Sashe 28
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kuka gwanin ban tausayi kmr gaske ka taimakeni yaya ka tausayawa rayuwata ka rabani da akil bana son ko kallon inda nike ya sake Yi arayuwarsa. ya mike ahankali daga zaunen dayake jikinsa a matuka sanyaye ya Dagota tsaye bisa kafafunta yana kallon fuskarta cike da ruwan hawaye . Yasa yatsan hannushi yana daukewa dake silalowa bisa kuncinta cike da tsantsar tauyayinta.. ya rungumeta tsam tsam ajikinsa yana shafa bayanta tare da tsigar rarrashi is OK Zainab I believe you ,yanzu danike jinki ajikinna zuciyarta Ta amince dake ta amince bazaki taba Aikata hkn ba . da fari zuciyarta Ta shiga zargi da wasi wasi iri iri akan mgnr akil Amman a yanzu na tabbatar da zantuttukansa akanki gababaya karya NE ba gsky. "shiyasa na hukunta miki shi bisa ga zunubin dayaso aikatawa.. kuka take sosai har da shesheka yashiga rarrashinta da gaya mata word masu dadi da sanyaya zuciya ta wani sake lafewa ajikinsa tana shakar daddaden kamshi turaren jikinsa. Da sakin ajiyar zuciya. ya koma ya zauna tare daita ajikinsa sannan ya zaunar daita kusa dashi .kusan mintina 15 sannan kowanensu yasamu natsuwar zuciya nan km suka shiga hirarsu irin wanda suka saba ta dauko masa coffee dinsa Ta bashi byn tayi masa mix da me zafi. yasoma sha ahankali kirjinsa na bugawa Wanda yarasa daliln jin hk sai kusan shabiyu ya mike yace suje ya raka Ta kwanta shima kiransa ammi tayi tace masa me Zeey takeyi a part dinsa har lokacin. har dakinsu ya kaita Wanda zuwa lokacin tuni Iman Ta Dade da yin bacci. AK ranar kwana yayi yana tufka da warwara akan matsalar dake tsakanin akil da Zeey ya sake yin tir da hali da dabi'u irin nashi dana akil . Juyi kawai yakeyi akan bed dinsa yakasa runtsawa tunani yake tare da jin zafin irin barnar da akil yaso Yi masa aboye yake yana cikin wannan tunani dayake take km yashiga tariyo maganganun akil inda yake cewa Zeey ce tace ya dinga biya mata bukatarta a boye batare da kowa yasani ba a take kirjinsa yayi wani matsanancin bugawa tare da bada wani gajeren sauti ya runtse mayatattun idanunshi tsabar jin zafin mgnr...... Ahankali ya ja ajiyar zuciya da numfashin a tare . ya tabbatar lallai akwai wani abu da Zeey Ta boyemai akan akil ya tuna sanda yake tmbyrta akan make tsakaninta da akil, a iya saninsa tayi mugun tsUrewa dataji abinda yace sannan ta canza daga zeey din dayasani zuwa wata ta daban. ahankali yashiga tuna komai da tunano kalaman da suka dinga fitowa daga bakin akil ayau din Nan .. Anya Kuwa babu kamshi gsky cikin lamarin yayiWA kanshi tmbyr? Kai Kai Zeey bazataba aikata hk ba inji wani bangare na zuciyarsa .. Zeey kamila ce ba waysartsiya ba yasan Zeey Yasan kowacece sunkasance MA junansu daya bazai iya rayuwa ba indai ba daya ba ,batun yau ba, ko yana kasar ko bai kasar dole suna tare da juna... Yasan halinta bazata taba kasancewa cikin masu munannan hali ba. To me yasa wani bangare na zuciyarsa km taki amincewa daita sannan yakasa gasganta Zance akil akanta... Meyasa zuciyarsa take neman karyata abinda tagaya masa yanzu da kanta? ya jima yana mamakin da tunanin akan rayuwar Zeey da halaiyeta. Farincikinta zuwa yanzu da komai yake neman canzawa ya kara tuno kyawawan halaiyenta.babu abinda Zeey zatayi batare data sanar dashi ba, sannan Duk abinda yace daita shi zatayi bata tsallake mgnrsa, shiyasa kullun take sake shiga ranshi har ya bata matsayin da ba kowa keda shi azuciyarsa ba, Yana cikin wannan tunanin har bacci barawo yayi nasarar daukarsa. Zeey tacigaba da gudanar da rayuwarta kmr yadda take so cikin jin dadi da farinciki yayinda komai nata ya dawo daidai kwata kwata yanzu akil yafita cikin rayuwarta . ko kiransa bata gani ballantana wani Mesage dinsa duk da tayi nasarar AK yarabata da akil to yaya zatayi da bukatuwarta ta yau da kullun.. Ita fa Allah dayayi ta tana da tsanain bukata Dan namiji . ,yanzu waye zai Maye mata wannan gurbin?........ mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE