Sashe 260
Sai Ka Aureni Dole Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
motsi tayi daga zaunen datake duk da tasan zainab tayiwa d'anta asiri amman batun bin maza ya taba mata zuciyarta ,yau da wani ne yagaya mata zata karyarta hakan. da taimakon dady aka samu aka kamo Zeey dake ihun"kubarni na fita shugaban bokaye da aljanun kan dutse na kirana "a a nazo zo, nazo mu tafi ko piiiiiiipppppp ganin nan zuwa "wayyo ku sakeni bokana nakirana tayi kukan kura ta kufce daga hannunsu bayan ta dauke hjy kaka da gigitaccen Mari har kuga biyu hjy tayi taga taga ta zube kasa warwas tana kuka maman zeey nayi.. zeey tayi waje aguje tana zunduma ihun "nice nice nayi komai "shugaban bokaye ganin nan zuwa. maman zeey ta kurma ihu " wayyohhly Allah dan girman Allah yaya kutaimin karta fita "wayyo Allah mutuwa zanyi wani irin rayuwa ce haka zainba kikajefa kanki ciki ? take securities suka shiga tara taran kamota a man kafin kace me tuni ta balle ta fice aguje tabar gidan tana tuki da hannunta kan titi unguwar securities suka bita abaya. maman Zeey naganin ficewan zeey nan ta fadi k'asa sumammiya.... securities kasa kama Zeey sukayi har titi suka bita amman ina ta tsere musu d'an kafin kiftawa da bisimilla suka nemeta suka rasa.. Haka akaci gaba da gudanar da sha'anin biki bisa umarnin dady, sai dai kallo d'aya zakayi ma Ammi kagane tana cikin damuwa da tashin hankali matuk'a, domin batada walwala ko kad'an rashin su'ad wani babban gib'i ne a rayuwar ta. Wai d'anma Umman su'ad ta tsaya kai da fata akan bikin domin Ammi birkice musu tayi ita sam baza ayi wani biki ba inba anga diyarta ba, gashi neman duniya anyi amma ba aga su'ad ba, duk inda akasan zata anje babu ita babu ala'mun kullum AK yana faman bulayi a gari neman su'ad tamkar mahaukaci gbdy duk yafita haiyacin sa yakoma tamkar sabon kamu, rabon shi da runtsawa tun randa abun ya faru ,kwana yake kuka da addua Allah yabayyana masa inda matarsa take. maman zeey kuwa da tun lokacin da abun ya faru tana hospital da kyar likitoci suka samu ta dawo haiyacinta , numfashinta ya dawo ta farka tana kuka tare da yiwa diyarta adduar samun lafiya. Ita kuwa Umman su'ad bata tab'a tsintar kanta cikin farin ciki, nishad'i da kwanciyar hankali ba irin na wannan lokacin, ita jikinta yana bata 'yarta tana wuri nagari wurin daya dace. Hannu nagari aduk inda 'yar take to lallai tana cikin farin ciki da walwala wanda bata tab'a samu ba a rayuwar ta domin kullum sai tazo mata cikin barci tana mata murmushi me k'ayatarwa tace "Ummana ban tab'a samun kaina ciki jindadin rayuwa ba irin wanda nake ciki a yanzu. "kema ina miki k'wad'ayin shigowa duniyar danake ciki Umma kid'and'ani dad'i da gardin dana ke d'an d'an. Kullum haka Umman su'ad take fama kuma inta tashi zata dinga jinta cikin farin cikin . Yau ake Mother's Day d'in eman da Musty hall yacika yayi mak'il da al'umman annabi inda Ado Gwanja yazage sai wake amarya da ango yake MC ne yadakatar da Gwanja domin gayyato amarya da angon a fili "Ado Gwanja yace "yana ison kayarta ma amarya da angonta da zafaffan wak'a saboda yanzu lokacin iyayen amarya ne sufito sunana farin cikin, dai dai Umman su'ad ta dok'a wurin Ammi tanace mata tasaki fuskanta dan Allah muryan MC sukaji yana fadin." "Gaskiya amarya tamu 'yar gatace lallai wannan bikin na yar gata ce shugaban airvioce da kansa lallai babu mamaki dan an lika dollas. dollas kawai ke zuba musu makad'an Gwanja anga dala sai k'ara sautin muryarsa suke da iyankan k'arfinsu Umman su'ad tace ammi "tashi muje muyi lik'i da kyar dai Ammi ta tashi. Sir mahabub yana ta barin dala shida matarsa shemah su Ammi suka iso suka fara nasu zuba ruwan kudi juyowan da Sir mahabub yayi don gaisawa da Amim idanunsa ya fiddo waje gabanshi yafad'i da k'arfi kanshi yasara yasoma ganin juwa tare bakinshi dake rawa yace " "Sali.......tun kafin ya kai ga rasa furtawa ya zube k'asa wanwar................ mmn sudais ce SAI KA AURENI DOLE