar da shema ke masa bai masa ba, hankalinsa gbdy na gurin sahebar ransa, gidansa dake banana estate ya yanke shawarar nan salema zata Zauna ita kuma shema zata cigaba a 1 thousand 4 ,cikin satin yayi duk abinda yakamata akan tarewar salima. ranar lahadi yan'uwan salema suka dira agidan ammi ,an musu tarba ta musamman da mutunraka daga karshe sukaje sukaga inda salema zata zauna, iyayen salema sun nuna mata gata fiyye da tuninata ,duk da prof taufeek yace karsuyi wahalar kawo komai , amman sai da sukayi duk abinda sukasan anawa duk wata diya me kima da daraja agidan aurenta. umman su'ad ta tare a hadadden gidanta wanda yasha kayan alatun more rayuwar duniya ,ahankali take bin d'akin da kallo tana mamakin irin duniyar prof ya kashe kamar wasu auren saurayi da budurwa ta
Chapter 268 · 0% Book details